← Book details Abban Sojoji Local reading mode
READING PART 28 OF 92

Sashe 28

Abban Sojoji · about 8 min read

Bin jinin da kallo yayi tunani yayi kodai kansa ne ya bugu ayayin da ya sume a gefen stair,
Don haka cikin sauri ya koma yahau saman gadon inda ya kwantar da shi, a hankali yasa hannunsa yana tattare hular dake kanta a ƙoƙarinsa na ya cire hular yaga ta inda jini ke zuba,
Can kuma ya fasa saboda ganin yadda fuskar tukur É—in ta dame da jini da majina, handkchief ya zaro daga front pocket É—in rigarsa, ya shiga goge mata fuskarta,
Kwatsam gashin bakin da take manna wa a fuskarta ya ya goce saboda ya jigata gashi dama gam gare sa ruwa ya taba sa sosai ,
Hankalin junaid ba ƙaramin tashi yayi ba ganin ya cirewa tukur gashin bakinsa duk sai yaji ba daɗi yakai hannu domin ya gyara sai yaga ya ballo gaba ɗaya, da ya ƙura ido yana kallon ƙasan hancin sai ya gane cewa dama babu gashin bakin fixing ɗinsa akayi,
Saboda babu hudojin gashi a wurin sai kansa ya ɗaure ya gaza gane menene dalilin liƙa gashin baki,
tabe bakinsa yayi alamar i don't care, ci gaba da gogewa yayi ana haka sai ya ga gashin girar ta da aka liƙa masa shima ya zame gefe guda, tashin hankali a fili ya ce meke faruwa ne wai
Hannunsa ya sa ya ciro gashin girar duka guda biyun nan take asalin jagirarta mai kyau ga tsari ta bayyana,
Natsuwa yayi ya ƙurawa face ɗinta ido sai yaga fuskar ta koma ta mace sak ! Kansa ya gama ɗaure wa sanya gashin girar dana bakin yayi cikin handkchief ɗinsa ya naɗe su ciki ya ajiye gefen bedside drawer ɗinta,
Ya jima yana kallon wannan kyakkyawar fuskar har lokacin bai kawo wa ransa cewa maca ba ce ba sai da yasa hannu ya tumbuƙe hular dake kanta, nan take gashin kanta ya tarwatse ya warwaro har saman shoulder ɗinta mai kyau ga laushin gaske,
Nan fa junaid yayi zuru yana ganin wannan ikon Allah ( wonders shall neva ends)
ganin ta soma motsi zata farka, yasa shi yin wuff ya dira daga saman bed É—in ya boye abayan curtins É—in dakin,
buɗe idonta tayi waɗanda suka cika tab da kwalla, sunyi jawur sun ƙanƙance, wani irin raɗaɗi taji a marar ta, gashi sam ba ƙwarin jiki atattare da ita, wata irin kasala ce ta dabaibaye ta a galabaice ta miƙe tana zubar da hawaye, yunƙurawa tayi tare ɗan matsawa gefe nan taga jini malale a saman bedsheets ɗinta ya baci sosai ,
Wani irin mugun bugu xuciyarta tayi mata saboda ita sam batasan jinin menene ba, saboda bata ta6a yinsa ba wannan ne karo na farko a wannan shekarun nata 17years,
lokaci guda ta fashe da matsanancin kuka ganin jini 6aro 6aro na fitowa daga jikinta, cikin kuka take faÉ—in "innalallahi wa'inna ilaihirraji'un shikenan na mutu wayyo Allah wannan wane irin ciwo ne naji haka, nasan mutuwa zanyi
tashi tayi a firgice tasa hannu ta cire zanin gadon ta nannaÉ—e sa ta ajiye sa anan,
gaba ɗaya ta fita hayyacinta ta zabure kamar wata mahaukaciya tama rasa me zatayi , cikin toilet tashi ge tana kukan baƙin ciki ,
A jiyar zuciya junaid yasaki, har yanzu ya gaza gasgata abunda idonsa ke ganin masa, shin wanene wannan tukur mai aikin mu ko kowa ? kamar mace nake gani fa, oh my God mafarki nake ko gaske, kodai idanuna ne ke nuba min hakan taya tukur mai aikinmu zai kasance mace !! Ya jefa kansa wannan tambayar
Hannu yasa tare da murxa eyes É—insa don yayi comfirming abinda ke faruwa cewa gaskiya ne its not a dream,
yana nan tsaye la6e a bayan labulen yana jiran fitowarta, saboda ya gane wa kansa zahiran abunda ke faruwa ,
Sehrish kuwa tamkar ranta zai fita, saboda tsoran jinin da ta gani ga kuma ƙyanƙyami daya kamata,
cire wandon jikinta tayi sannan ta cire rigar ma, hannu tasa ta balle abunda take matse ƙirjinta dashi tayi wurgi dashi,
ta firgita da ganin yadda jinin yake gangarowa a tsakankanin cinyoyinta kai kace fanfo aka buÉ—e,
Cikin tsananin tsoro ta ƙarasa gaban fanfo tashiga dambe da jinin nan ita ala dole sai ta dakatar dashi daga fitowa 😟
Tana wanke wa yana sake kwaranyo wa kamar ana ingiza shi,
ganin yaƙi tsayawa yasa ta dakata, ta zuƙunna a wurin tana kuka tayi mai isarta, sannan ta yanke shawarar ta koma cikin bedroom ɗin ta samu wani abu ta cusa, sam ta manta cewa pant ɗinta ɗaya ne kuma ya bace shima, koda me zata sa ?
A haukace ta fito cikin sauri junaid ya rufe idonsa tare da jan labulen ya rufe face É—insa, bai jin daÉ—in tsayawa ba saboda yaga abunda yake haramin agare sa sam babu kaya ajikinta,
Jikinsa ne yasoma kerma nan take yadinga jin zuciyarshi na tashi ynx ya tabbatarwa kansa cewa tukur mai aikinsu zankaÉ—eÉ—iyar budurwa ce ba namiji ba, shigar maza kawai take yi saboda wani dalili nata,
buɗe wardrobe ɗin tayi saboda rashin natsuwa duk ta watso da kayan dake ci tashi ga laluben ɗan kyallen da zata sa, wani mayafi ta ɗauko sai da ta riƙe sa gam a hannunta sannan ta tuna cewa bata da pant ɗin da zatasa,
zuƙunne wa ƙasa tayi ta shiga rera wani sabon kukan, gwanin ban tausayi jin har yanzu wannan blood ɗin yana mata flooding a under ɗinta yasa ta koma cikin toilet tana kuka,
Shiga tayi taja kofar ta rufe ...
Ganin ta shige yasa junaid saurin fita daga ɗakin, tafiya yake amma tunanin yadda zai taimaka mata yake yi saboda ya gane cewa akwai abubuwan da take buƙata, amma tayaya? bayaso ta gane cewa ya ganta a matsayin mace, baisan wani hali zata shiga ba,
Maganar abbansu ya tuna a inda ya ke cewa
_aduk lokacin da kuka ga wani na buƙatar taimako, to kutaimaka masa indai kuna da halin yin hakan, a sanadiyar hakan kuma Allah zai agaza muku a lokacin da kuka shiga wani hali na rayuwa,"
Cikin sauri ya hanzarta nufar bedroom É—insa , key É—in motarsa ya dauko tare da kuÉ—i , sannan cikin gaggawa ya kama hanya ya fita daga main palour É—in ,
Babu kowa tsit kake ji amma ko'ina akwai haske kamar rana, saboda an ƙawata gidan gaba ɗaya da wasu irin electric bulbs,
Moto park É—insu ya nufa buÉ—e inda tarin motocinsu ke nan, motarsa yayi ya shiga nan take yayi mata key yaja ta,
Sam junaid ya manta cewa security guards É—in gidan soldiers ne kuma bana wasa ba, kuma ba'a basu iznin subar wani ya fita a wannan lokacin ba kosu fawan dake satar hanya su fita night club su suka san ta boyayyiyar hanyar da suke fita,
Santal ya miƙi titin da zai sada ka da babban gate ɗin gidan, yana isa wasu gabza gabzan sojoji guda 4 suka tunkare sa kamar zakuna,
a dolensa ya dakata da tuƙin ya tsaida motar, jikinsa sai rawa yake yi ba don komai ba sai don uzirin dake gare sa, zuge glass ɗin motar yayi yana kallonsu a yatsine, .
"Where are you going in this darkness night,"? ɗaya daga cikinsu ya tambaya yana kallonsa, banza yayi baice musu komai ba don yasan koya ce ɗin ba barinsa zasu yi ya fita, rigima ce zata tashi ƙarshe suce zasu sanar da Abbansu a tada hargitsin duniya,
jin yayi shiru yasa ɗaya daga cikinsu daka masa tsawa tare da cewa "maza ja mota ka koma gida ƙaramin yaro dakai sai taurin kai,'
ÆŠaya daga cikinsu ne ya kwatsa ma wanda yayi masa tsawa magana" stop shouting at him ! he's a young lallashinsa ya kamata kayi ya koma "
xukunno wa yayi cikin lallami ya ce masa "pls go back ba'a bamu izni mubar wanin ku ya fita ba daga gida a wannan time É—in,'
girgiza kai junaid yayi tare da cewa "am sorry to say i won't go back just allow me to go, duk rigimar da za'ayi sai dai ayi amma ba inda zani i will stay here till u give me the permission to go,'
Ya ƙarasa maganar tare da jingina kansa jikin kujerar motar yana kallonsu fuska adaure"
*_Hafsat Bature_*
~(Boss Lady)~

Page 33-34

Kallon juna suka shiga yi, ganin cewa ya toge yasa É—aya da cikinsu sake yi masa magana cikin lallami " tell me why do u want to go out ? if u need something i can go and buy it for you ,"
Jin hakan yasa junaid jin sauƙi aransa, hannu yasa ya zaro kuɗi kusan dubu goma ya miƙa masa sannan ya cije ya daure ya ce "pads nake so na mata kwali guda sannan panties dozen ɗaya bansan size ɗin ba amma karya wuce na ƴar 17 years "
tsananin mamaki ne ya kamasu jin yace pad da panties, amma basu ce komai ba saboda baya a tsarin aikinsu fira ko tambaye tambaye da É—an masu gida,
"Sojan yace shikenan, ka koma ciki nan da 15 minutes sakonka zai iso,
Amsa yayi da cewa "thank you i will be waiting,"
Sannan yaja motar a hankali yayi baya da ita ya karya kwana ya koma ciki,
A bangaren sehrish kuwa tagama galabaita, ta jigata sosai tarasa uwar ubanta , sai faman zarya take tsakanin toilet da bedroom , daga taji ya zubo sai taje ta wanke ta dawo ciki yana ƙara zubowa sai ta koma da gudu tana kuka 😖
Chapter 28 · 0% Book details