← Book details Abban Sojoji Local reading mode
READING PART 27 OF 92

Sashe 27

Abban Sojoji · about 5 min read

•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•
*_Hafsat Bature_*
~(Boss Lady)~

Page 31-32

Ba ƙaramin zafin marin nan sehrish taji ba, don kuwa har hancinta sai da ya fashe cikin kuka take basu hakuri " kuyi hakuri bada sani na hakan ya faru ba bazan ƙara ba,
tsawa fawan ya daka mata "hakuri fa ? A wannan babban laifin da ka aikata zamuyi maka hakuri dole ka É—anÉ—ani kuÉ—arka kasancewa agidan Abban sojoji kake aiki,!"
duk sai junaid yaji jikinsa yayi sanyi ganin yadda mai aikin yake ta zubar da hawaye amma ba yadda zaiyi kuskurensa ne!
cikin tsananin 6acin rai Jahan ya ruko hannun Ayaan suka shiga ciki saboda ya shafa masa magani don wurin har yayi jawur ya tattare,
dukar da kai sehrish tayi tana jiran sauran hukuncin da zai biyo baya,
Fawan ne yaso ma magana " ka fara tsallen kwaɗi daga nan har zuwa saman stair ka zakayo ta ɗayan stair ɗin ka kewaye falon gaba ɗaya haka zaga dinga yi har mu kammala cin dinner ɗin mu, bayan nan akwai wankin motoci kusan goma da sukayi ƙura sun jima a ajiye, a wanke su tsaf duk a cikin daran nan nakeson hakan, sannan ba shikenan ba gobe akwai wani horon,'
ba ƙaramin tashin hankali ta shiga ba jin irin wannan muguntar da fawan ya tsara mata, ta razana sosai saboda girman wurin babban tashin hankalin shine tsallen kwaɗi a saman matattakalar bene har biyu ya abun zai kasance?
muryarsa ce ta katse ta "Oya start frm now, we're watching you banda tsayawa if u do so you will see the trouble,'
Zukunnawa tayi ta fara tsallen kwaɗin ta miki hanya ta tafi , idonta cike taf da hawaye damuwa iri iri, tasha wahala fiye da tunanin mutun tun tana yi cikin daɗin rai har kafafunta suka soma rirriƙewa ga wani irin raɗaɗi da suke yi mata, numfashin ta ne ya soma fita agalabaice amma haka ta jure ta daure taci gaba da yi , lokaci guda ta hada jini da majina a fuskarta hancin ta yasoma bleeding dama tana yi in taji wuya, babban tashin hankalin ma nan take period ta balle mata jini ya soma zuba ta ƙasan ta Subhanallahi ,
tana jin ɗiɗɗigar wani abu ta cikin pant ɗinta yana gangarowa amma batasan menene ba, Allah yaso wandon jikinta baƙi ne bazaiyi saurin bayyana ba, shi dama jinin al'ada sometime bakar wahala na kawo sa a time ɗin da bakayi tsammani ba,
Sam junaid ya gaza samun natsuwa yarasa dalilin dayasa yake jin tausayin tukur ɗin nan mai aikinsu, ganin bazai iya jure ganin wannan zaluncin na fawan ba yasa shi tashi cikin sauri yabar table ɗin duk da bai koshi da abincin ba ya miƙi hanyar zuwa ɗakinsa yana hawa saman stair ɗin suka ci karo da ita alokacin take saukowa , dakyar take numfashi kamar kwaɗo haka ta koma , bin kafafunsa tayi da kallo a hankali ta ɗago da idonta wadanda suka kaɗa su kayi jawur ta kallesa shima a lokacin idonsa nakanta da take zuƙunne hannunta ruƙe da kunnuwanta,
Ido cikin Ido suke kallon juna tazama gwanin ban tausayi baiwar Allah, shi kuma amatsayin namiji yake kallonta tsananin tausayi ne ya kamasa a hankali ya furta "Am sorry" cikin wannan sanyayyiyar muryar tasa, yana faÉ—in hakan yabi ta gefenta ya haye sama,

Sai da kowa yabar dining table ɗin amma fawan mugu yana nan zaune yana jira mai aikin nasu tukur yagama punishment ɗin daya basa, sannan suje ya nuna masa motocin da zai wawwaken duk acikin daren nan kusan ƙarfe 9,_
JUNAID
tun da ya shiga room É—insa ya gaza samun natsuwa tunaninsa yaron nan mai aikinsu tukur bai kamata abarsa yayi wankin motoci cikin daren nan ba saboda shima mutun ne kamar kowa, in akai masa hakan ba'ayi masa adalci ba!
Tunano wa yayi da maganar babban yayansu (talaka da mai kuɗi duk ɗaya suke a wurin Allah babu wani banbanci don haka kada ku kuskura don Allah yabaku wani matsayi aduniya kuce zaku wulaƙanta wanda ke ƙasa da ku domin bakusan Wace rana zai yi muku ba, kuma Allah zai iya kar6e wannan matsayin da kuke taƙama dashi yaba shi wannan wanda kuka ƙasƙantar aranar ya zakuyi ? kowa zai iya kuskure a rayuwarsa amma aduk lokacin da wani yayi maka badai dai ba kazamzo mai hakuri da yafiya domin Allah ma yana gafarta mana in mukayi ba dai dai ba sai mu ƴan adam zamu gaza yin haka bazamuyi koyi da manzon Allah (SAW) ba ?
tuna wannan maganar yasa shi fita cikin sauri ya , cikin gaggawa yake saukowa down stair a lokacin har sehrish ta sume a ƙasan last step ɗin benen, shi kasan fawan baisan hakan ya faru ba saboda wayarsa yake ta faman daddanawa ,
Hankalin junaid ba ƙaramin tashi yayi ba ganin yadda me aikin nasu yake sume a kwance ba numfashi ,
tsallake sa yayi ya wuce inda fawan ke saune sai faman murmushi yake yana daddana waya ,
Kamar daga sama yaji an fizge wayar daga hannunsa, cikin sauri ya É—ago yana kallonsa yace "Junaid wannan wane irin abune zaka sa hannu ka fisge waya daga hannuna kamar wani tsaranka,'
harara junaid ya wurga masa tare da cewa "bansani ba! saboda tsabagen mugunta irin taka kasa wancen mai aikin wahala wadda tasa shi sume wa amma sam baka damu ba ,"
tsoki fawan yasaki tare da sa hannu ya ƙarbe wayarsa ya wuce tagabansa yana faɗin "Matsalarsa ce,"
Binsa da kallo yayi har ya shige bedroom É—insa,
Ba yadda junaid ya iya dole ya koma inda tukur ke sume yasa hannu ya É—aukesa, sam baima san ina ne inda É—akin kwannansa yake ba ,
Amma yasan cewa bazai wuce kwanar da É—akin azmi take ba, kama hanyar yayi , ko nauyi baya ji haka ya dauke ta kamar yar baby ,
cikin sa'a ya samu É—akin,da kafarsa ya turo kopar É—akin ya shiga da ita , a saman bed ya kwantar da ita
Ransa ne ya basa ya dauko ruwa a freezer yazo ya yayyafa masa , yana sa hannu zai buɗe kofar idonsa yakai a jini dake hannunsa, har sai da gabansa ya faɗi rass ! ya soma tunanin jinin menene wannan !!! 😳
Chapter 27 · 0% Book details