← Book details Ali Abbas Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 38

Sashe 34

Ali Abbas Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Bansan irin hakannan wlhy, idan ke baki san darajar mijinki ba nina sani, idan kuma ke bakisan lafiyarshi itace gatanmu ba toni na sani, gwara na gayamai me kikai masa sabida gove idan kin kawo mai ruwa a kofi ya dena sha,kinata wannan rawar jikin sekace wacce ke shirin yin kisa, kokinji nace kinyi wani laifi ne? Ki nutsu kinji ba yauwa" kallon Ali Abbas tayi

"D'azu ina zuwa kithen na tarar da wannan cup da irin qatuwar tsutsar nan me gashi aciki, masu sanya gabaki daya quraje su fito ajikinn mutum, shine fa nacewa buwa a jefar da cup din shine wannan matar ta hauni da zagi wai ba ubana bane ya siya mata kayan dazance a wurgar, nabata labarin illan tsutsar shine fa zagi ta uwa ta uba tace a jefar da tsutsan a wanke mata cuo din ta,yanzu sabida taga qarshena shine ta zuboma ruwa aciki,nikuwa bazan bari kasha ba  wlhy" Kallon sa ya mayar ga huddy daketa mayarda numfarfashi cikin kasala, taji dadin rufin asirin da manga ta mata cox wannan dukme sauqi ne ai

"Mesa zaki kawon ruwa acup din to? Sabida kishi ne kokuma kasheni kawai kikeso kiyi?" matsawa tai kusa dashi ta kamo hannunshi

"Haba Abbi yazakace inaso in kashe ka? Nice fa hudaisan ka Abbi, wlhy mantawa nayi dabadan haka ba dana kawo ma a wani dan Allah kayi hakuri" murmushi ya sub'uce masa ganin dukta damu lokaci d'aya ya gaskata cewar kuskure ne da mantuwa

"Shi kenan a kiyaye gaba plss,irin wannan qwarin sunada had'ari kinga be kyautu ace ana mantawa da inda sukaje ba,gashi damunane be tsaya ba suketa yawo,zansaka ayi maganin feshi seku koma dayan bangaren na kwana daya" yana gamar fadan hakan ya koma cikin parlor din ya zauna abinshi......Juyawa huddy tayi dakinta manga tabi bayanta...

"Aunty huddy inasan sanin ruwan meye kika zubawa yaa Ali tare da swan kikeso ki bashi yasha?" kallonta huddy tai

"Manga wai ina wasa dakene?" murmushi manga tai

"Bakya wasa dani amma kina qoqarin cutar da mijina, na duba darajar su Ameer ne ya sanya kikaga na rufe tukunyar asirinki, wlhy kiyi a hankali da bin bokaye da malaman tsibbu inba haka ba wlhy nida kene a gidannan, sabida bazaki zauna kina cutar dashi ba a banza, daga kin gano matar ceni duk kin sauya halaye ina kallon ruwan da kika zuba a cup din baqi ne qirin kina sanya swan suka hade suka dawo fari, wlhy tsafine kurin zeyi wannan kuma kiji tsoron Allah kina aikata shirka a banza a wofi sabida san duniya" kasa magana Huddy tai tagano manga taga komai asirin ta kurun take rufe wa,juyawa manga tayi Ali ma dake bakin qofar ya koma ya zauna da sauri jin shiru alamune na juyowa za'a fito yana mamakin sauyawar halin huddy gakuma mamakin wai baqin ruwa ya sauya launi zuwa fari a cup, manga na fitowa tagama fusata shi d'inma bata kalleshi ba ta nufi d'akinta, tana zuwa dining ta manta zancen kwalbar cup data fashe ta taka daya qara ta k'walla ta sunkuya a wurin riqe da qafar, da sauri ya taso yazo ya riqeta yana tambayar ta lafiya, qafar data riqe ya kall,glass din ya kafe a ciki yana ta zubar jini, ya sake kallon ruwan a saman farin tile din sunyi baqin qirin dayan barin kuma fararen ruwa na gangara wanda sukai baqin kuma sun cure wuri d'aya, mamaki sosai yake huddy kasheshi zatayi kenan?? Akan tagano tanada kishiya anya ba manga ya dace tai wannan haukan ba kuwa? D'agata yayi zuwa kan kujera ya cire mata glass d'in a qafanta sannan yace yana share mata jinin da hanky dake hannunshi

"Baki kula da glasa d'in bane Hilwa?" qwallan datake tarewa ne ya silalo mata ta sanya hannu ta share su sannan tace

"Shap na manta wlhy banma kulaba" cikin tausayi yace

"Sannu Hilwa inaga se munje chemist ko hospital ma deep ne abin" kwab'e fuskan ta tae

"Yaa Ali me zasumun acan,dan Allah karka kaini,ka sanya mun kananzir jinin ze tsaya" harara ya wurga mata

"ke kina haukane kananzir kinsan chemical nawa ne aciki,maza ni ki tashi mu tafi" tabare fuskan tayi lokaci d'aya sega hawaye sharr be kulata ba ya d'agata suka bar gidan zuwa hospital har lokacin yana tsananin mamakin mugun abinda huddy ta aikata masa ko meye ribar ta oho......

Har akai kwana biyu baya kulata tayi ba ban vaki har ta gaji ya gagara sanar mata me kunnen sa ya jiye masa, ko Manga be sanar wa komai ba game da yaji zancen su, haka ya shirya ya wuce batare daya koda kulata ba ko mata sallama, abin duk yabi ya dameta, Manga ma bayan kwana d'aya ta sameshi a lagos da jirgi ta tafi....

Ammyn huddy ce tsugune a gaban boka tana sanar masa komai yanda ya faru, bayan ya gama saurarenta ya soma bugun qasa da kuma bincike binciken sa, a haka ya gano tare sukai tafiya ma suna dubai, ya gayawa Ammyn huddy ya qara da cewa

"Aljani zan tura ya shiga jikin ta ya sanya tae wata qasar daban daba tamuba bakuma inda ya dosa ba dan daganan Madina zashi, to tsayawa saka masa qiyayyar ta b'ata lokaci ne sabida haka zamu sauya akalar rayuwarta zuwa wata duniyar tare da sanya mantuwa a cikin kanta na duk wani abu data sani har abada" murmushi Ammyn huddy tae

"Madallah mun gode, yanzu meye ladan aikin?" wani zabura yae yace cikin ihu

"Mahaifar erki shine ladan aikin, idan kinso ki amince nizan tura a cirota idan kuma kinso ki gayamata, sedai zata iya yi mana gaddama"

"Nima 'ya'ya na nawa a duniya, ta samu mace da namiji, sun isheta rayuwar duniya aciro mahaifar aiba dole" wata mahaukaciyar dariya ya kwashe da ita yace

"Kije angama karki damu!!!" haka tabar wurin tanata murna ta sanya a ranta seta sanya anma kasheta gaba d'aya kowa ya huta kawai..

Kwance manga take asaman doguwar kujerar dake cikin parlor d'in, sanye take da yaloluwar rigar bacci iya gwiwa,tayi kyau matuqa sosai acikin rigar sumar kanta baje saman throw pillow na kujerar datake kai, wayanta take danna wa sanda ya shigo ya je ya janye sumar kanta data baje a kanta ya sumbace ta a goshi sannan yace

"Hilwa er dubai, kinga yanda cikin kwana ki biyu kikai fresh kuwa,lallai ke ba kalar Nigeria bace bazamu koma ba" Murmushi tae ta sanya ta shafi sajen fuskarsa,sunyi kusan dasuke jiyo bugun zuciyar junansu tace

"Kasan dai kafini jin dadin qasar nan, kalli yanda yanda kai kumatu,kuma Allah na iya kula da miji,a jikina fa kake bacci har safe,gashi kuma abinci ma sekace se a baki" dariya yayi yace

"Dakike ta tatsa na kamar me,kinga ni wanka zanyi zo muje ki tayani" murmushi tae

"Sanyi nakeji Yaa Ali, kaje kayi kayanka,idan ka gama zan tayaka shiryawa" hancinta yaja

"Zaki shafamun mai da turare da komai da komai" murmushi tae

"Rigima dai kakeji, yau ba wani wanka dazan sakaka,sedai kai ka sakani "

"Dama kin huta abinki, Auwal friend d'ina yana waje yana jirana, zamui wani lissafi" dariya tayi

"Ba komai kazomun da ice cream" wucewa yanayi yana murmushi da tsananin jin dad'in rayuwar dayake da Manga ya jima sosai yana tafkawa kanshi kuskure da qwarar kanshi" Kamar an tsikari Manga haka taji, haka kawai ta dire wayarta tayi hanyar waje, kofar d'akin ta bud'e ta fito ta soma tafiya gashi batada maraba da tsirara ita kanta bazatace ga inda ta nufaba, tadai san cewar babu nutsuwa akanta bata tunano komai daya shafi rayuwa......

Auwal daya ga manga mamakine ya kamashi amma ganin ko horn aka mata ta tsayawa se tsallaaken titi takeyi ya sanya ya fara tunanin da wata matsala binta yakeyi da qafa lokaci daya yana dannawa Ali Abbas kira ba qaqqautawa shi kuwa se faman shiri yake a gurguje yaqi daga wayar gani yake tamkar dan yana jiranshi a waje ne ......

Wata motace tasha gabanshi, kafin ta d'aga ya duba qasa da sama bega Manga ba, har tsorata yae ya soma ambaton Allah, yasan yanda me gidanshi kuma abokinshi ke tsananin qaunar Manga ya kuma kula sosai batama san inda kanta yake ba, adaidai lokacin ne wayanshi ya qara da sauri ya d'aga ganin Ali Abbas

"Auwal baka reception?" murya na rawa yace

"Yallab'ai, Manga ne ta fito da wannan rigan bana tunanin tasan inda kanta yake, gani nan kan hanyar dera market kuma ta b'acewa gani na sam, mota yakai biyar daya kusa kad'ata" tunowa yae dabe ganta a parlor ba kuma bata daki,wato sabida yana sauri be kula bata dakin ba da sauri ya ce

"kaman ya wai kana nufin da wannan rigan ta fice,yanzun nan muka gama magana, yanzu tsaya ma kai kana ina?" misalta mai komai yayi ya soma tiqar gudu zuwa hanyar...... Yayinda Auwal neman duniya yayi be ga koda me kamar Manga ba!!!!!!!!!

*Fan' s ina godiya da qauna, se kuma bayan sallah idan Allah yaso* Allah sa manga ta bata,haba haka kawai tazo ta raba masoya

#Team Huddy sak# Ana tare.
*HASKE WRITER'S ASSO. (Home of expert and perfect writer's)*

*👑ALI ABBAS👑*

*Billy Galadanchi*

*Sadaukarwa gareki qawa tagari Fulany saddy*

       27

Koda Ali Abbas yazo  adu'a d'auke a bakinshi sabida iya tashin hankali ya shiga ciki, 

"Ina kaga tabi ne?" ya tambaya a razane kanya bashi amsa ma ya hangota wata mota na shirin kad'e ta wani balarabe ya sanya hannu ya janyota da qargi ta fad'o j8kinsa, wani sanyin ganinta yaji lokaci d'aya wani azababben kashinta ya tasowa Ali Abbas da gudunshi ya nufeta har tsere suke shida yaron nashi karban ta yayi yana isa yace yana kallon ta "Hafsa lapiya kuwa? Mesa kika fito kuma a haka" kallon rashin sani ta masa tace
Chapter 34 · 0% Book details