Sashe 24
Ali Abbas Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ku tafi kawai zan gana da baqona" kallonta zuhair yayi yanda ta sauya mulki da sarauta sukayi matukar karb'ar yanayinta yace aranshi "Shisa ba'ason wulaqanta mutum, yanzu duk iya wulaqancin da huddy tagama yiwa manga takereta a matsayi gaba da baya ko wane dangi datake dashi jinine na sarauta me qarfin gaske uwa uba ko taqi kota so Manga ce uwar gidan ta.... Kallon ta Ali Abbas ya miqe yanayi ita d'inma shi take kallo ganin kallon kallo din nasu bame qarewa bane ya sanya ta mayarda dubanta zuwaga zuhair sosai ta sake masa fuska,dama ta sanshi kuma yanda ta saba haka ta masa har qasa ta duqa ta gayar dashi mamakin rashin girman kanta yake dukda ta gano asalinta,cikin sakin fuska sosai ya ansata suka gaisa sannan ya basu wuri, miqewa tayi daga tsugunon da tayi dama shi a tsaye yake be zauna ba, matsowa tayi daf dashi sanye da murmushi a fuskar ta tace
"Ina maka barka da zuwa,yaya hanya ya kuma gajiya?" murmushin shima ya sake ya damqo hannayenta duka biyu ya sumbaceta a hannun sannan yace
"Hafsat kin bani wuya,tun yaushe rabon danaji muryanki,mesa kika zab'i azabtar dani ne hafsat?" ya fad'a tare da langwab'ar dakai tamkar qaramin yaro,hakan dayayi seya bata sha'awa har wani qayataccen murmushi ya sub'uce mata tace tana qoqarin zame hannayenta daga nashi
"Bansan da zuwanka sorry na barku kuna jira" kallonta yayi yanda take qoqarin kawar da zancen dayake mata,zama yayi shid'inma kusa da ita yace
"Amma dai kin shirya komama Nigeria ko, sabida gaskia na gaji da rashinki a kusa dani" murmushi tayi
"Nina dawo Niger kenan yaa Ali,dan Allah kama dena zancen komawa na garinku" kallonta yayi batare dayayi magana ba, sabida yanda yaga bilhaq da gasken takeyi, kodai tasan sharad'in da kakanta ya gindaya ne akan aurensu, ba kamar yanda akace bata sani ba
"Kana kallo na yaa Ali, bana so ka b'atawa kanka lokaci sabida zancen gaskia yaa Ali nina rigada nazo gidan gata, bazan koma inda ba'asan daraja taba" juyawa yayi ya fuskanceta ya riqe hannayenta duka biyu
"Baby dan Allah karkice haka, ki yarda da qaddara komai ya wuce wlhy hafsat ina sonki some yawa me kuma tsananin gaske,ki bani dama in saka miki da alkhairin ki fiyeda wanda kikamun, ki bani dama in nuna miki kalar qaunar danake miki,ki bani dama in nuna miki kalar sonki danake,ki bani dama mu rayu dajuna" fincike hannayenta tayi miqe tsaye, qwallan datake tarewa ya silalo mata tace cikin d'aga murya
"Dama!!! Dama kake cewa in baka fa yaa Ali,kasan meye ma'anar dama kuwa? Kasan amfaninta? Kasan muhimmancin dama awurin d'an adam? Kasan gudummawar da dama ke baiwa rayuwar d'an adam? To idan baka sani ba bari kaji in gaya maka... Dama itace wacce takeda sauqin samu awurin d'an adama kuma take cikin abubuwa masu sauqin sub'ucewa d'an adam,yayinda sub'ucewar ke matuqar tarwatsawa d'an adam lissafi sabida sam ba'a samun dama ta biyu idan akayi sakaci da ita.....ka sani yaa Ali ka samu dama fiye da d'aya sab'anin wasu da sam idan ta farkon ta wuce shikenan ta sub'uce musu har abada....karkayi tsammanin bana sanka,sam ko d'aya kaine namiji na farko danaso tun farkon sanina dakai, kuma ka sani bakada na biyu a wurina, na soka fiyeda komai da kowa,na soka da fuskar ka ta qarya sannan na sanka da fuskarka ta gaskiya, na yarda zuciyata da taka ne a had'e amma inaso kayi hakuri ka sani cewar nayi iya qoqarin in manta wulaqancin dakamun amma sam na kasa manta komai, dan Allah ka hakura dani kamar yanda zan hakura dakai, ka manta dani kamar yanda zan mantaka a rayuwa, ka fita arayuwata kamar zan fita a taka daga yanzu har abada....." tana gama fadar haka ta juya da gudu, yayinda tabar shi cikin tsananin tashin hankali da qunan rai me tsananin gaske,ya dasqare a wurin se wasu zafafan hawaye dayake saukewa....
Mom Nu'aiym....
*HASKE WRITER'S ASSO. (Home of expert and perfect writer's)*
*👑ALI ABBAS👑*
*Billy Galadanchi*
*Sadaukarwa gareki qawa tagari Fulany saddy*
18
Da baya da baya ta koma ganin yanda kawu bala ya qura mata ido (yayan innoh) yanayin kallon dayake mata kadai ya sanya ta fahimci cewar yaji komai kuma ta gano ya shaqa sosai ba kadan ba, dama tun zuwansu gidan ta kula yanada zafi sosai da hannu ya mata alama akan ta koma ciki ba musu ta juya qirjinta na tsananin dokawa, a qasa ta zube yayinda Ali Abbas ya qura mata idon shi da suma rine sukayi ja tamkar gaushin wuta, be iya cewa da ita qalaba har kawu bala ya shigo parlor d'in da sallamar shi,miqewa Ali Abbas yayi ya miqa masa hannu sabida sun had'u a fad'a, sosai yake qoqarin saisaita nutsuwarsa karya fahimce matsalar dukda yake ya soma fahimtar wani abin....zama yaga kawun yayi shima ya zauna kawun ya mayarda dubanshi zuwaga Manga yace cikin nutsuwa
"Hafsat ki sani bazan miki fad'a ba, sabida na sani kinsan ciwon kanki, zan dai yi qoqarin tunasar dake abubuwan danake da tabbacin kin sansu mantawa kikayi,da farki dai kinsan kalmar zawarci ko a fad'i ba tada dadi sam bare kuma shiga acikin layin zawarawa masu jiran tsammanin dababu tabbas, ki sani yanzu zawarawa neman miji suke ido rufe, kin girma kin isa kisan me duniya take ciki sabida haka yanzu na miki tuni akan siyawa kai zawarci, abu mafi muni shine tsinuwar Allah dakike janyowa kanki kina hanawa mijinki haqqinsa, kana kina neman saki da kanki, ke a wa da zaki keta haddin Allah? Kinsan abinda kike fad'a kuwa?, ki sani dama kakanki na wurin uba ya rantse seya raba aurenki da mijinki koda kotu ne se sunje sekije ki biye masa ku shiga hurumin Allah,dandai iyakar sanina aure raine dashi kuma se ranar ajalinsa ze qare lallai ki nutsu ki rungumi mijinki sau da qafa kuma ki tabbatar kin bashi kulawa ta musamman, me martaba be turoki wannan sashen danki ci zarafin sa ki wuce ba anan zaki zauna ki kwana atare da mijinki harse ranar daya shirya barin garin nan, dama aikoni kurun akayi na kai abokinsa masaukinsa na daya baren ke kuma ku zauna anan gidan" sadda kanta kurun tayi qasa batai magana se hawaye, yaya zatayi ta aiwatar da shirinta bayan idan ta kalli qwayar idanshi yana saukar mata kasala da wani qaunarshi, duk sanda ya matso daf da ita hakan yakan saukar mata da wani shauqi na musamman gaurayuwar numfashinsu na saukar mata da tsananin nutsuwa da farin ciki,duk yayinda ya had'a hannayenta da nashi ji take tamkar bazata iya haqura dashiba harse ta manna jikinta da nashi.....taso yasan muhimmancin ta a rayuwarsa amma bazata taba iya aiwatar da hakan ba sabida ganinsa kurun yana hanata aiwatar da dukkanin ayyukanta,kallonshi tayi bayan kawun yabar wurin shida zuhair sunbar part d'in gaba d'aya tace
"Zanje na shiryo kayana ka bani awa d'aya" kasa cewa da ita komai yayi sabida har lokacin zuciyarsa tuquqi take masa, gabaki d'aya gani yake ko cewar datai tana sanshi qarya ne bata sanshi, besan ya zeyi ta soshi ba, lokaci d'aya yaji kanshi yana mugun sara masa, abubuwa sun masa yawa ya sani idan beyi da gaske ba Hawan jinin sa tashi yakeso yae gashi sam ya kasa cire abin a ranshi yanda ta dage take zayyano masa zata iya rabuwa dashi qiri qiri....yana zaune hartaje ta dawo bayi d'auke da akwatin kayanta da sauran su,kai tsaye ciki suka wuce da kayan yayinda ta wuce shi agun batare data koda kalleshiba,wanka tayi ta sanya rigar bacci wata shara shara ruwan sararin samniya iya cinyarta, ba komai ajikinta ajikinta se rigar ta sakko da yalwataccen gashin kanta yana yawo, tunda tayi rashin lafiya take yawan shan tea da dare, wannan ya sanya ta fito ta wuce ktchn har lokacin yana zaune a wurin dafe dakai, ta kula bangaren irin na dukkanin sauran bangarorin gidan ne sabida wannan ne karonta na farko na zuwa bangaren na baqi, bayi ta gayawa su hada mata tea, kuma dai ta tsaya da kanta ta hada sannan suka dakko mata zuwa parlor, kusa dashi ta zauna yayinda baiwar ta dire tray d'in a sama centre table dake parlor din, kallon baiwar tayi tamana nuni data bar wurin,kai tsaye kuwa tabar wurin ita kuwa ta mayarda dubanta zuwaga Ali Abbas da har kawun ya fita banda gaisuwa babu abinda ya shiga tsakaninsu bece kanzil ba ko sallama bewa zuhair
"Yaa Ali kasha tea kafin ya huce" hannun shi ya sauke daga riqon dayawa kanshi ya sauke rinannun idanuwan shi akanta,sosai ta tsorata da yanayinshi matsawa tayi daf dashi ta riqo hannunshi zafin dataji a hannun nashi ne ya qara rud'ar da ita tace murya na rawa
"Yaa gadanga dama zazzab'i kake shine baka fad'a ba?" nanma dai bece mata komai ba,gani yake tamka idan yae magana zuciyarshi fashewa zatayi sam baya ganin komai,ganin haka ya sanya jikinta yae matuqar sanyi ta sani an sanar mata yanada ciwon hawan jini, kaddai kala mantane suka haddasa masa wannan zazzafan zazzab'in? Lumshe idanta tayi tana tunanin wawtar data aikata masa a hankali ta bud'esu ta dire masa su ta kula sam baya tare da ita, tea d'inma gabaki d'ayanshi ya fice mata akai,sosai ta matse a jikinsa zuwa yanzu ta kasa riqe kukan daya zo mata tayi wani dana sani mara misaltuwa,tana kukanne yayinda kanta yake kwance saman faffad'an qirjinta abinda ya qara bata tsoro tafi 20mnts tana kukan amma be motsa ba kuma beyi yunqurin koda rarrashin taba, ganin hakan bame qarar ta da komai bane ya sanya ta tashi ta wuce cikin d'akin tarasa ma me zatacewa matsalolinta da Ali Abbas, anya ba wani laifin tawa mahalicci yake jarabtar taba kuwa? Istigfari ta dingayi har bacci ya sure ta asaman gadon.
Ali Abbas seda ya samu nutsuwarshi sannan ya tashi ya shiga d'akin watsa ruwa yayi ya sauya kayan jikinsa sannan ya hau gadon ya kwanta gyara mata kwanciyarta yayi yayinda kansa ke masifar sara masa a haka shima bacci me nauyi ya sure shi.