← Book details Ali Abbas Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 38

Sashe 19

Ali Abbas Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Autan ummu zan kiraki anjima, ayita zaman haquri kayan ki suna hanya, yanzukam kiyi zaman gidan mijinki shine mafi aa la agaremu baki daya, ban yarda da rashin kunya ba ko wani abin qi" Itama gyad'a mata kai kurun tayi batai magana ba daga nan ta fice, haka suka zauna shiru ita a tsorace shikuwa tamkar ya hallakata yakeji har wasu daqiqu da mintuna suka shud'e ba wani mewa waninsa magana, seda ya gaji dan kanshi sannan ya tashi ya shaqo wuyanta yace cikin fusata

"Tun farkon had'uwa ta dake tausayine ya rinjayi hangen muyagun halayenki a wurina, daga bisani kuma narasa da wane mugun tsafin naku na buzayen daji kika yi sa'ar sacemun zuciyata na soma sanki, na tabbatar da zancen huddy na baya a yanzu cewar ku d'innan mayune, banda haka tayaya iyayena da kansu zan rantse musu cewar ni d'innan bani na miki ciki ba, bansan da wannan qazantar cikin ba amma su nuna sunfi yadda da qarairayinki akan gaskiyar dana sanar musu, wlhy ku baqaen mayu ne masu muguwar zuciya, kuma ni bazan koreki ba amma baqar wuya ce zata sanya ki gudu daga gidannan da qafafunki, matsafa kawai masu bin mutane da baqar yadiya azzalumai masheranta" kuka manga ta fashe dashi iya qarfinta

"Haba Yaa Ali, banyi tunanin duk mutanen duniyar idan sun kasa yadda dani ba kai bazaka yadda dani ba, yaya kake qoqarin toshe idanka da kunnuwanka daga ganin zahiri wlhy ni bantaba aikata zina ba, kuma nida iyayena ba matsafa bane bakuma mayu bane" Tassss taji saukar wani gigitaccen marin da alokaci d'aya jini ya soma sakkowa daka cikin bakinta kuma ya zagaye mata ilahirin rabin idanta na hagu yana huci yace

"Bazan qara baki wata damar dazak8 rainawa tunanina hankali ba, jaka kawai me zina da auren wani akanta, jahila me bakar zuciya Allah ya isanni wlhy akanki,kin cutar da masarautar mu kin tozartar da zuri'armu kin kawo mana b'ara gurbi acikin mu, na tabbatar a India kikayi cikinnan,Allah yayi ikonshi ki haifo ba'indiye sak,kinga sena miqaki dashi baki daya awurin uban shi mayya kawai" kuka ta durqushe wurin tanayi kurun batare datayi yunqurin kare kanta ba a karo na barkatai......

*Bayan wata hud'u*

Banda duka zagi da cin zarafi babu abinda yake shiga tsakanin Manga da Ali dukta birkice yayinda cikinta ya zamto wani uban qato na ban mamaki ma dan bazaka yarda cewar wai watanni shida ne da cikin ba, yauma kamar kullum tana zaune ta rafka uban tagumi se kuka takeyi yana zabga mata zagi tamkar ba Ali Abbas me nutsuwa da hangen nesa ba

"Allah Manga duk sanda na kalleki naga wannan cikin se in riqa jin tamkar in shaqeki sekin sheqa lahira, sam bakida mutunci kuma kin citar dani, wato duk tsawon shekarun nan cutane kike se yanzu ne Allah tona asirinki jakar banza kuma jahila, kina haihuwa zan karbi dan dan Allah ki tallafi rayuwarshi dakika gurgunta ke kuma seki koma ki taya dattijon ki kwarewa masu gate, asararriya kawai" Ita wasu lokutan ma mamaki yake bata har dake sanyawa ta manta ilahirin duniyar datake ciki, kamar kuma an tsikareshi ya miqe yabar gidan, sabida ranshiyana b'ace ya sanya bema tsaya kallon qofar d'akin huddy ba ya wuce d'akin shi muryan daya jiyo ne ana waya daga ban d'akin ya katse masa tunaninshi

"Haba Ammy yaya zaki kunno wutar da Allah ne kadai ze iya kasheta, yanzu dani aka yiwa hakan zakiji dadi, mata da mijinta ki tashi hankulansu, ina namiji ze yadda da cikin daba nashi ba, kuma wannan aljanin da kika tura ki sani fa wlhy shima se Allah ya tambayeshi haqqin er mutane lahira,kuma wlhy bazan rufa asiri ba sena gayawa ummun Abbas kece kika turawa manga Aljani babu wani cikin datake dashi, tun lokacin da Ali yaji Manga nada ciki baya cikin nutsuwa yarinya duktabi ta fige ta lalace akan abinda bataji ba bata gani ba, dukda an haneta gayawa kowa amma wlhy sabida ta yarda dani seda ta sanar dani, amma ke Ammi kirana ma kike zancen waiko an saketa, Lallai wannan san kan naki ya tayar mun da hankali, bantaba ganin mutum me masifar sankai irin naki ba" shiru yajiyo alamun uwar ce ke zazzagawa er masifa ya sanya ya juya yabar dakin zuwa bangaren Ummu da sauri.....

Mom N'aiym ce

Kumun uzuri inata hidima shisa.
*HASKE WRITER'S ASSO. (Home of expert and perfect writer's)*

*👑ALI ABBAS👑*

*Billy Galadanchi*

*Sadaukarwa gareki qawa tagari Fulany saddy*

14

Wayanshi ne yayi qara ya zaro ta jin yanayin sautin dake tashi ya tabbatar wa kanshi cewar me martaba ne, Dagawa yayi sannan yayi sallama a hankali

"Kazo ina san ganin ka yanzu a fada" ya kashe kawai dama haka me martaba yakeyi idan ya gama fad'ar abinda ze fada seya kashe kawai, dafe kanshi yayi ya juya akalar shi zuwa fada yana mejin haushin wannan kiran ainun......

Huddy na kuka tace da mamanta "Ammy amma dai aikinsan cewar ba'a barin aikin Allah ayi na bawansa, ni nasan niyyan Alkhairi nake da sabida haka tsinuwarki bazata kamani da yardar Allah" tana gama fadar hakan ta kashe wayarta ma gabaki daya ta dauki hanyar b'angaren ummu zuciyarta na mata wani irin rad'ad'i shirkafa ai dole ta nemi zarewa ma gaba d'aya wlhy...

Tana zuwa akai mata iso, taje bayan sun gaisa da ummu se kuma wasu sababbin hawaye tace murya na rawa

"Ummu dan Allah karkiwa magana ta mummunar fassara wlhy banida masaniyar abinda mahaifiyata ke aikata se sati biyu dasu ka wuce, kuma nayi mata nasiha da wa'azin abinda take ba kyau amma batajiba wannan ya sanya nace ni agaskiaya zanzo da kaina na sanar dake halin da ake ciki, zancen cikin nan na Manga Ammy nane taje ta sanya akayi asirin da aka turo mata aljanin dake sanya ake ganin cikin koda a awon asibiti ne kuma yaketa hura cikin yake girma tamkar cikin gaske, wlhy ummu ba yanda banyi da itaba amma sam taqi ta gane taje ta sanya a karya asirin tunda ni nasani babu zaman lafiya tsakaninta da yaa Ali tunda gani yake shiba cikinsa bane ba, yanzun ma da ita na gama waya ta kasa ganewa ta tubarwa Allah ta raba er mutane da wannan takaicin datake ciki, yarinya duk tabi ta gama ramewa ta stuke ta lalace akan abinda bataji ba bata gani ba sam shine kurun nace nizan sanar dake, anemo malamai suyita adu'a ko Allah zesanya asirin ya karye kuma a tayani yiwa Abbin Ameer haquri wlhy ba laifi na bane banmasan da wannan abinba se daga baya" Nisawa Ummu tayi acikin zuciyarta tana godewa Allah daya karbi adu'arta gaskia ta bayyana

"Ki kwantar da hankalinki huddy nina sani wlhy ba hannunki aviki koda baki fada ba, sanida na yaba da nutsuwar da addininki tuni, so ban taba zarginki ba,kuma Har a wurin Allah bakida laifi danke akayi amma kika nunawa duniya kinfison waninki akan kanki lallai kin cika er halak kuma darajarki da qimarki ayau tafi ta duk wata mace da yaro ze auro agidannan dama wacce ke ciki,k8nyi abinda dubunki bazasu yiba Allah ya miki albarka ya sanyaki a aljannar sa mad'aukakiya, ni zan sanar da yaro dame martaba se asan matakin daza'a d'auka akai inshaa Allah, mahaifiyarki kuwa kina mata adu'a plss karki wani en damu zata gane gaskia ne inshaa Allah ta tuba kedai kiyi mata biyayya indai bata sab'a abubuwan Allah daya gindaya wa bayin saba" Yaudai ta kasa hakuri kwanciya tayi saman jikin ummu tayi ta kuka tana rarrashinta har Bacci ya kwasheta a wurin.....

Sosai me martaba ya tsorata da al'amarin mutane amma seya sanar wa Ali Abbas da Ummu kar wanda yayi wa Manga maganar ze kawo malamin daze yaqi abubuwan a hankali.

Yaudai banda sauri babu abinda Ali Abbas keyi so yake yaje yaga Manga koda kallontane ya dingayi, da sallamar shi ya shiga cikin d'akin nata kasancewar ya duba sosai parlor batanan, halin daya saba taddata aciki yauma aciki ya taddata, tana zaune saman sallaya ta rafka tagumi,jin sallamarsa besa dakoda motsa ba se bakinta datake motsawa a hankali wanda ya tabbatar masa cewar amsa sallamar takeyi, abakin gado ya zauna yana jiranta yau seya tsinci kansa da mugun tausayi dajin kunyarta fiyeda kullum, se yanzu ya gano tsananin damuwar datake ciki,se yanzu yake hango gaskiyar ta,yanayin ta kawai ya isa ya sanarwa me lura da hankali cewar lallai she's innocent, tajima a zauna kanta taso, nesa dashi ta zauna da wannan qaton cikin daze kai girman cikin en shida, gashi ajikinta shi kad'ai yake girma komai nata yana nan yanda yake lafiya lau kawar kanta tayi gefe d'aya tunda ya gama zazzaga mata wannan uban zagin takejin wani matsanancin tsanarsa na qara d'arsuwa a ranta da qyar ta furta

"Ina wuni" tausayinta me tsananin gaske ya mugun kamashi muryarshi na rawa yace

"Lapia lau, na ganki wani kala yau, menene yake damunki?" kallon mamaki ta mishi dama kuma tanada damuwar setace dashi

"Kasan ance idan yaro ya mutu acikkn uwa mahaifa rub'ewa takeyi uwar ma ta mutu idan ba'a gane da sauri ba, naji ance ciki yana motsi na bantab'a jin motsin dan Allah ka kaini gun Aunty huddy ta dubani" Wani uban tausayinta yaji ya kamashi daya sanya ba shiri yaje gareta ya rungume kasa daurewa yayi yau kad'ai tausayinta ya sanya ya soma yi mata kuka tamkar wani jinjiri
Chapter 19 · 0% Book details