← Book details Abban Sojoji Local reading mode
READING PART 74 OF 92

Sashe 74

Abban Sojoji · about 7 min read

â—» gaba É—aya ta tafi duniyar tunani har batasan cewa masu gidan duk sun fito ba, domin yin breakfast, yawancinsu duk jallabiya ce ajikinsu,
â—» Fawan da twins ne suka fara hallara suka zauna a kusa da juna, sai Irfan da jabeer bayansu sai khaleed da kanal yusif, duk suka gaishe da Azmee ta amsa musu kafin ta ci gaba da saving É—insu,
â—» Har time É—in sehrish bata cikin hayyacinta tana tsaye kamar gunki tana tunane tunane iri iri aranta, sam azmee bata lura da halin da take ciki ba,
◻ A tare Abbansu ya fito da baby junaid hannunsu cikin na juna, fuskar nan tasa a washe tun da idonsa su kayi Arba da sehrish ɗinsa, tunkan ya ƙaraso ya lura da cewa ta tafi duniyar tunani,
â—» Ganin Abbansu yasa suka haÉ—a baki wurin gaishe shi "Barka da safiya Abba, kun tashi lafiya,"
â—» "Alhamdulillah My Sons ina fata kuma kuna lafiya,"
â—» da fara' a fuskan kowannansu suka amsa mishi,
â—» Bayan sun zauna cike da tsokana junaid yace
â—» "Ni bazaku gaishe ni ba"? ya faÉ—i yana kallonsu,
â—» Tsoki fawan yaja tare da cewa "kabari sai ka fara ajiye gemu da Æ´a'Æ´a tukunna,
â—» "Wai junaid da gemu ba rana ba wata, don gsky ban ga alamar junaid zai yi gemu ba ko nan gaba,'
â—» Acewar Jahan,
â—» Abbansu yace "Talle zatai wa audu gori, ka fara duba fuskarka tukunna, muddin junaid bazaiyi gashin baki ba ko na gemu to kaima haka baza ta6a yi ba,"
â—» dariya su kayi gaba É—ayansu kanal yousuf yace "Wai ina Haroon ne ? Shi bazai fito bane?
â—» Abba yace "taya zai fito bayan abunda ku kayi masa jiya, sam banji daÉ—i ba, tun da ya dawo ya kamata ku tarbi É—an uwanku hannu bibbiyu, in baku ja shi ajiki ba taya zai shiryu ? Yayi maganar cike da nuna 6acin rai akan abunda su kayi jiya,
â—» "Abba amma ba ka ga irin yadda yake mana magana ba har agabanka batare da jin komai ba? Acewar Irfan,
â—» Ajiye cokalin dake hannunsa yayi tare da cewa " in da sabo ae ya isa ace kun saba da halinsa, addu'a kawai zaku bishi da ita Allah ya shirye shi," yana kai karshen maganar ya É—auki spoon É—in yaci gaba da cin abincin dake gabansa,
â—» Jinjina kai su kayi kawai shikam fawan ta6e baki yayi tare da cewa "Ashe dagaske yazo, ae ni nayi tunanin duk mafarki ne zuwan nasa jiya,"
â—» Harararsa khaleed yayi "dole kace haka dama bakwa good time dashi ae,"
â—» tun da suka ambaci sunan HAROON hankalin sehrish ya dawo jikinta, sai faman sauke ajiyar zuciya take yi ga zufa na wanko mata,
aza idonta tayi akan junaid wanda ke ta faman satar kallonta yana mata murmushi
â—» Murmushi itama tasakar mishi,
◻ So yake yayi mata magana amma ba hali sai dae daga inda yake ya rinƙa yi mata alama da bakinsa batare da sauti ya fita ba yace "Sehrish kin tashi lafiya,"
â—» tagane me yake cewa don haka itama tayi kamar yadda yayi tace "lafiya lou junaid ina fata kaima haka,"
◻ ɗaga mata kai yayi alamar eh, duk abunda junaid keyi akan idon Abbansu mamaki yake menene tsakanin junaid da mai aikin nan tukur, kodae sun ƙulla abota ne, ɗan murmushi ya saki domin yaji daɗin hakan, sbd duk wani abu da zai sanya shalelensa farin ciki son shi yake,
â—» "Ga babban yaya nan fa kowa ya shiga taitayinsa" fawan ne yayi maganar a yayin da yake cunkusa kebab abakinsa,
â—» Yadda fawan yayi maganar yasanya abbansu yin dariya, wai ga babban yayanan kowa yashiga taitayinsa, Kanal yusif yace "wato kaine annoucer duk in big bro zai fito sai kace kowa ya shiga taitayinsa, nawa ake biyanka salary ne ?
â—» Dariya sukayi gaba É—ayansu cikin nishaÉ—i in ka cire Twins dake ta faman jin bugun zuciya,

â—» A tare suka fito su biyu shi yana saukowa daga saman stairs yayin da shi kuma Haroon ke fitowa daga part É—insu dake a nan down,
â—» Jikinsa na sanye da tank top riga ce kamar singlet haka take fara, sai wando jeans, sumar nan tasha gyara,
â—» Shi kuma Haroon shirt ce da gajeran wando ajikinsa, ga uban gashin jiki da Allah yayi masa don ma Allah yasa kwantacce ne amma duk da haka ba kyan gani,
◻ Ganin Sgr yasa shi fara yi mashi kirari "Barka da Fitowa Babban yayanmu Namijin Zaki Uban dawa, mai mulkar ƙananun ƴan iska kai ɗaya tak kake tada runduna, gabanka Bullet bayanka Bomb ka ga Ingarmar Namiji ƙasaitacce takawarka lafiya Namijin duniya,'
â—» wannan kirarin na haroon yasa su Yousouf dariya, shi kuwa Sgr ko kallo haroon bai ishe shi ba,
◻ A tare suka ƙarasa ya zauna a empty chair ɗin dake kusa da Junaid, haroon ma yasamu wuri ya zauna,
â—» "Barka da safiya Abbana abun alfaharina,"
â—» Murmushi Abba yayi tare da cewa "Yawwa barka dae Haroon ya gajiyar tafiya ?
â—» "Abba ae ta washe tun jiya, yanzu garass nake jina,"
◻ Jinjina kai Abba yayi tare da cewa "Naji kace ka ƙaro wulaƙanci dagaske ne?
â—» Cikin sauri haroon ya saci kallon Babban yayan nasu yace "Bana cikin hayyacina ne, shiyasanya nayi maganar,"
◻ Murmushi su kayi gaba ɗayansu,bayan nan suka shiga gaishe da babban yayan nasu, bai amsa ba sai dai ya rinƙa yi musu alamar yaji da kansa, gyaran murya abbansu yayi hakan yasa Sgr ɗagowa ya kallesa cikin sanyin murya yace "Gm Dad,"
ta6e baki Abba yayi tare da cewa "sai ynx ka ganni? Ni fa narasa ganewa, nan gaba ina ga sai na rinƙa gaishe ka dakaina da alama,
"Insha Allah hakan bazata ta6a faruwa," sgr yayi maganar ayayin da yaÉ—auke idonsa daga nakan Abban, Murmushi Abban yayi, yarasa dalilin dayasanya yake jinshi sosae aransa ko dan yana kama da Momynsa alexandra,

Sehrish kuwa
â—» Wani irin sanyi ne ya ratsa zuciyarta time É—in da tayi arba da kyakkyawar fuskar Sgr duk da a firgice take ganin yadda haroon ke satar kallonta,

â—» tunkan azmee tayi yunkurin zuba mishi breakfast É—insa sehrish ta riga ta, plate ta É—auka ta zuba mishi Chips ta shake mashi shi, sannan ta tura mishi agabansa ta kuma haÉ—a masa da hot coffee a acikin cup,
â—» "Mlm tukur ni baza'a zuba min bane"? Haroon ne yayi mata maganar yana binta da wani irin shu'umin kallo,
â—» Jiki na rawa sehrish ta É—auki plate hannunta har kerma yake yi, tama rasa me zata zuba mishi,
â—» Muryarshi ce ta katse ta da cewa "Snacks nake so",

Cikin sauri sauri ta zuba mishi snacks É—in sannan ta haÉ—a masa da lemu a cup ta tura mishi,

â—» "Yawwa Good Job," ya faÉ—i yana kai hannunsa cikin plate É—in ya É—auki donuts yakai bakinsa,'

â—» matsawa tayi daga bayan sgr ta tsaya saboda ta
◻ samu damar da zata rinƙa kallon sumar kanshi da kyau, tana shakar turaren shi,
◻ Ji take tamkar takai hannunta ta shafi sumar nan tashi, tun da ta tsaya abayan sgr bata motsa ba, duk wanda ya faɗi yana buƙatar wani abu sai dae azmee ta zuba mishi, ita kawai Babban yaya take saving abunda yake so,
◻ ɗagowa junaid yayi da idonsa ya ɗan kalle ta dayake tana tsaye daga bayansu, mamaki ne ya kamashi ganin yadda sehrish ke ta faman kallon Babban yayan nasu ko kyaftawa batayi, sam bai kawo wa ransa komai ba game da kallon nata kawai yasanwa ransa cewa wata'ƙil respecting ne yasanya sehrish tsayawa abayan, kallonsa kuma da take yi may be burgeta yayi ne, amma yaso ace shi sehrish take ma wannan kallon dayaji daɗi, mayar da kansa yayi jikinsa a sanyaye yaci gaba da shan farfesun naman dake gabansa cikin plate,
â—» Sun jima suna É—awainiyar zuba musu breakfast É—insu kafin daga bisani kowa ya fuce, banda junaid da haroon suna acikin gidan, Sgr sun fita tare da abbansu headquater

_______________________________________________
Chapter 74 · 0% Book details