← Book details Ali Abbas Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 38

Sashe 36

Ali Abbas Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Wlhy muhammad kasani tun aurena danuwarsu hudaisa nakeshan baqin cikinta kala kala, ko wancen batan da manga tayi wlhy da sanya hannunta,ayi mace ba imani yanzu nasan akwai wani a qasa, sabida bakasan dajin da aka samo motarta ba, dajine me nisan gaske wanda harya keta qasar mali, ni koda naga motar a hoto nasha mamaki en sanda ma acan suka barota sabida ba wayanda nabaiwa report bane suka ga motar sojojin da aka tura kwantar da tarzomane, kaga wannan shine tayi sharri ya dawo kanta tunda gashi Adama tace Ali ya sanar mata, ita batada mahaifa dayan matana ma ta sanya anyi tsafi an cire mata yanzu tacire ta erta idan ka duba duk sharrin kanta takeyiwa sabida neman abin duniya, nidai babu inda zanje nemanta wlhy kuma na saketa saki biyu idan an ganta asanar mata karta takomun gida, ke kuma huddaisa wlhy kika qara cutar da manga da gangan koda ta hanyar taka mata dan ya tsane indai da niyyar mitgunta ne Allah ya isa ban yafe miki ba, kije ki zauna da mijinki da kuma qanwarki lapiya ya fiye miki zama alkhairi sokuwa kawai dabatasan ciwon kanta ba, ke yanzu banda kike sakarai Mangan kike kishi da ita? Yarinyar da kike riqe kusan shekaru hudu idan kinada adalci ai abin a tausaya mata ce shine tsabar sankai kike shirme" kuka ta sanya ta dinga bashi haquri harseda me martaba suka sanya baki sannan ya haqura tanaji tana gani yace bazata jira harse anga uwartaba ta wuce Madina gun mijinta ta nemi gafarar sa.

  Manga kuwa ciki yaqi ya bada had'in a angwance bata iya cin komai se tea da bread, dukta wani yamutse,shi kuwa se nan nan yakeyi da ita...yauma kamar kullum kwance take tayi matashin kai da cinyarsa yana shafa gashin kanta a hankali yace

"Hafsatu Manga inaso in sanar dake wani abu kuma banso ki tashi hankalin ki plss" gyaran kwanciyarta tayi

"Inajinka yaa gadanga indai ina tare dakai bana tunanin akwai wani abin daze d'aga hankali na har abada,koda hankalina ya tashi ma nasan zaka kwantar mun dashi" murmushi yae

"Manga ki sani Huddy koda ba matata bace itad'in er uwarki ce, bakida wani hurumin dazaki aminta da qaddarar da Allah ya gindayawa dukkaninku a matsayin ku na matana, Huddaisa zatazo Madina itama kuma tare da yara zatazo,na kula kina da tsananin kishi to ina rokonki da Allah ki rage nuna mata wannan kishin a zahiri ke kanki abinda kike mata sam bakya kyautawa koba komai ta cancanci ki mata kawaici sabida tin farko ta karbeki juyar mata da kai ne akayi, kuma yanzu ta gane komai so dan Allah ki bata girmanta ita kuma zan mata magana ta dauki abinta ta girmamaki kema" qirjinta ya d'an doka ta d'ago ta kalleshi tace

"To anan d'in zamu zauna dukanmu ne yaa Ali?" shafa kanta ya qarayi ya kula qirjinta ya doka

"Ba anan zamu zauna ba Manga nan ai hotel ne,kinsan saudi akwai tsaro sosai, dole sena jira an mana katin zama en kasa, sannan mu shirya kama gidan zama, sabida ni a nawa tsarin nida Niger kuma ba yanzu ba gaskia zanci gaba da aikin dana soma kuma tun kafin nazo an shirya komai na samu sun mayar dani" nisawa tayi ta shagwab'e fuska

"To kaima dai yaa Ali ka dena kakkamata a gabana kana mata kiss" murmushi yae yace

"Na dena idan shine bakyaso amma dai a kiyaye a zauna lafiya plss" 

*Bayan kwana biyar*

   A haka su huddy suka sauka tun a airport jikin dukansu su biyu  ya mace sabida ko wacce kishin er uwarta take,Manga sororo tayi ganin yanda Ali Abbas ya nuna tsananin murnarshi ganin huddy atake ya rungumeta yakuma sumbaceta a kumatu tare da rungumar yaranshi duka biyu ya manna musu sumba suma, sun gaisa kafin huddy ta tako ta rungume Manga hade da riqe hannunta

"Er uwa kin rame meyake damunki?" murmushi tayi tace "Zazzab'i nake Aunty huddy amma na warke" kallonta ta mayar gun Ali Abbas tace

"Zazzab'in lapiya kodai yaro nane ze sauka inji Allah" murmu shi manga tae ta sadda kanta qasa lokaci daya ta tsinci kanta cikin tsananin jin kunyar kalaman na huddy, shi kuwa Ali Abbas cewa yae

"Ke muke jira ki gano mana bakin zaren babbar likita"  dariya sukayi dukkansu sannan suka juya zuwa mota, a hotel suka sauka inda su Manga suke anan ya raba musu daki, inda bayan lokacin kwanciya yayi seya barwa manga su Ameer shi kuwa yaje dayan dakin da huddy, sun jima suna magana da dirzar soyayya kan daga bisani su zanta game da yanayin ciwon huddy ta gaya masa lallai batajin ko dayan nonon nata yana mata ciwo wanda suka yanke hukuncin zuwa ganin likita anan madina!!

  *Bayan watanni biyar*

Zamane aka ginashi da amana tsakanin wannan mijin da matayenshi guda biyu, Manga kam ciki ya tasa watanninshi shida da kusan sati biyu, idan ka ganta bazakace da ciki ajikinta ba sam, mahaifiyar Huddy kuwa ko labarin wanda yaga wacce tai kama da ita ba a ganiba, anyi nema har an cire rai amma ba labari.....Huddaisa kuwa ciwon nan ya ciwo qarfinta ya tasota agaba kullum qara tasowa yakeyi, gashi sunyi wata uwar shaquwa da Manga idan ka gansu zaka dauka sister's ne bawai kishiyoyi ba, zaman lapia suke me ban sha'awa, huddy abubuwan sun mata yawa ga rashin ba'aga mahaifiyarta ba ga azabar ciwo Manga na kulawa da ita sosai tamkar mara juna biyu....

  En kwanakinnan gaba d'aya huddy a rikice take, harma an kwantar da ita a asibiti, batada lapiya haryakai batasan metake ba,ta dawo se fauwalawa Allah lamuranta tayi tanata istigfari da adu'o i zuwa yanzu ta gama yaddarwa kanta cewa rayuwarta bame tsayi bace, likitocin sun tabbatar cancer dinta ya dawo ga dayan maman ta gashi ba mahaifa abubuwa goma dasha biyar,sumar kanta ta gama kakkab'ewa ma kaf, yaudai gabaki daya a rikice ta wuni se neman gafara takeyi tana kuka da barin wasiyya,  akan yaranta da mahaifiyarta idan an ganta, Ali Abbas kasa tsayawa wurin yae sabida shima jikinshi ya mutu se manga ce tsaye riqe da hannunta tana mata adu'a a hankali taga ta soma yin laqos mamaki ya kama manga ta kalli injin da hancinta da bakinta suke ciki idanta ya wani birkice, tsoro me tsanani ya shigeta, ganin hannun ta saki ya tafi luu ya sanya tabi hannun shima da kallo, lokaci d'aya taji maranta yayi wani irin Murd'awa,dafe marar tayi ta kasa koda motsi se yarfe hannaye take, a haka Ali Abbas da doctor suka shigo suka sameta, kai tsaye doctor wurin huddy yae yayinda Ali Abbas yariqe Manga yana tambayarta lapiya, da qyar ta iya furta

"Ka duba Aunty huddy bata Numfashi sam, kalli idanta" saketa yayi ya juya a sukwane, girgiza masa kai doctor din yayi cikeda tausayi sannan ya dafa kafadarshi yace cikin harshen turanci

"I'm sorry to say, she's gone" Gabaki d'aya kan Ali Abbas kasa gane komai yayi,kanshi ya juye gaba daya zuwa wata duniyar yakasa d'aura tunanin sa amizanin fahimta me daidaito, lumshe idanshi yayi sannan a hankali ya mayarda dubanshi zuwa ga Hudaisa kwance tamkar me bacci an shafe mata ido ruf babu alamar numfashi atare da ita,se gani yake tamkar tana masa murmushi matsawa yayi ya riqo hannunta dayayi sanyi qalau yakasa koda zubar da hawaye kukan zuciya yakeyi yasani yakuma ji ajikinshi tun kwana biyu data wuce cewan hudaisa se Allah da tsawan rai amma tayi nisa,Maganar manga ne ta dawo dashi daga duniyar tunani dayaji tana salati

"Bayana nashiga uku" Dr din na mata sannu koda ya juyo gareta ta soma bleeding baiwar Allah, mutuwar er uwarta ya gama gigita tata duniyar, a haka aka kaita wani dakin amma ya zusuyi haihuwa ce da wata bakwai kacal, taci wuya kam amma cikin lokacin dabefi awa biyu ba ta haifo 'yarta er tsito tamkar ba mutum ba, er bakwaini se a kwalba aka direta.....

Allah ya jiqan ki huddy, masu karatu zakuga ina komai a gurguje wasu daga cikinku suka soma qorafi akan inajan labarin, shine zan datseshi abgurguje kowa ya huta.

Mom nu'aiym ce

Masu mun waya da masu mun txt da dm ta wtsp nagode sosai, naji sauqi cikin ikon Allah se Allah ya kaimu shafi na gaba nanan zuwa wanda yake kusa dana qarshe.
*HASKE WRITER'S ASSO. (Home of expert and perfect writer's)*

*👑ALI ABBAS👑*

*Billy Galadanchi*

*Sadaukarwa gareki qawa tagari Fulany saddy*

              29

Ali Abbas duk ya gama rud'ewa arayuwa  besan dame zejiba,gashi sam yakasa gaskata rasuwar Huddyn sa, waya ya d'aga ya kira sume martaba bayan sun gama gaisawa yace da qyar

"Abba Hafsa ta haihu sedai yarinyar bakwaini ce amma tana nan lapia lau" murmushi tsohon yayi yace

"Lallai Ali ka soma tara iyali kace mata naketa samu haka,to Allah ya raya mana madeena ya baiwa uwar lapia,ya wurin su huddaisa kuma, nasan zata kula da ita sosai koda yake ba lapia bane da ita" kuka kawai Ali Abbas ya fashe dashi wanda ya tashi hankalin me martaba cikin gid'ima yace

"Subhanallah Ali lapia kuwa kuka kuma? Da kanka Aliyu? Menene yake faruwa kuma daga labarin murna?" cikin kuka yace

"AbbU Huddy ce ta rasu, gid'imewan mutuwanta ne ma ya haifarwa Manga da tasowar naquda, Ban taba kawowa huddy mutuwa ba yanzu Abba yaya zan rayu idan babu huddy Abbu?" 

"Innalillahi wa inna illaihiraji'uun" itace kalmar da Abbu keta nanatawa bayan jin bayanin Ali Abbas, shi kanshi mutuwar hudaisa ta gama girgiza shi gyaran zaman rawaninshi dake shirin faduwa yayi da hannu d'aya yace

"Ka kwantar da Hankalin ka Ali,kasani ubangiji baya barin wani dan wani anan ko kadan, Inaso ka nutsu ka dinga mata adu'a a maimakon kukan nan dakaketa faman yi, kasani Huddy ta samu rana yau juma'a fa, yaushe abin yafaru?" girgiza kanshi ya dauke majina da bayan hannunshi yaukam maza na cikin rud'u

"Rashin lapian manga ya rudar dani, jira nake ashiga masallacin juma'a se ayi janazar acan inda zata samu mutane da yawa" nisawa abbu yayi yace
Chapter 36 · 0% Book details