Sashe 75
Abban Sojoji · about 8 min read
A 6angaren su Hosana kuwa Tun da asuba da saude ta tashe su su kayi salla, suka koma tare da shimfiɗa wani sabon baccin kamar matattu haka suka dingi sharar bacci, dole kuyi bacci Allah, zaman cell ba daɗi anjima ana cikin tashin hankali, ga sauƙi yazo daga Lillahi, Koma wa kitchen saude tayi ta shiga harhaɗa kayan breakfast da zatayi amfani dashi, shaf shaf ta fere dankali turawa bayan ta kammala ta yanka shi slide sannan ta shiga soya shi a saman frying fan, Muryar goggo ce ta katse ta da cewa "umm agogo sarkin aiki nace ya akai banga yaran nan ba? Kodai mafarki nayi jiya? Fuska ɗauke da dariya saude tace "Su wa kike nufi kenan"? Watsa hannu tayi tare da cewa "Ƴa'ƴan Abusufyan mana? waɗannan tagwayen ? ta tambaya tana neman jin ƙarin bayani, Bin ta da kallo saude tayi jikinta na sanye da kayan baccin nan ƴan gado, sun yamutse sun tsufa riga da wando kwalar rigar ta sukurkuce, gasu Over size sun mata yawa kamar agwagwa haka ta koma acikinsu, taƙi ta janza wasu koda yaushe akayi mata magana akan ta sauya wasu kayan baccin sai tace tafi son waɗannan saboda ƴan ƙasar turƙiya ne irin wanda Zehra ke sanya abarmata abunta, wato ta cikin tarkon kauna, Abusufyan ne yayi mata tsarabar su tun last year dayazo nageria, Gashi ta ƙife ɗan kwalin atamfa akanta abundae ba'ace wa komai, "Saude kinyi shiru baki ce mun komai," daker saude ta iya cewa "Suna nan mana, ba mafarki kikayi ba goggo, suna can suna sharar bacci ɗakina, Washe baki goggon katsina tayi tare da cewa "Yawwa madalla har hankali na ya kwanta," ta faɗi tana shafa saitin zuciyarta, hakan ba ƙaramin sa saude dariya yyi ba, goggo taci gaba da cewa "Saude so nake ki shirya musu karin kumallonsu mai daɗin gaske, a shaƙe musu tray, sannan a hada musu farfesun kaji dan Allah naga ƙasusuwan wuyansu kamar an jera ƙarafuna suna fama da yunwa, so nake kafin Abusufyan yadawo daga ƙasar turƙiya ko ina na jikinsu ya cicciko suyi kyau ƴan dumur-mur,' tayi maganar tana kwatanta yadda take so su koma da hannunta, Dariya kawai saude ke saki jin abunda goggon tace wato ƙashin wuyansu kamar an jera ƙarafuna, har dafe ciki take yi, "Bansan iya shege wa kike wa dariya? Saude kin raina ni ko ina magana kina mun dariya, idan kika fusata ni, yau yau ɗinnan zakiyi fiffige ki koma rugarku acigaba da kiwon shanu," Tsuke fuska saude tayi jin abunda goggo tace rai abace tace"shikenan tun da haka kke so bari naje na shirya kayana yau dai na tafi na huta da gori," tayi maganar tare da kama hanya zata bar kitchen ɗin, . Da sauri goggo ta ruƙo hannunta fuska dauke da murmushi cikin lallami tace "haba ƴar saude ta ke ko bakisan wasa ba, in kika tafi wa zai haɗawa ƴa'ƴan abusufyan ɗina breakfast ɗinsu," Murmushi saude tasaki ganin yadda goggo ke lallashinta yau, ita tasan saboda twins ɗincan tasamu wannan kulawar, Koma cikin kitchen ɗin tayi tana cewa " shikenan na fasa, amma goggo gsky ki barni nayi aikina mana, kinzo sai katse ni kike yi," Juyawa goggo tayi ta fi ce tana cewa "To natafi Allah baki haƙuri, ayi aiki lafiya, Sai da goggon katsina ta wuce ɗakin saude ta tura kopan ɗakin ta hangi su Hosana da Jahad suna bacci sannan hankalinta ya kwanta hada jinjina kai da cewa "Masha Allah, ƴa'ƴan abusufyan ɗina kusha baccin ku ku more ƴan gatana abinci na nan yana jiran ku," ta kammala sambatun nata sannan ta koma falo ta kunna kallo ta samu wuri ta zauna saman 3 seater tana cewa "Oh ko yaushe suke maimaicin shirin Omaru da zahra, aiko bari waɗancan yaran su tashi daga bacci in nuna musu ƙasar da mahaifinsu ke zaune, ni nasan ma ba'a rasa ganin shi acikin film ɗin wata'kil ko yazo giftawa aciki Camera man ya hasko dashi," Haka ta runka sambatu ita kadae abunta, sam bakinta bai zama hakannan batare da tace wani abu, Bayan saude ta kammala breakfast ɗin, acikin katon tray ta jera warmers ɗin da sauran food stuffs ɗin ta shigo falon dasu, Tunkan ta karaso goggo tace "Yawwa saude na maza ajiye shi anan gabana, sannan kije ki tasomun ƴa'ƴan Abusufyan ɗina, bayin Allah suna can suna fama da yunwa, bacci bai da imani baisan in kana jin yunwa ba ya ƙyale ka ba," Fashewa da dariya saude tayi aranta tana cewa wato da ace goggo ƴar comedy ce ba ƙaramin nishaɗantarwa zatayi ba, Ajiye tray ɗin tayi asaman carpet ɗin geben ƙafar goggon kamar yadda tae commanding ɗinta, sannan ta wuce room.ɗin ta don ta tayar dasu Hosana da Jahad, Duk wannan abun dake faruwa Goggo da saude basusan cewa Omar da Babban likita suna cikin gidan ba, saboda dama jiya bayan sunyi bacci suka dawo, Su hosana ne kawai suka sani saboda sunyi magana dashi, duk in taga yaran wani farin ciki take ji aranta, sai faman sharar baccinsu suke, addu'arta Allah yasa Yaya Omar yabar musu twins ɗin su zauna agidan koba komai zata samu abokan fira, Ƙarasawa tayi gaban gadon ta sanya hannunta ta ɗan bubbugi ƙafafunsu a hankali kamar wadda zata tasar da Jarirai, Farkawa su kayi kowa na faman yin hamma, atare suka tashi zaune suna kallonta, lokacin da jahad ta shaida ta cikin sauri tace "ina kwana Aunty," murmushi saude tasaki tare da cewa "Lpy lou my sisters fatan kun tashi cikin ƙoshin lpy," Jahad tace "Alhamdulillah aunty, munji daɗi sosai da kulawarnan, "Aunty nidai Yunwa nake ji, da yunwa natashi kamar na cinye ƴan hanjin ciki na," hosana ce tayi maganar, fashewa da dariya saude tayi hada jahad ɗin, murya a ƙule Jahad tace "waike baki da kawaici ne? Ko gaishe ta bakiyi ba sai magana akan yunwa yunwa," Murmushi saude tayi tare da cewa"kwantar da hankalin ki, special breakfast na nan nayi maku reserving ɗinshi a palor, kuma goggonku na nan tana jiran ku, sai tambaya take ina ƴa'ƴan abusufyan ɗinta," Jin hakan yasa su yin murmushi tare da kallon juna, kafin jahad tace"Aunty saude dama ina so na faɗamiki jiya yaya Omar yazo munyi magana dashi har yace mana, mu shirya yau zai wuce damu kaduna gidan yayan shi, gsky mun fi so muzauna anan," ta ƙarasa magar tana kallon sauden, dafe ƙirji saude tayi tare da cewa "Wai dagaske abunda ya faɗamaku kenan ! Hakan na nufin bazai bar mana ku nan ba, mu zauna atare ya Allah,' sam bataji daɗin hakan ba, har cikin ranta, babban tashin hankalin ma da taji Jahad tace zai kaisu kd gidan Yaya ishaq, Aranta tace "tabɗijan gidan wannan shu'wa arab ɗin jarababbiya, sam bana fata akai yaran nan can saboda bazata ƙyalesu ba, sai ta azabtar dasu waiyo Allah na, ya zanyi yaya omar yabar mana su anan su zauna, wlh aunty babba bata da mutunci ga Hafsat kuma yadda yarinyar nan ta tsani talaka aikom yaya omar zaiyi gangancin jefa rayuwarku cikin hadari,' "Aunty baki ce komai ba? dan Allah kice masa yabarmu anan muzauna daku munfi jin daɗi," jahad ce ta katse mata tunanin da take yi, Jiki a mace saude tace "i dont know wat to do, yaya omar in yayi niyar yin abu no body can stops him, kuyi addu'a kawai Allah yasa goggo ta hana shi tafiya daku, amma muddin aka kaiku gidan yaya Ishaq kun shiga uku," Hankalinsu ba ƙaramin tashi yayi ba jin abunda saude tace, murya na rawa jahad tace "aunty meyasa kika ce haka"? Saude tace "hmmm abar zancen kawai, ku tashi ynx ga breakfast can na jiranku, ga goggo kuma nasan ganinku, ni ynx kitchen zan koma na shiryawa su yaya Omar nasu, pls kusan yadda zakuyi kar yaya Omar yabar gidan nan daku," tana gama faɗan hakan ta fice izuwa kitchen zuciyarta nayi mata ba daɗi saboda tausayin yaran duk da batasa su wanene su ba amma tasan basu da gata, yaya Omar kuma dama shi mutun ne mai son taimakai wata'kil wani wuri yagansu a wahalce yake son taimakon rayuwarsu, da wannan tunanin Saude ta shige kitchen, Kallon juna su kayi cikin tsananin tsoran inda za'a kaisu, atare suka tashi haryanzu doguwar rigar material ɗinnan ce ajikinsu, mayafi kawai suka ɗaura akansu sannan suka fito, Goggo naganinsu ta soma washe baki tana cewa "masha Allah ƴa'ƴan abusufyan ɗina maza ku matso ku kwashi albarka wurin gaggonku, ga kuma abincinku na jiranku," Da fara'a suka karasa atare suka zauna suna gaishe ta "barka da safiya goggonmu fatan kun tashi lafiya," "Lafiya lou Alhamdulillah, har mafarkin ku saida nayi jira, tsorona kar na farka na taras da bakwanan agidan bansan ya zanyi ba, in banga ƴa'ƴan abusufyan ɗina ba," fuskarsu cike da tsantsar farin ciki ga kaunar goggon katsina data shiga ransu daga jiya izuwa yau," "Yawwa maza ga shinan kuci ku ƙoshi, in ma bai isa ba aƙaro maku," Cike da zumuɗi hosana ta ɗauki plate ta bude warmer ɗin dake ɗauke da soyayyan dankalin turawa ta shake plate ɗin dashi, sannan ta bude ƙaramar kular jar miya ta lafta asama, ta motse ta shiga da turama cikinta, Jahad kuwa Wainar kwai ta rinƙa haɗawa da slide bread tana cunkusawa abakinta, hannu goggo tasanya ta ɗauki flask ɗin dake ɗauke da ruwan liptop, ta tsaiyaya musu a cup kowa da nasa sannan tace "ga madara nan leda kowa ya zuba yadda zata ishe shi," Zame hannu hosana tayi daga irishi ɗin da take ji don haɗama, ta ɗauki milk ɗin ta zazzafa acikin ruwn tea ɗin mai uban yawa, tana jin jahad na cewa "banza kaɗan zaki zuba," Harara ta watsa mata tare da cewa "ina ruwanki ! ki ci abunda ke gabanki," sai da taga ruwan tea ɗin yayi kauri yaji uwar madara sannan ta tsagaita ta sanya sugar," ta hada tana sipping ɗinshi, girgiza kai kawai jahad tayi tare da haɗa nata tea ɗin tashiga kurbarshi tana ci da bread ɗin," Kamar kura haka ta lamushe abunda ta zuma sannan ta bude warmer ɗin dake dauke da chicken pper soup, ganin lafiyayyiyar kaza yasa hosana gyara zama, anjima ba'a haɗuwa hannunta har kerma yake yi wurin daukar cinyar kazar tana turawa abakinta, gwanin daɗi kunnanta har