← Book details Ali Abbas Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 38

Sashe 10

Ali Abbas Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Bayan na nutsu se mahaifina ya turani wani kamfaninshi dake kaduna na sarrafa qarafa ganin nafi qwarewa acan,tunda na dawo gidannan naga yanda bayi kemun tamkar sumun sujjada se abun ya d'aure kaina matuqa sekace ba mutane ba ko kuma rayuwarsu a hannunmu take? Wata rana naje wurin me martaba lokacin ban dade da dawowa ba sena tarar bayi sun zagayeshi anata fadanci ina zuwa se dukkansu suka miqe seda na zauna sannan suka fad'i suna zuba gaisuea yarima me jiran gado waye waye, mamaki nake ya sanya na miqa musu hannu muka fara musabiha nasan haka akeyi abinda na kula dashi shine wasun su suna tsoron bani hannu musabu ladar musabaha, yayinda wasun su gabaki d'aya sun kasa miqo min hannun, ganin haka ya sanya me marta ya kira bayan na bar wurin yake mun fad'a akan bayi cewar nawuce na baiwa bayi hannuna mu gaisa sufa bayi nane, mamaki ya kamani sanida banga wani banbanci tsakanina dasu ba da har zan saki ladar dake cikin yin musabaha da musulmi dan uwana ba,amma dukda haka sena bashi hakuri akan zan kiyahe.

Ba'afi sati dayin wannan ba se kuma nazo zan shiga wurin dawaki na tarar wata yayata dabatayi aureba tana zagin wani bawa dake kulada sha'anin shuke shuken dake gidan tamkar zata cinyeshi, nayi mamakin ganin yanda yakeda qoqarin aiki amma kuskure daya an kasa yi masa uzuri, tausayinsa me tsanani ya shige ni,da wannan na sanyawa raina sanjin yaya sukeji idan aka ci zarafin su? Mesa ba'a musu adalci sumafa mutanene? Yaya rayuwarsu ke musu idan sukayi qoqari amma ba'a gani ba?...." nayi tunani iya tunani daga qarshe na yanke shawarar zuwa nima wani gidan nayi basaja nayi aiki ko wane irine inji yaya yake.......dana sanarwa abokina zuhair seya nuna rashin dacewar hakan amma inada wani hali daya na kafiya da kuma bana sauya zance idan nayi wannan ya sanya na kafe, muna nan haka mahaifina ya turani wannan aikin na Kd senaga na samu opportunity nayin hakan a garin daba nawa ba,da kuma naje America siyo wasu kaya kurin senayi sha'awar yin mask, na sanar musu a duba amun ta daidai skin color dina batare da bata lokaci ba kuwa akamun fuskar, koda na dawo na nunawa zuhair seya b'ata fuska akan karnayi bayaso, ni kuwa na kafe ban shiga tsoro ba seda naga neman aikin ma ashe baze yiyu ba, sabida wuya yakeyi aikin na qarfi ma wuya yakeyi duk inda naje babu......Harna watsar kuma seme martaba ya had'ani da mahaifin su huddy dama kuma tun ina qarami na sanshi aminin mahaifinane, bayan na gama zagayena ban samu aiki ba, wani yammaci muna tare da Daddyn huddy nake sanar masa,jiya na wani nazo nan neman aiki amma ban sanshiba ya sanar dani malamin addini ne amma nace dashi ni baqo ne bansan kowa ba, gobe da yamma nace yazo ya sameka ko ze samu,bansan ma sunan saba, yayi murna yace ze jarraba iliminshi idan yazo, dana tashi gobe sena masa wayan cewa bazan fito aiki ba, sena shirya kamar yanda kikaga inayi nazo wurin shi azuwan nine wancen, ya bincikeni na sanar masan qauyenmu soba da sauransu yace wurin kwana fa nace masa banida matsalar wannan, daga sannan nake masa zagaye duk sanda zan koma sakkwato sena baiwa wani bawa nawa danazo dashi nan aikin kula da flowers na gidanku......Bazan miki qaryaba Manga ban taba sanki ba, amma kwatsam se mahaifinki ya zomun da zancen kuma take a wurin ya sanya namai alqawarin aurekin ko bayan ranshi, babu yanda za'ayi na tsallake sharad'in alqawarin dana d'auka tsakanina da Allah, shine fa naje na samu mahaifina da zancenki amma tsakaninshi da Allah yace bazanmai haka nan ba, dole na haqura babu na biyunshi agarin nan dazan saka yamai magana, naje gun ummu amma kinsani bata saka komai nawa agaba, haka nayita yawo na rasa ya zanyi, hanyoyi kala kala nabi akan kaucewa aurenki amma na kasa, a haka zuhair yace na gudu kawai amma girman alqawari ya sanya nakasa daukar wannan matakin, wlhy manga babu yanda zanyi ne ya sanya na tsaya aka daura aurena dake da mutanen danake iqirarin dangi nane alhali kuma ko sanin su banyiba......bayan an daura aure na qara komawa mahaifina amma fir yaqi yadda dukda ban sanar masa an rigada an daura ba, a haka badan inasan huddy ba ya tilastani aurenta bazan iya yi masa musuba dole na aureta wanda halinta na gari da yawan girmamani ya sanyani na sota, abu dayane matsala da huddy shine rashin san talaka da rashin girmama shi komai yawan shekarunshi,da kaina nayi qoqari na magance wannan matsalar wanda kema shaidace alhamdulillah ta sauya..

Manga bayan da kikaga na tafi ban dawo ba mahaifinane ya tilasta akan lallai indawo kusa da gida sabida shi mahaifinshi be rasu ba da ranshi kinsan me martaba takawa ai, shine yace sena dawo sokoto da zana na baro kaduna sabida ban tashi nan ba bansan komai gameda mulki waye waye, dole akamun na dawo sokoto,manga bansan yanda zanyi dake ba yasa ban sake waiwayarki ba, amma senayi yunqurin ganin kin dawo kusa dani ina kula dake sosai,yanzu kuma banida abar so kamarki kuma zuciyata ta kasa daurewa rashinki da kuma ganinki cikin damuwa danake kullum, ki tallafawa rayuwata ki yafemun abinda na miki, ki agazamun mu nunawa duniya mun aminta da juna mata da mijine mu qaddara ce sanya mukai wa juna nisa, kuma a shirye nake dana nunawa duniya ke matatace kuma ina sanki" kallonshi takeyi ba qaqqautawa tunda ya soma wannan maganar, ita gani take komai tamkar a mafarki, miqewa tayi da zummar barin dakin ya rungumota gaba d'aya yana ban baki,tureshi tai da qarfi tasoma masifa kukan ma ya gagareta

"Bance qarya kake ba, ban kuma ce bakai bane Aliyu Gadanga amma dankaine na gane sai me?? Bakada imani wlhy kuma nayi dana sanin saninka arayuwa, nayi dana sanin san danake maka, nayi dana sanin aurenka arayuwa, nayi danasani zuwana duniya gaba d'aya, abu d'aya zan sanar maka kuma wlhy summa tallahi karka saka a ranka wasa nake, ni Hafsatu Manga na gama aurenka daga yau, wannan fuskar ta zalinci dacin amana daka sako ta karya, zan dauketa ta karya kamar yanda zan mayarda soyayyar ka ta qaryar gaske azuciyata, ni ba wannan Aliyu gadangan na aura ba, Aliyun dana sani shine me fadar Allah yace Annabi yace yake kuma aiki da cewar su, ban auri wannan fuskar takaba, sabida bazan taba zama da kaiba, inaso kayiwa kanka adalci karka daga wannan maganar daganan sabida wlhy bazan saurara maka ba, zanje kaduna dana kallama exams kuma zanje court araba aurena dakai kai tsaye malam,mugu kawai azzalumi macuci" matsawa yayi ya riqe mata hannu, tsabar mamaki ma takasa k'wace hannunta

"Haba Hilwa ki tausayamun mana wlhy zan iya rasa raina idan baki"

"Kai kasan tausayi kuwa Yaa Ali!!! Kasan yanda nasha wuyar rashinka a kusa dani? Kasan azabar dana d'and'an akan rashin ka? Bari kaji wlhy wa ennan hujjojin daka kawomun wai kake iqirarin sune dalilinka na takurani ka cutar dani ka tauyemun haqqina basu gamsar dani ba, sam basukai matsayin dazan karbe su matsayin uzuriba,kaidai kayi amfani da rashin karfin mahaifina ka wulaqantar dani, daka barni da igiyar aure aida sakina kayi ka tafiyanka, kana cewa Aunty huddy batasan talaka aita fika wlhy kaine babban mugun dabesan haqqin dan adam ba, kuma ka rubuta ka ajiye an raba aurena dakai an gama, gwarama kaja bakinka azuwan bakasan komai ba innuna nina gaji inba haka ba tonuwar asirinka ka janyo, karkayi duba da irin qarfin san danakewa gadanga ka dauka wai zan sassauta maka, gadanga naso ba Ali Abbas ba kuma bazan taba san Ali Abbas ba, dama gadangan naso kuma babushi, fuskar gadanga qaryace, zuciyar gadanga qaryane, soyayyar danakewa gadanga ma karya ne, zan maka hauka idan baka buden kofar nan na fita ba wlhy, dole ya bude nata da qafa tabar gidan, shi kuwa kwantawa yayi ya runtse idanshi, be taba zata abubuwan zasu cabe masa haka ba sam!!!!!!

Mom Nu'aiym

[7/6, 3:06 PM] ‪+234 706 571 7620‬: *Haske writer's Asso.(home of expert and perfect writer's)*

*👑ALI ABBAS 👑*

Billy galadanchi

Sadaukarwa gareki qawa ta gari *Fulany saddy*

                                        07

Tafiya kawai takeyi amma batasan inda take sanya qafanta ba, wani irin tashin hankali take ciki mara misaltuwa ta dade sosai tana ganin yanayin gadanga akomai na Ali Abbas hatta tafiyarshi da muryarshi tasha ayyana aranta dama shine takeso ba gadanga ba sekuma ta tuna yafi qarfinta, tasha jin tanasi tayita kallon qwayar idanshi sabida yanda yake mata kama da gadanga amma bata taba kawo wa ranta cewar wai Ali Abbas shine gadanga ba, tayaya ma hakan zata faru a rayuwa? Mesa ya zab'i cutar da ita? Sabida tana talaka? Mara galihu ko sabida ita d'in ba mace bace?  Kai tsaye gidansu wata friend dinta ta wuce dake lowcost wacce dama tana cikin qawayenta na sokoto tana yawan mata qorafi akan bata zuwar mata, koda tashige dakin Bilkisu bata qara fitowa ba, yau dai ta kasa daurewa rayuwarta zama tayi ta gayawa Bilkisu komai daya shafeta tana kuka sosai tamkar ranta ze fita, Bilkisu ma kukan tayi na tausayin qawarta sannan tace

"Nasani abinda ya aikata agareki cutarwa ne ammafa ki sani mijinki mijinki ne, bance ki sake masa fuskaba kokuma kici zarafinsa noo ina daiso ki gasashi cikin ruwan sanyi, ki sani wllh hafsat yanzu maza wuya sukeyi,idan kika kashe aurenki wuya zakisha, karki dubi wai wata huddy to saime dan mijinta ne, kibi komai a hankali sannan karki kuskura ki gayawa wani wannan maganar da kika gayamun, kiyi tamkar baki sani ba shi yaje ya fada da kanshi, ki nuna masa lallai abinda yayi bame yafiya bane, kuma lallai bazaki zauna dashi ba amma karki tsaurara kin ganni nan miji nake nema ido rufe, so ki kula ki kuma kame kanki, karki bari ya fahimci kin razana ki daure kiyi komai yanda kika saba a gaban mutane ma ku gaisa yanda kuka saba kinji?" murmushi tayi taiwa qawarta godiya, tayi zamanta anan suka ci gaba dashan hirarsu.....

Ali Abbas be koma gidan ba se wuraren karfe 7 na dare, yana shiga ya had'u da yalwa, zubewa tayi ta soma wurga masa gaisuwa
Chapter 10 · 0% Book details