Sashe 22
Ali Abbas Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Taimaka mana zakayi ka kaimu gun hukuma ko sarkin garinnan, wlhy yan shan jini suka kamamu, se bayan kwana uku abinci se yanzu Allah ya tserar damu muka yanko daji muka iso nan,gashi sabida muna tsirara kowa se gudun mu yakeyi, wannan hijaban ma wancen shagon dasuka gudu na kwaso mana su da kokai ka ganmu dole ka gudu anata mana kallon mahaukata" sosai ya gamsu da bayanin ta yace yana zuwa, yaje ya gayawa abokan kasuwan cinsa take aka rakasu gun sarkin Jega mutum adili me karamci, ba jimawa kuwa ya saurari komai da manga tazo mai dashi aka shigar dasu cikin gida aka basu abinci sukayi wanka sannan ya sake kiran Manga ya kula itace shugabar taron, haka yagama jin inda tafito cewar surukar sarkin musulmi ce yace ilai kuwa aranar zasu sokoto.........
Koda sarki yagan su sam be wayi Manga ba amma ya gane muryar kamar yasanta, haka ta bayyana komai se a sannan ya kula sosai manga ce, media da cops ya kira aka taru akazo jin zancen manga beko kira su ummu sunsan me ake ciki ba, kuka kuma agaban media yayishi sosai akan rashin kulawar gwamnati na tura sojoji yawon dazuka domin ceto rayuwar bil adama da ake sacewa ana cutar dasu, kowa yaga Manga baya shaidata seya qura mata ido, farin ma babu shi ko kadan ga kan qwam ba komai a ciki, a wannan lokacin kuwa Ali Abbas na bangaren su ba lafiya ko tashi da qyar yakeyi duk akan rashin Manga....
Sanda aka kaisu dukkansu gun Ummu ba qaramin kuka tayi ba,kuma karo na farko kenan dataje da kanta b'angaren su huddy tun bayan aurensu, ta sanar wa Ali Abbas yanda ake ciki cewar matarshi ta dawo ga bayanin labarin ta, sega mara lafiya a tsaye lolxxxx ba shiri ya bazama bangaren ummu, yaudai har Manganshi da kanta ta rungumeshi agaban ummu tana tsananin mamakin ramar dayayi da baqi sosai.....
Mom Nu'aiym.......
Vote plssss
*HASKE WRITER'S ASSO. (Home of expert and perfect writer's)*
*👑ALI ABBAS👑*
*Billy Galadanchi*
*Sadaukarwa gareki qawa tagari Fulany saddy*
*Ina godiya sosai pheey da alkhairin ki, Allah ya saka miki da alkhairi ya bar qauna,wannan shafin nakine ke kadai kiyi yanda kikeso dashi*
16
Koda Ali Abbas ya d'ago ya kalli Manga yaga yanda ta dawo se kawai ya sanya wani kuka me ban tausayi, wai Manganshi ce ta dawo qwarangwal tamkar ka busa ta fad'i, manga fara ta dawo baqa, Manga gajeruwa ce sedai ba cancan ba amma fa yanzu gabaki d'aya tayi wani tsawo sabida a bushe take, juyawa yayi ga ummu yana kukan yace
"Ummu kalli abinda aurena ya janyowa Manga? Kalli dalilin aurena abinda Manga ta zama, sam wlhy ban cancanci zama mijin Manga ba, tun ranar dana tsoma rayuwata acikin tata take fad'awa iftila'i iri iri, dana riqe igiyar aure da muhimmanci dabata shiga cikin wannan masifar ba,yanzu mezance wa iyayenta irin wa ennan musibun haka" hannunshi ummu ta kama
"Ka nutsu babana ka sani sarai bakajin dad'i godiya ya dacewa kawa Allah daya dawo mana da ita da rai dan bazamuce da lafiya ba sedai adu'a kawai, yanzu me martaba yace a dauketa a je da ita asibiti su mata qarin ruwa da sauran gwaje gwaje, sannan ta kwanta ta huta acan kuma dole amata adu'o i sabida sharrin matsafannan dabazamu san me suka mata ba ajiki, idan kana haka ita kuma fa ya zataji? Ka nutsu kawai kamata adu'a" shiru yayi yana me tsananin tausayawa Mangan shi.....
*Bayan kwana bakwai*
Inno kam tasha kukan ganin yanda Manga ta dawo qata abar tausayi, tamkar ba ita ba, gabaki d'aya halittarta ta sauya dukuwa da yake sunzo ne bayanda komai ya lafa awurin manga sabida a kwana biyunnan harta wartsake ta soma cikowa, Kallonta tayi bayan kowa ya wuce adakin asibitin daga Manga se Inno tace da ita
"Mangan Innoh yau dai zan sanar miki tarihin rayuwata data mahaifinki abinda kika dad'e kinaso kiji, da farko dai mahaifinki sunanshi Ibrahimou Ahamadou mousa, sanin kowane har yanzu Ahamadou mousa shine sarkin garin yamai dake qasar Niger wanda tun shekaru arba'in dasuka wuce shine akan karagar mulkin, mahaifinki mutum ne da yake da kyakyawan usuli kasan cewar sa d'a d'aya tilo a wurin me martaba sarkin yamai Alhj Ahamadou mousa, yasanya ya taso a sangarce kuma cikin gata mara iyaka, tun a wancen lokacin a wajensa yayi karatu acan france, bayan ya kammala karatunsa ya dawo ya had'u da wata yarinyar er bawan gidansu,soyayyar gaskia ta haqiqa yake yiwa Aicha kazalika itama tana tsananin sansa, sun gama shirya cewar zasuyi aure yaje ya gabatar da ita awurin me martaba, amma qememe me martaba yaqi amincewa da buqatarsa, babu yanda beyiba,ba wurin wanda be jeba amma me martaba yace baze taba zubar da martabar masarautar saba ta hanyar aurawa sarki me jiran gado yar bawa ba, daga qarshe dai ina zaman zamana, mahaifina wanda ya kasance sarki a jihar agadez dake Niger ya umarceni akan auren d'an sarkin yamai,ni a wannan lokacin banida wani tsayayye kasancewar bama inda nake zuwa, dayake ni nafito a cikin dangi gaskia ba kamar mahaifinki ba dayake shi d'aya tilo ba wa ba qani awurin mahaifinshi da babarshi, Ranar daya soma kawomun ziyara yamun gargadi akan nace bana sanshi, ya sanar mun lallai zanyi bankwana da farin ciki kamar yanda zanyi bankwana da en uwana duk na sake aka daura aure na dashi, ban baiwa maganarshi muhimmanci ba haka kuwa aka daura aurena dashi bayan ansha biki na tare da kwanaki tara ranara ya tasheni da dare a haka ya sakoni a kotarsa muka bar gidan su, washe gari kuwa da kanshi ya tuqomu har Nigeria muna iskwa yaje ya sayarda motarshi munsha wuya sabida bamajin hausa sosai... Haka inaji ina gani mahaifinki yace tunda yake sarakuna basa san yaransu suna rayuwa da talakawa,kuma suke tauyewa talakawa haqqinsu suna nuna cewar lallai talaka qasqastaccene to kuwa se yaransu sunyi rayuwa irinta bayi ya da sukeji idan an wulakansu seya saka suma an musu koda iyayen basu sani ba dai yasan ammusu, da wannan ya nemi gadi sabida baya sona ya sanya duk sanda nayi ciki ya asa masifa kenan akan sena zubar kafin ya zubar se kiga cikin yafadi da kanshi, haka dai inata hakuri sabida yace idan nayi yunqurin komawa garinmu abakacin aurena nidashi, harna samu cikin ki, cikin ikon Allah daga ni harshi bamusan da cikin ba sabida ina al'ada ta har tsawon watanni sannan na soma jin motsi naki gaya masa, har seda cikin ya bayyana kanshi lokacin yakai watanni 6 abin mamaki senaga yana murna tun lokacin daya san da cikinki sena soma ganin sauyi tarayraya ta yake yana kuma nunamun kulawa matuqa, ban damu ba dai haka naita daurewa da halayenshi, dama ni gaskia inasan iro wannan ma yasa sam ban ganin laifin sa ko kadan a irin azabar dayake ganamun,a haka harna sauka lafiya, zan iya cewa soyayyarki ce ta haifeni wacce harta sanya komai na yanayin qiyayyar da mahaifinki yakemun ta sauya zuwa soyaya me ban mamaki, a haka a haka dai har kika zama abinda kika zama yanzu, babu yanda bana roqarshi akan komawar mu gida amma sam yaqi, se wannan lokacin ya yarda da zuwan mu gun en uwansa, a yanzu haka daga zaran kin murmure tare dake zamu tafi" mamamakin jin asalain su ya kama manga ta jinjina kai kurin tana me al'ajabin halayen mahaifinta na kafiya.....babu kalan gatan da Manga bata samu har aka sallameta ta koma gida, babu wanda ya qara zancen tafiyar su Niger seda tayi good 2 month ta dawowa jikinta tayi kyau sabida hutu gashi ana yawan mata adu'a se ta dawo tamafi da yin kyau da komai, a wannan lokacin kuma baban Manga yayi bayanin komai wa me martaba dan gane da asalinsa da dalilin barowarsa gida dakuma dalilinsa nasan komawa sabida ya nemi gafarar iyayenshi musamman mahaifiyarshi da mahaifinsa, ya kuma roqi alfarma abashi manga domin ya gabatar da ita wurin mahaifansa, ba gaddama Ali Abbas ya amince da zancen tafiyar yaso ya tafi tare dasu amma se me martaba yace tunda sunce wata daya zasuyi ya bari in zasu dawo seyaje su dawo tare.....
Sun jima a tsaye suna kallon kallo tsakanin Ali Abbas da Hafsatu Manga, lallausan murmushi ta sakar masa, ta gama sakewa Ali Abbas ragamar zuciyar ta, ta gama yadda yanzu wahalar da kanta kurun takeyi Ali Abbas shine masoyinta,bazata rayu bashi ba, huddy da kanta ta sanar mata kalar azabar dayasha akan rashin ta har ciwon hawan jini ya kamashi, tace cikin wasa
"Yaa Gadanga zaka cinyeni ne wai" murmushi yayi shima yace
"Dole in kalle ki Manga wata d'aya fa zakiyi a wata qasar, gashi baki barni da wata ajiyar bama dazanna tunawa dake" wara ido tayi tana murmushi tace
"Zan baka ajiyar zobe mana kalan yanda kayi sanda zakaje soba daga kaduna" Dariya ya gano gayya take masa ya matso daf da ita ya had'e hannayensu wuri daya ya matse nata seda ta qwalla qara "Yaa Gadanga da zafi Allah" waist d'inta yakai hannu ya matsa seda ta sunkuya tana dariya
"Gobema ka qara tsokana na, yanzu muje d'akina in baki wani saqo" maqe kafad'a tayi "Bazan bikaba kamun mugunta Allah kuwan, nidai kaga su Inno ni suke jira kurin ka tafi" kallonta yayi "Aunty Manga dan Allah zan biki" murmushi tayi tasan yanda ya mat sanda ze gudu ya barta, rungumeshi tayi tana bubbuga bayanshi a hankali kalar dai yanda ya mata sanda ze gudu ya barta, sannan ta sanya hannu ta tallafo habarshi tace bayan ta sumbaceshi a kumatu
"Kayi hakuri yaa gadanga, nima badasan raina zan tafi in barka ba, ka kwantar da hankalinka ba dadewa zanyi ba wata daya kurin zanyi" ya tuna sanda abun ya faru murmushi yayi yace aranshi Manga so take kota yaya seta rama komai daya mata kenan, yace "Allah ya kiyaye hanya" murmushi ta kuma yi
"Jeka dakko kayanka zan jiraka a mota mu tafi tare" sannan ta juya bayan ta barshi a tsaye, jikinsa ne yayi sanyi yana tunanin mesa ta masa haka, Kaddai ta masa nisa na har abada, da kuwa ya shiga ukunsa ba kad'an ba......
*Yamai Niger republic*