Sashe 6
Ali Abbas Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Mangan Inno ki sani koni nan wayannan kalaman iya bakina kawai suka tsaya amma sam zuciyata bata aminta dasu ba, sabida nasan halin Gadanga halinshi ba haka yake ba, bana fatan mutuwa yayi, ammafa ki sani a qa'idar aure idan namiji ya tafi abinshi da gangan harna tsawon watanni 4 tofa babu aure,idan kuwa fad'a yayi toko shekaru hud'u be wa'adin indai muddin be dawo ba dole a raba auren ki auri wani, wannan tsarin ba nawa bane manga na musulunci ne"
Tana kuka tace "Niko shekaru dari gadanga zeyi zan jirashi na tabbatar ze dawo gareni, dan Allah Baban Manga ka dena fadar zancen raba auren nan,wlhy inasan mijina" tausayinta ya kamashi yace
"Allah ya zab'a miki mafi alkhairi Manga, aalhj ya sanar dani ki shirya kayanki jibi zakije sokoto hurin hudaisa, dukda yake nasani cewar bakwa shiri amma haka zakiyi hakuri, a yanda naji batada lafiya ne, kuma ma acewarsa bazakine wurinta matsayin er aiki bane zakijene a matsayin er uwarta ya sanar da ita hakan, zance na gama kije da komai naki na karatu zaki soma makarantar gaba da sakandire acan kan Allah ya bayyanar mana mijinki ko labarinshi, banso hakan ba Amma bazan iya masa gaddama akan lamuranki ba, sabida Alhj yayi duk yanda akeyi ya d'auke ki matsayin 'ya, ki kame kanki ki sani fa danigiyar auren wani a kanki bawai sagaga zakina yin wannan haukan nakiba.... Kuka kawai take, batason zuwa sokoto itakam tafiso ta zauna gida tayita jiran gadangan ta amma yata iya batada zabin daya wuce bin umarnin iyayenta......
*Sokoto*
Koda Manga tazo gari mamaki tayi ganin cewar har cikin jikin huddy ya fito, sedai fa tayi baqi sosai ta rame har tsoro ta baiwa Manga, tunda tazo gidan bataga Ali ba, kodai dan bata fita ko ina bane ohoooo....
Satinta biyu da zuwa wani yammaci tana zaune sega Ali Abbas yazo parlor d'in, tashi tayi ta sunkuya ta gaidashi, ga mamakin ta wannan wasan dayake mata sam beyiba, fuskarnan a hade alamun ba wasa yace da ita
"Ke Manga kikace da huddy bakyason course da aka baki? Me kikeso a miki to? Late admn fa na sanya aka baki, karatun dole sekinyo zab'i a kanshi? Idan kikace dole se kinyi Law idan kuma ba alkhairi bane a gunki fa? Med lab aka baki kuma shi zakiyi, idan kinje ki bari inga sakamako mara kyau kiga yanda zamuyi dake, akwai driver daze kaiki jami'ar gobe ki fara registration" lokaci d'aya taji qirjinta ya doma kuma ta soma wani tsoron shi, muryarta na rawa tace
"Kayi hakuri yaa Ali inshaa Allah zanyi" miqo mata kudi yayi yace
"Ungo wannan keba indigen din nanne dake ba, na kd ne, zaki biya registration sannan kuma ku biya ta bank dashi, na sanar masa ya kaiki gt ki bude acc goben" godiya ta masa sannan batare daya saki fuskar ba ya wuce abinshi.....
Tun daga ranar da ya bata kudin bata sake ganin shiba gashi dai takan jiyo muryarshi sabida part dinsu take zama amma sedai ta jiyo suna raha abinsu shida matarshi, yaune ranar farko dazata soma zuwa lecture koda ta fito wuraren 7 ta ganshi zaune Huddy tayi matashin kai da cinyarshi yana shafa sumar kanta a hankali, kawar da kanta tayi gefe sannan tace
"Yaa Ali ina kwana, Aunty huddy ya jikinki" be amsa gaisuwar tba huddy tace "Naji sauqi Manga,skul din zaki tafi?" kan tabata amsa ta tsinkayo babbar muryarshi yana cewa
"Zonan Manga" zagawa tayi a kunyace tace "Gani" seda ya danja fasali sannan ya saki muryarshi dake da fad'i yace
"Manga ki sani kinada aure akanki, sannan dukkanin abinda kika aikata na batanci Allah yanaji kuma yana gani, kada kiyi amfani da damarki ta ya mace ki cuci igiyar auren dake kanki, inshaa Allah mijinki ze dawo gareki ko yaushe ne, duk abinda kikayi me kyau masarautar nan kikayiwa, idan kinyi mara kyau ma haka, motar da zakije skul da ita ki dawo da ita duk tanada tambarin nan gidan, driver daze kaiki ma na nan gidan ne kowa ya sanshi, dan Allah ki rufa mana asiri ki kare mutuncin aurenki" shiru kawai tayi masa yaci gaba
"Nine nake kula da komai da komai na karatunki, idan kina buqatar wani abu ni zaki tambaya, seki sanar wa huddy buqatunki ni kuma nasan zata sanar mun" godiya ta masa sannan ta tashi ta miqe zuwa skul din....
Allah sarki rayuwa haka Manga ke rayuwa agidan batare data samu wata walwala ba, gabaki d'aya tayi sanyi sedai ba laifi tana karatunta, bata wani ganin Ali Abbas agidan, yayinda kuma sam huddy bata mata wulakanci ko kadan, suna zaman lafiya tadai kula kaman huddyn batada lafiya sosai sabida yanda ta yamutse....
Sana'ar kukan ta kwanta parlor tanayi yau ma ita kadai sabida tasan ba kowa a bangaren huddy taje gaisawa da surukanta, sambatu takeyi
"Yaa Gadanga ga sauarari kukana a duk inda kake, ka gane ina cikin tashin hankali, yaa gadanga yau shekarana d'aya ban gankaba, kasan kuwa abinda nakeji, kasan rashin ganinka meyake sakani ji, bazan manta kaba arayuwa, banida sauran amfani idan baka nan yaa gadanga dan Allah ka taimaki wannan baiwar Allah ka bayyanar mana kanka" ta qara rushewa da kuka me ban tausayi.....Ali Abbas dake bayanta kuwa dafe kanshi yayi dake sara masa, da qyar ya iya d'aga kafarshi zuwa d'akin shi har wannan lokacin batasan da zuwanshiba
"Yaya zanyi da Manga ni Ali, ina zankai wannan tausayin datake bani? Mezan iya yi mata? Mesa arayuwa zuciya batamun adalci ba, tayaya zataso manga matar wani?? Tayaya zan kasa sukuni akan ta, tayaya zan zamto mara amfani agareta, yaya zanyi inga Manga ta dena kuka?? Yaya zanyi inga Manga tana walwala kona samu nutsuwar zuciyata, yaya zanyi da qaunarki Manga????? Ya akayi nayi saken da wani ya rigani mallakar zuciyarki? Kasa hakuri yayi kurun ya soma hawaye......
Hmmmmm
Mom Nu'aiymm
[7/6, 8:07 AM] +234 706 571 7620: *Haske writer's Asso.(home of expert and perfect writer's)*
*👑ALI ABBAS 👑*
Billy galadanchi
Sadaukarwa gareki qawa ta gari *Fulany saddy*
*Wannan shafin sadaukarwa ne gareki ke kadai Jamila sani, kinfi kowa san littafin Ali Abbas, Allah yabar qauna*
*Gareku mom Areef, Rukeey,da kuma fatima Adams, wannan shafin tukwici ne a gareku, sabida k'aunar da kuke nunawa wannan littfin, Ali Abbas yace a gaidaku*
04
Da sallama Huddy tashigo parlor din,yanayin data tadda manga aciki ya bata tsoro, da sauri tayi kanta ta rungume tana neman sanin dalilin kukanta haka tamkar zata shid'e
"Manga Lafiya dai, menene? Koni na miki wani abinne ban saniba?" tana kuka tace
"Aunty Huddy yaufa shekara d'aya amma ko labarin gadanga babu, ina kuke so in saka rayuwata wlhy ina matuqar so da kewar mijina, mutum me tattali da kulawa dani, me lurar dani inda duk na kuskure, yaa huddy idan har ba'aga Gadanga ba banga amfanin rayuwata ba" da sauri ta toshe mata baki da hannunta
"Haba Manga, yaya zaki so kauce hanya akan d'an Adam, idan kikace bakiga amfanin rayuwarki ba idan bashi ashe rayuwar dakikai a baya kenan batada amfani kafin zuwanshi cikin rayuwarki,karki kasance cikin mutane wayanda basa karbar uzurin kaddarar datazo musu mana? Ki godewa Allah mana da tarin tulin ni'imomin daya wadatar dake dasu, kinsan ko koda lafiyarki aka barki kina cikin ni'ima? Wata tana tare da mijinta amma sam baida amfani agare ta,baya kula da cinta bare sha ko suturu, ita ke ciyar da kanta da yaranta, iyaye ko en uwanta basuda karfi, yanzu ashe ba ni'ima bace kinada masu tallafa miki dukda kasancewar sam mijinki be bar miki komai ba, idan mutuwa yayi akwai tanadin da madaukakin sarki ya miki, idan kuma yana raye adu'arki bazata fad'i qasa banzaba, yanzu ki kalleni da kyau ki gani Manga tsaye kawai nake amma sam banda lafiya kuma karki zata wasa ciwone dabaze warke ajikina ba,sedai na mutu dashi ni kuwa me zance?? A ganina ba san kaiba manga jarabawa ta tafi taki dukkuwa dayake nasan ciwo ba mutuwa bane, nida nake da wannan ciwon nayi imani zancen likitoci bawai dole ya zamto bazanyi rayuwa me tsayi ba, sabida tsarin Allah yafi na kowa, dan Allah ki fauwalawa Allah lamuranki Manga" shiru tayi sekuma jikinta yayi sanyi ta qurawa huddy ido tace
"Aunty kuma kema bakida lafiya? Mesa kikace bazaki warke ba? Meyake damunki?" murmushi huddy tai
"yanzu ki tashi kije kiyi wanka kiyi sallah lokaci yayi, kukan ya isa haka ki mana adu'a dukkanmu plss" jiki ba qwari ta miqe zuwa cikin dakinta,yayinda huddy ta miqe tana share kwallar daya zubo mata
Tana shiga dakinbta tarar da Ali Abbas ya sunkuyar da kanshi bemasan da zuwanta ba, zama tayi ta dafa shi tace
"Haba Yaa Ali? Mesa a rayuwa zaka kasa yarda da qaddarar da Allah ya daura mana? Dacen danake rayuwa batare da ansan da ciwon ajikina ba likitocin ne suka rayani? Yaya yanzu dan sunzo da zancensu na banza zaka gagara yarda da qaddara, idan kana hakan ni kuwa mezanyi? Kaine fa babba, ashe ba dagaske kake rarrashina ba kenan, bayan idona seka zauna kanata faman tunani, toka sani ni wlhy nafi yarda da cewar wannan likitan dayace bazan rayu da tsayiba seya rigani mutuwa sabida rayuwa da mutuwa a hannun Allah suke, ni kagama naji sauqi kafin su gano wannan ciwon ma ai kaga ni bantaba kwantawa ciwo ba bare in yarda da shirmensu" shiru yayi yana kallon ta yarinyar nan akwai imani a tattare da ita, ciwon cancer ba abin wasa bane yaga ita ko a jikinta, tundaga zuwa awo aka gano cancer din amma taqi ta nuna damuwarta sam, likitoci sun sanar masa ba lallai ta rayu da tsayi ba, bemasan taji ba se yau kodan kasancewarta wacce ta karanci aikin likitanci ya sanya tasan komai dan shidai yasan be sanar mata ba sam, tausayinta da kanshi yaji sabida besan yaya rayuwa zata kasance masa ba idan ba huddy yayi sabo da ita me tsananin gaske,yana kuma san matarshi tsakaninshi da Allah mabuwayi, rungumeta yayi yace