← Book details Abban Sojoji Local reading mode
READING PART 91 OF 92

Sashe 91

Abban Sojoji · about 7 min read

  Junaid na lura da halin da Sehrish ta shiga,
   lokacin da tazo ƙarshen sakon, zumbur ta miƙe tsaye cikin tashin hankali murya na rawa take faɗin"Innalallahi wa'innna ilaihirraji'un junaid tun yaushe saƙon nan yake ...? ta tambya a rikice,
   Miƙewa shima junaid yayi yana cewa "Am sorry sehrish wlh naso na taimaka musu tun lokacin ki duba message ɗin dake a ƙasan nasu ki gani na tura masu  sako nace su turomin acct number nasu amma shiru i ave been trying their phone number but always switched off har na haƙura. '
   Cikin shesshekar kuka Sehrish tace "Allah sarki hosana, nashiga ukuna bansan ya suka ƙare ba, hosana tana raye kota mutu nasan ba mai taimakon su....." Kuka ne yaci ƙarfinta sosai,
  Cikin sanyin Murya junaid yashiga lallashin ta,
   Cikin kuka tace "junaid bazaka gane bane...nasan suna cikin mawuyacin hali babu mai taimakonsu ina so naje wurinsu nagansu....' tayi maganar a kasalance,
  "Sehrsih in dai anan garin suke ni zan kaiki a mota ta ki gansu,'
   Girgixa mishi kai tayi tare da cewa "Ba'anan suke ba junaid" duk tabi ta susuce,..
   Ajiyar zuciya junaid yasaki tare da cewa "kada Ki damu sehrish nayi maki alƙawarin cewa da kaina zan kai ki, ki gansu koma ina suke, amma sai Babban yayan mu ya koma U.s saboda in yana nan bazan samu hanyar da zan fita ba,'
  tsagaitawa tayi da kukan ta kalle shi tare da cewa "kayi Alƙawarin xaka kaini "
  "Eh insha Allah, amma ynx ki goge hawayen naki, ashe kin iya kuka har haka just like a new born baby,' yayi maganar da zolaya yana Imitating ɗinta,
   Ita kanta batasan sadda ta fashe da dariya ba, saboda yadda junaid yake kwaikwayon kukanta sai ya koma mata tamkar babyn,
   Hannu tasa ta share hawayenta, sannan yace "Kin natsu yanzu"?
  "Eh" ta bashi amsa,
Komawa su kayi tare da zama, sannan junaid yashiga nuna mata yadda zatayi amfani da wayar, Sam hankalinta baya akan jawabin Junaid ta tafi can duniyar tunanin halin dasu hosana ke ciki, Apps ya tura mata kala kala a wayr masu amfani daga wayarsa, dayake akwai sim aciki mtn nan take ya buÉ—e mata whatsapp, Duka ya zuba mata numbers É—in yan gidansu aciki, sannan yasanya ta a grps É—inshi na friends,.
  Daga bisani ya bata wayar suka yi sallama ta koma bedroom ɗinta, ganin time ɗin Sallah yayi yasanya ta ajiye wayar saman side drawer ta wuce toilet tayo alwala tayi sallar la'asar,

______________________________________

Bayan Aunty Babba ta kammala waya da Amani Fitowa tayi ta sauko down anan tasamu hafsat ta buÉ—e akwatinan kayan da suka siyo tana duddubawa, Kayane masu kyan gaske, Cord laces, Materials atampha, dogayen riguna kala-kala, Sleeping dress, Inners ba abunda basu siyo ba,hada Shoes & bags na gayu, ga Ribboms , turarurruka , jewellery everthing fa sun sayo,
   "Gasky mommy na cha6a fa, kayan nan sunyi kyau saura a ware wanda za'a kai ɗinki,.  Hafsat ce tayi maganar tana kallon Aunty babba wadda ke tunkaro ta,.
   Gefenta ta zauna saman 3 seater ɗin da take, sannan tace "Zamuyi magana akan wannan zuwa gobe, ynz nagama magana da Amani a waya,'
  ta6e baki Hafsat tayi tare da cewa "kin faɗa mata game da twins ɗin can?
  "Eh na faɗa mata har ta bani wata shawara,'
  "Me tace ita"? Hafsat ta tambaya yayin da take ajiye Veils ɗin dake hannunta cikin akwatin kayan data buɗe
Nan Aunty babba ta kwashe komai da suka tattauna ta sanar mata,
  wani irin kallo hafsat tayi ma mommyn nata kafin tace "ke kuma sai kika ɗauki shawararta ko?
Aunty babba tace "eh naɗauka saboda gsky ta faɗa Omar zai iyayin zuwan bazata kuma duk sanda yazo zai fahimci halin da suke ciki zai tuhume ni akan hakan, don haka zan basu kulawa ta wani lokaci kafin nasa a Zubar dasu,'.    Rai a6ace hafsat tace "Yanzu mommy har shawarar Aunty Amani zata fi tawa mahimmancin a wurinki !?
   murmushi aunty babba tasaki tare da cewa "Ko kusa, kawai akwai abunda na hango ne shiyasanya,"
  Jinjina kai hafsat tayi tare da cewa "Shikenan Mommy, amma koda za'a rinƙa basu abinci dole suyi mana bauta acikin gidan nan !!".  
   "Wannan ae dolene, zasu aikatu kamar jakuna duk wani aiki na gidan nan kansu zai koma," aunty Babba ta bata amsa,
  Murmushi hafsat tasaki tare da cewa "daga yanzu na daina wanki da washing maching, Tun da Allah ya kawo mana sauki lallai ne zasu aikatu,
  "Kwarai kuwa, yanzu dae ki tattara akwatinan nan ki kaisu bedroom ɗinki, Ni bari naje wurinsu naga ya suka kwana, Allah yasa suna raye dae"
  ta faɗi tana dariya itama Hafsat ɗin dariyar take yi,

______________________________
Abban sojoji sashe na biyu wasu haryanzu basu fara payment ba, Free pages ne nake sanyawa yanzu don haka ku hanzarta biya tunkan su Ƙare saura pages kaɗan ma, idan kuka ce zaku naɗe hannu nima zan dakata ne🙅, inyi takaina dama ya lafiyar giwa, abun ya bani mamaki many of u sunyi shiru akan hakan, zamu ba juna mamaki ne insha Allah 😂 Boss Lady ce fa,

Abban Sojoji akwai Nrml grp 300
Special grp 500
Vip (700) iya kuɗinka iya shagalin ka, ni nawa tsarin daban ne nasan yadda zanyi da kowa,🙌 Wanda suka shirya 08103884440, su tuntu6e ni,

*sai naji sauƙi insha Allah zan ci gaba*🙏 Just keep praying for me don bani lfy😥, sannan waɗanda suka ga Pictures ɗina pls don't share it, ban bada Iznin ayimun share ba, sbd bansan bakin wasu ba,bansan me zasu ce ba,🙏😿*💋💋💋ABBAN SOJOJI💋💋💋*

_🔥the Father Of Soldiers🔥_

ﻗﺼﺔ ﺣﺐ ﺭﻭﻣﺎﻧﺴﻴﺔ ﺑﻴﻦ_ ﺳﺤﺮﻳﺶ ﻭ ﺍﻟﺠﺮﺍﺡ ﺍﻟﻌﺎﻡ
ﺭﺍﻓﻴﺖ💞😍

ﺣﻔﺼﺔ ﺑﺎﺗﻮﺭ✨
*Mallakin*

*✨HAFSAT BATURE MOH'D✨*

~BossLady~💋

*Final Page In Part 1*

*page 100*âš¡

  "Kwarai kuwa, yanzu dae ki tattara akwatinan nan ki kai su bedroom ɗinki, Ni bari naje wurinsu naga ya suka kwana, Allah yasa suna raye dae"
  ta faɗi tana dariya itama Hafsat ɗin dariyar take yi,

tayi mamakin ganin ƙopan store ɗin abuɗe turowa tayi ta shiga samun su tayi a tsaitsaye sai faman zagaye zagaye suke yi sun jigata sosai,.

Suna ganinta gabansu ya faÉ—i rass saboda tsoran matar suke ji sam sun gaza magana sai zare ido kawai,

murmushi Aunty Babba tasaki tare da cewa "Ashe kuna raye, gsky kuna da taurin rai,'
Jahad ce tayi ƙoƙarin gaishe ta bata amsa ba sai cewa tayi "ku biyo ni"
Sannan ta juya ta fice suka bi bayanta aransu suna Allah Allah gudun karta yi masu wani abun,

A wani bedroom ta tsaya ta turo door É—in sannan tashiga, suma suka bi ta ciki, É—umemiyar katifa ce a É—akin sai wardrobe ta bango, da Æ´ar drawer,

"Kada kuyi tunanin a É—akin nan zan barku, tsohon store É—in can shine wurin baccinku in dare yayi, na kawo ku nan ne domin kuyi wanka ku samu kuyi sallah, sannan zan baku abinci duk rana plate É—aya, amma ku sani zaku Aikatu sosai, don Gwamnati bata aikin banza,'

aunty babba ce ke kora masu bayanin nan ba mutunci a fuskarta, a daga tsayen da suke,
Kallon juna su kayi jiki asanyaye koba komai sun samu sauƙi atlease,
Jin sunyi shiru yasa ta daka masu tsawa da cewa "Baku ji ina magana bane, kun wani tsayamin kamar ƙerarrun gumaka,'.
  Murya na rawa suka haɗa baki wurin cewa "Zamuyi komai kke so insha Allah,"
  ta6e baki tayi tana kallonsu tace "kada kuyi tunanin sauƙi kuka samu a wurina, sam ba haka bane don yanzu uƙubar tafara,"
  Jahad tace "Laifin me muka yi maki ?.
  dariya aunty Babba tayi tare da kallonta ita da tayi magana tace "bakuyi mun laifin komai ba, kawai kun shiga tsakani na da abun Hari na ne shiyasanya,' tana faɗin hakan ta fuce daga ɗakin,
  Shiru su kayi suna kallon juna bakomai ya tayar masu da hankali ba face abunda Aunty babba tace wato kada suyi tunanin sun samu sauƙi yanzu uƙubar tafara, me hakan ke nufi !?!?
   ajiyar zuciya Suka saki atare wuce wa Jahad tayi toilet domin ita damuwarta Sallah, Hosana kuwa saman katifar tahau ta zauna idonta cike tab da kwalla luhu luhu Yunwa take ji Over,

Wuce wa kitchen Aunty babba tayi lokacin har hafsat ta koma bedroom É—inta ta kwashe kaf kayan da aka suyo masu hosana da Jahad ta shige dasu (uwar Son banza)

Sai faman yamutsa fuska take kamar uban wani ya matsa mata ta haÉ—a musu abinci,..
Duddubawa tayi Cikin kitchen É—in tana jin bazata Iya girkawa yaran Abinci da hannunta ba, Akwai sauran breakfast É—insu na safe da suka rage duk yayi sanyi abincin,

Tsayawa tayi tana tunani aranta kawai ta daure Just for today ta dafa musu ko Indomie ce,
  Nan da nan ta kunna gas ta aza pot ta zuba ruwa ciki, shaf shaf ta haɗa kayan haɗi aciki ta zuba musu Indomie ɗin aciki,
  Bayan ta kammala dafuwa, ta ɗauko plate mai ɗan faɗi ta baza musu Ita aciki da zafi zafinta sai ƙamshi take yi,
Chapter 91 · 0% Book details