← Book details Abban Sojoji Local reading mode
READING PART 7 OF 92

Sashe 7

Abban Sojoji · about 8 min read

Bayan fitarsu sehrish ta zabga uban tagumi tana jin kewar kasancewarta ita kadai a wannan hamshakin gidan da batasan kowa a cikinsa ba , gashi tazo a matsayin namiji , duk in ta tuna wannan hankalinta tashi yake , abu dayane ke kara mata karfin guiwa , y'an uwanta in ta tuna su sai taji ba irin kasadar da bazata iya shiga ba ,

Dawowa ciki azumi tayi fuskarta a sake tace da sehrish " tashi mu shiga ciki na nuna mka bedroom din ka , in ka huta zuwa anjima before magrib zamu shiga kitchen",

Sehrish ta amsa da toh tare da mike wa tabi bayan azmi , suka shiga ciki tayi mamakin bedroom din da azmi ta nuna mata a matsayin nata na yar aiki , wannan koda amayarce tasamu wannan falillahil hamdu , ba tarkace a ciki , single bed ne , ga beside drawer mai dauke da bedside lamp a samanta ga wardrobe madai-daiciya ta manne jikin bango , ga wadatattun curtains a kowane window , komai na cikin bedroom din brown color be banda labulayen da suka kasance milk colour , da zanen gadon ,

Ba abunda ya kara burgeta sai dressing mirriow din da tagani , duk da ba cosmetics a samansa , madubin yayi mata da yar chair din dake gabansa ,

Murmushi azumi tayi ganin yadda yaron yake ta farin ciki don haka tace "komai yayi ko "? da sauri ta amsa da "eh hajiya harma yayi yawa "

Dariya azumi tayi jin yace harma yayi yawa ,
"Ynx dai ni zan shiga ciki , ka zauna ka huta , sannan akwai bedsheets a cikin wardrobe din nan , in zaka canza saika dauka ," tana gama fadan hakan ta fice ,

Kamar jira takeyi azumi ta fita tahau ihu tana tsalle , kafin ta tsagaita da haukan nata ta shiga bathroom din dake ciki ,

Nan fa ta soma wani sabon kallon , ko a mafarki bata taba tunanin zata mallaki irin wannan tsantsararren bathroom dinba mai kama da bedroom saboda haduwarsa ,

Dakyar ta samu natsuwa , ta dauro alwala tafito , a cikin wardrobe din ta samu prayer mat (sallaya) ta dauko ta shimfida , ta kabbara sallah , duka ta hada tayi zuhr da isha saboda batasamu damar yi ba a kan hanya , gashi ynx ankira isha'e shiyasa ta hadesu duka tayi ,

Bayan ta idasa sallar , ta daga hannayenta sama tana addu'ei at the end ta fashe da kuka , Sbd tuna wa da halin da y'an uwanta ke ciki , magana ta soma yi cikin kuka " har ynx na gaza yarda cewa nice zan yi rayuwa a cikin wannan daular ba tare da y'an uwana ba , taya zanji ddin rayuwata batare dasu ba , ni ina nan sukuma suna asibiti cikin wani hali , Allah sarki rayuwa ! bazan taba yafe ma wanda yayi silar shigarmu cikin wannan tashin hankalin ba , Ya Allah ka hana sa jin dadin duniyar nan gaba daya , Ya Allah ka kaskantar da rayuwarsa kamar yarda yayima ta mu....." kuka ne yaci karfinta har ta kifa kanta saman sallayar tana cewa "I will never forgive u in my life and I will neva forgt u ! i must take revenge koda ace nikadai ce na rageda zan yafe maka ka shiga aljanna to tabbas bazaka taba shigar ta ba.
*_Hafsat Bature_*
~(Boss Lady)~

Page 9-10

Bata tashi daga saman sallayar ba har aka kira Magriba tana tunanin abu daya, sai da ta kammala sallar sannan ta nad'e carpet din ta turasa cikin wardrobe , tare da hijab din duka.

tsayawa tayi gaban dressing mirror tana kallon kanta a cikinsa , sak namiji ba wanda zai gane mace ce sai yanayinta ya koma kamar d'an daudu , hannu tasa tare da shafa gashin bakin da ma'reeya ta sanya mata , murmushi ta d'an saki a ranta ta ce "Sehrish ke nan dramatic girl."

Kara kimtsa kanta tayi saboda azmi tace mata akwai aiki a kitchen da zasuyi, sai da ta fara rufe kofar dakin gudun kada Azumi ta same ta tana canza kaya , ta gane cewa maca ce ita ,

Cire kayan jikinta ta yi , ta maida su cikin bag dinta , sannan ta dauko wasu riga da wandon , ta rige a hands sinta gaban mirror din ta koma ta tsaya tana kallon jikinta , ziririn pant ne a ajikinta , takai hannu tasha fa flat tommy dinta , wanda yake a dam'e kaman bata cin abinci saboda shafewarsa ,

Mayar da hannun tayi saman boobs dinta wadanda ta matse su gam , da abun matse belly , har cikin ranta ba taso hakan ba tana son abunta ssae , amma ba yadda zatayi duk cikin aiki ne ,

ga hairs dinta da aka maida mata shi guntu , amma hakan bai dame ta saboda a iya sanin ta in aka aske mata gashi irin hakan cikin one month zai koma yadda ya ke tsayinsa ma harya karu ,

Jin alamar tafiyar mutun kamar bedroom ta ake nufowa shine ysa ta yin saurin , zura dogon wandon tare da rigar sa , tayi gaggawa gyara daurin da m'reeya ta yi mata , mai kamar rawani ,

Kwan ! kwan !kwan taji an knocking , cikin sauri ta karasa ta bude kopan azmi ce tsaye fuskanta da murmushi tace "tukur ina fata ka shirya sbd ynx zamuje na nuna maka yarda abun aikin yake ,"

Cikin girmamawa sehrish tace "toh hajiya ,"

Azmi tayi mata wani irin kallo har gaban sehrish ya tashi a tunaninta ta gano lagwanta , amma sai taji tace "stop calling me hajiya , my name is azmi call me by my name , cos we re d same , am a house maid just like u ,"

taka rasa mgnr tare da fice wa tana cewa "follow me" rishi ta bi bayanta tana d'an murmushi ,

Kitchen suka shiga amma sehrish ta gaza gane a ina suke , haduwar wurin ce ta rikitar da ita , an kawata komai na kitchen din da dukkannin abubuwan da akeso,

Sam ta manta aiki ya kawosu sai faman kalle-kalle take yi , sai da taji muryar azmi a kunnanta sannan ta dawo dai dai

"tukur ynx bamu da enough time , we'll make a dinner now in yaso zuwa tomorrow i will explain everything to u , Especially zama da samarin gidan nan darasi ne me zaman kansa duk zan koya maka ,"

sehrish sai take ganin maganar azmi kamar shiriri tace , ynx har akwai mutumin da za ace sai an koyi darasin zama dashi ?

haka suka fara aiki , azmi ce ke yin girkin , yayin da tabarma sehrish ferar dankalin turawa , ga yankan albasa , acewarta tafara da karamin aiki ,

Suna cikin aiki sehrish tafara jiyo karar shigowar motoci , rass taji gabanta ya fadi , da jiniya motocin ke shigowa ,

"Hmmmm wannan alama ce mai nuna cewa masu gidan sun dawo " a cewar azmi ,

Zuciyar sehrish sai harbawa take yi saboda tsananin firgicin da wa zata fara cin karo ,

"Ka'ida ne daga sun shigo babban falo zasu fara kwalamin kIra ka saurara kaji ," azumi ta fada tana murmushi ,

Hannun sehrish sai kakarwa suke yi ,

ita dai baza ta iya tantance muryar mutun nawa bace amma taji sauti iri iri

"Azumi ! Azmi !! Azam zam !!!" da karfi suke kwala mata kiran without any respect , cikin sauri azmi ta fice tana ce ma sehrish "pls ka kula da girkin am coming back now ,"

Sehrish ta amsa da toh , daga inda take tana iya hangosu saboda kitchen din irin model design dinnan ne wanda ba kopar shiga gare sa a bude yake bata iya identifying faces dinsu ,

Hankali a tashe azmi takarasa wurunsu tana fadin "welcome back Sirs ," ko arziki amsa bata samu ba sai complaining da suka soma yi mata, "Ina fata angyara min bedroom dina don bansan kazan ta ! in ma kinsan baki gyara ba let me know ," daya daga cikinsu ne yayi wannan maganar ,

matsawa tayi kusa dana gefensa don taji shi mai zaice , hannu ysa yana shafa ciknsa yace "Ni matsala ta abunda zansa ma cikina pls kafin na shiga ciki nayi bath na tarar da abinci jere saman dining table if not kinsan sauran ,"

matsawa azmi ta sake yi kusa dana gefensa dayake duk suna a jere kusansu takwas,

" Na fadamiki Injin wanki na ya samu matsala dazu da safe ga shi na tara kayan dauda , gajerun wanduna na ma duk sunyi dirty dafatan kin wanke mun su ,"

Haka ta dinga sauraransu ba wanda baiyi magana ba acikinsu , bayan ta gama sauraransu one by one tace " Komai da kuka lissafamin na kammala sa , abinci ne kawai shima ynx zan idasa ,"

Kama hanya suka yi kowa ya wuce bedroom dinsa , wasu na upstairs wasu na a downstairs,

Babu abunda ya burge sehrish sai kakin sojojin dake jikinsu , abunka ga handsome guys ga tsawo ga hadaddiyar sura sai abun ya bada citta 😘

tunanin ta soma yi a ranta "oh ni ko wanene babban yaya acikinsu , koda yake naji azmi tace ba sojan nigeria bane U.S ARMY ne , zanso nagansa daga ji ya hadu yadda hajjaju ke zuzu tashi ,"

takarasa tunanin tana murmushi ita kadai abunta , shigowa azumi tayi tana fadin "maza tukur a shirya abinci a dining before su fito, ai ina ji girkin ya isa ya kammalu ,"

Wasu hadaddun kuloli ta dauko daga kitchen cabinet kamar ranar aka budesu daga kwalinsu tsantsar kyansu kamar ba abinci za'a zuba ciki ba , saboda yadda murfinsu ke glowing har face dinka zaka iya gani aciki just like mirror ,

A wani faffadan tray ta shirya komai ciki , ta mika wa sehrish azuwan taje ta fara shiryasu a dining ,
Chapter 7 · 0% Book details