← Book details Abban Sojoji Local reading mode
READING PART 76 OF 92

Sashe 76

Abban Sojoji · about 4 min read

rawa sukeyi, Goggo sai murmushi takeyi tana kallonsu tsananin ƙaunar yaran take ji har cikin ranta, Jahad kam kunyar abunda hosana keyi take ji kamar ta shaƙo ta take ji, sai faman licking hands ɗinta take kamar mayya, Ƙasa ƙasa da murya tayi cike da jan faɗa tace "su hosana basaban ba, gida babu makwabta babu gidan miji ba tabbas, banza tasamu sai wankarta ake ba baka sai kunne," Fashewa da dariya su kayi gaba ɗayansu, ashe goggo na jinsu sai cewa tayi "Inji wa ya faɗi maki cewa gida babu, tab Ke ko kinsan katafaren gidan da abusufyan yake rayuwa acikinsa acan ƙasar Turƙiya? Kinsan irin daukar dayake ciki ? ae wannan bakomai bane, hmmm lokacin da naje turƙiya nakai masa ziyara, in zan ci abinci saiya sa an jera mun kayan maƙwalashe cike da dining tabur ae masu aiki gare shi sun iya girki sosai in sukayi abinci kamar abincin Aljanna don daɗi," ta ƙare maganar tana jaddada musu mgnrta Tsagaitawa da cin abincin su kayi suna sauraronta baki asake, sukam wai wanene wannan abusufyan ɗin da Goggon katsina ke ta faman labarta musu zancen shi? Kallon juna su kayi alamar neman karin bayani, goggo tace "ae ku kwantar da hankalinku, ni da kaina zansa abusufyan yazo nigeria ƙafarsa ƙafarku baxan ƙara bari ya tafi yabar yaransa cikin wahala ba," Sunnar dakansu su kayi ga dariya na cinsu, jin yadda goggo ke ƙaƙaba musu mutumin da basu san da Existing ɗinsa ba a duniya, Atare Omar ya fito shi da babban likita sun shirya tsaf, Goggon na ganinsu tace "Kai dirar yaushe ? ta ina kuka shigo cikin gidan," Murmushi Omar yasaki tare da cewa "goggona ke nan, ae jiya muka dawo tare da mutumina, mun same ku kuna bacci," Babban likita yace "Barkanka da safiya Mommyna fatan kun tashi lpy' yayi maganar ayayin da yake zama saman 2 seater, shi kuma marshal Omar ya samu wuri gefen gaggo yazauna saboda ya samu damar gaisawa dasu Hosana dakyau, Atare suka haɗa baki wurin cewa "Barka da safiya yaya Omar dafatan ka tashi lpy," . "Lafiya Alhamdulillah," ya amsa musu yana mai ƙara azan idonshi akansu," ba ƙaramin daɗi yaji ba ganinsu suna cin abinci," Duk kunya ta kama jahad har takasa idasa cin abincin, ita kuwa hosana bakin nan nata dama dama da jar miya, kuma a haka take kallonsa tana sakar mashi murmushi, Bayan sun gaggaisa da goggo tace "daɗa sai naga ƴa'ƴan abusufyan jiya, ance wai kai ka kawo su naita mamaki nace yanzu har yaran nan sunyi girma haka amma ba'a ta6a nuna musu gidan goggonsu ba sunzo sun gaishe ni,'? Tayi tambayar rai a ɗan 6ace tana kallon Omar, Jim omar yayi yana kallonta cikin mamaki yace "Suwa kenan"? Goggo ta nuna su hosana tare da cewa "gasu nan mana," ɗan murmushi yayi tare da kallon babban likita wanda shima murmushin ne a fuskarshi, sarai sunsan rigimarta, in ba haka ba yaushe Uncle Abusufyan ya ta6a aure balle har aje ga maganar aure, Babban likita yace "Mommyna ayi mana afwan laifin mu ne, da bamu kawo su ba, kuma hada ƙarin makaranta sukeyi ne boarding school shiyasanya," ta6e baki goggo tayi tare da cewa "amma dae nikam ba'a kyautamun ba Allah, yara har sun isa aure amma ban ta6a sasu a idona ba! koda yake ba laifinku bane laifin Sufyanu ɗinne zan hadu dashi sai yayimun bayanin yadda ya hana ni jinina, babban likita yace "Mommyna kenan, ina fata kina shan maganinki da na baki akai akai? Yayi maganar yana kallonta, Yamutsa fuska tayi tare da cewa "kai ni na manta da wasu magunguna, suna nan cikin kwandon shara nake zuba su, ai naji sauƙi ynx," dariya su kayi gaba ɗayansu hada su hosana, Omar yace "goggo ina fa sauƙi a nan? U need a medicine 4 ur health," "Ae narasa meke damun mommyna, magani mai tsada kike zubawa cikin dustbin, gsky bana jin daɗi," Tsuke fuska goggo tayi tare da cewa "nifa bansan Iya shege, lafiyata ce ko lafiyarku ? ta tambaya tana harararsu
Chapter 76 · 0% Book details