Sashe 57
Abban Sojoji · about 8 min read
At same time heart É—insu ke beating da karfi, ya jima yana mamakin wata zararriya ce wannan ta faÉ—o masa a Æ™irjinsa haka, this is d first time da mace ta faÉ—a masa a jikinsa, wadda ba muharramarsa ba, babban abunda ya É—aure masa kai yadda yarinyar ta Æ™anÆ™amesa bama Alamar zata sake shi, yana jin duk wani moving É—inta ajikinsa, hatta numfashi ta dake fita cikin sauri sauri, kamar jinjira haka ta kwanta masa luf tana sauke ajiyar zuciya, Mutanen dake wurin kowa yayi zuru yana kallon ikon Allah, wasu kam sai godiya suke wa Allah daya kawo masu sauÆ™i, har aka amshe gun É—in dake hands É—inta, Jahad kam wadda ke cikin matsanancin tashin hankali, ganin bala'en da hosana ke Æ™oÆ™arin ja musu, cikin yanayi na firgici ta Æ™arasa inda hosana ke jikin bawan Allahn nan ta ruÆ™o hannunta da Æ™arfi ta fisge ta daga jikinsa tana cewa "Dan Allah kayi HaÆ™uri bawan Allah, ba da sanin ta tayi hakan ba, she did it unintentionally, tana da ta6in hankali ne.....' muryar na rawa Jahad ke kora masa bayani, Har time É—im bai cire face mask É—insa ba, kuma bai janye idonsa daga na Yarinyar ba, "Ki rabu dani !!!!" honasa ta faÉ—i tare da cire hannunta daga na Jahad ta matsa wurin mutumin nan, da ta faÉ—a mawa ta sa hannunta cikin nasa ta riÆ™e kam tana kallonsa cikin muryar kuka tace "dan Allah ka rabamu da waÉ—annan masu baÆ™aÆ™en kayan wlh sun takurawa rayuwarmu, duk inda mu ke bin mu suke yi, wlh ba mu bane muka kashe ta ba, mun faÉ—a musu sunki yarda, ni dai kace su rabu ni in ba haka wlh zuciya ta bugawa zatayi na mutu kowa ya huta.....' "Hosana !!! Ba ki da hankali ne !! Kinsan wanene shi ki !! meyasa ki ke tona mana asiri ne agaban mutane," jahad ce tayi maganar ranta a 6ace ta janyo hosanar da karfin gaske ta dawo gefenta, Su dae mutanen dake tsaye tare da police É—in sun zuba ido suna sauraron su, Rai a 6ace hosana ta sake fisge hannunta daga na Jahad cikin Æ™unar rai tace "ki rabu dani, ki Æ™yale ni nace !!! meyasa kowa bai son mune !! Laifin me muka aikata, babu mai Æ™aunar mu wlh Jahad ba zan koma cell ba sai dae a shigar da gawa ta, amma bani ba,' tana gama fadar hakan ta koma wurin mutumin nan dae dake a tsaye, ta zura hannunta cikin lallausan tafin hannunsa ta rike gam, ta marairaice masa da kyawawan idanuwanta tace "Dan Allah ka tafi dani,ka da kabarni anan, bana son ganin waÉ—annan masu fararen kayan (wato likitocin dake tsaye da nurses É—in dake wurin) kuma bana son waÉ—annan masu bakaken kayan," ta faÉ—i tana nuna Æ´an sandan dake tsaye baki asake suna kallonta, kwantar da kanta tayi a damtsen hannunsa, sannan tasanya dukkan hannayenta ta rungumo nashi, (mutu ka raba kenan) Lumshe idonsa yayi a hankali, sai lokacin kallon police men É—in dake tsaye a wurin yace "wane irin shashanci ne yasa ku kabar yarinya harta kwaci bindiga daga wurinki!!"? Ya tambaya yana kallonsa, Rai a6ace wani inspector yace "kaga malam ka iya bakinka, mu jami'an Æ´an sanda ne munsan me muke..." tunkan ya Æ™arasa major É—in dake bayansa wanda ya fusata rai a6ace yace "Ka iya bakin ka !! Kasan wanene shi!!!"? "maganar wanene shi bata shafe mu ba, mu dae a bakin aikin mu mu ke," wani inspector ne ya bashi amsa a yayn da ya fiddo da ankwa alamar zai sanya masu hosana, Itakam Æ™ara kanÆ™ameshi take yi, gaba É—aya ta gama kashe mishi jikinsa, daurewa kawai yakeyi, "Laifin me suka aikata"? Ya tambaya yana kallon Æ´an sandar, Wannan copral É—in ne yayi saurin cewa "ana suspecting É—insu da kisan wata tsohuwa wadda take riÆ™onsu," Shiru ya É—anyi tare da jinjina kai, kafin yace "Cancel the case (akashe case É—in)" É—agowa su kayi jami'an Æ´an sandan suna kallonsa cikin mamakin jin abunda yace, a fusace wannan inspector É—in yace "malam wai wanene kai !! dame kake taÆ™ama ne !! kaga ka kama gabanka kawai cikin salama, in ba haka ba, zamu haÉ—a dakai mu tafi police station.....' Jikin major É—in dake bayansa har tsuma ya ke yi wurin cewa," Shut Up Stupid !!! ka iya bakin ka Æ™aramin Æ™waro ko kuma nayi Æ™asa Æ™asa daku a wurin nan....' cikin hanzari ya dakatar dashi tare da cewa "i did not allow u to talk again, last warn,' Shuru major É—in yayi sai faman huci yake yi tamkar zaki, rai a6ace ya wurgawa Æ´an sandar bindigarsu Æ™asa, Matsawa Inspector É—in yayi da nufin yasanya wa hosana ankwar dake hannunsa, amma sai mutumin ya dakatar dashi da cewa "karka kuskura !!! domin ban bada izini atafi da yarinyar nan cell ba, kamar yadda ta roÆ™e ni cewa bataso ta koma, daga nan ba inda zata je," Mamaki ne ya rufe Æ´an sandan, inspector É—in yace "idan ka cika shisshigi zamu sa bindiga mu kashe ka !! A wurin nna," Jinjina kai mutumin yayi tare da cewa "idan kuka kashe ni, ba hukumarku kaÉ—ai bace zata shiga haÉ—ari ba, gaba É—aya sai an tada nigeria saboda raina kawai," Kansu fa ya gama É—aukar zafi kowa mamakin wannan mutumin ya keyi, ganin ya toge yaki bari su ta6a yarinyar dake kwance ajikinsa yasa inspector É—in cewa "wai dan Allah wanene kai!!"? "Yanzu naji bayani" acewar mutumin bayan ya faÉ—i hakan ya zura hannunsa cikin aljihunsa ya zaro Æ´ar waya nokia, ya yi dialing wasu numbers da basu fi 5 digits ba ya miÆ™a wa, inspector É—in wayar yace "Ka kira numbers É—in dana sanya ka tambaye su*WANENE MARSHAL OMAR* za ka samu amsar da kake so," Jikin kowa yayi sanyi jin ance marshal, shi kansa inspector É—in yana É—an sauko, hannu yasanya ya kar6i wayar, ya danna call tare da karawa a kunnansa, one bugu on É—auka, cike da kwarin guiwa É—an sandar yace "WANENE MARSHAL OMAR, cikin harshen turanci yayi tambayar yana jiran amsa daga cikin wayar, tunkan ya cire wayar a kunnansa, wasu irin jibga jibgan motoci ne suka soma antayo wa cikin asibitin aguje masu É—auke da fusatattun sojoji zafafan gaske, runduna guda kamar a filin yaÆ™i, zaro ido su kayi gaba É—ayansu cikin tsananin mamaki, kowa dake kallon wannan al'amar tsantsar mamaki ne a fuskarsa, Da gudun gaske sojojin nan suka shiga dirowa daga saman motocinsu kowanne riÆ™e da manyan bindigogii, da gudun gaske suka tunkaro inda Marshal omar yake sukayi masa Æ™awanya, tare da buga Æ™afa suka sara mashi sannan suka haÉ—a baki wurin cewa "We're waiting for your command Sir !" (Umarninka mu ke jira yalla6ai) 😳 Gaba É—aya hankalin kowa yayi mugun tashi, sun tsorata ainin ganin sojojin ma ba na nan qasar bane, Black americans ne masu wata irin Æ™ira ta zakuna, kai kana ganinsu ba É—igon Imani a fuskarsu, umarninsa kawai suke jira, koda hospital É—inne su tada gaba É—ayansa 😳 Cikin rawar murya É—an sandar nan wanda yaci ka zaÆ™e wa yace "Yalla6ai, dan Allah wanene kai"? "dan Allah ka miÆ™a masa wayarsa, salin alin mu tafi," acewar wannan copral É—in daya gama tsorata, Hosana ta firgita sosai, amma maimakon ta cire hannunta daga nasa, sai ma ta Æ™ara Æ™anÆ™amesa sosai, duk yana jin motsin hannun yarinyar acikin nasa, ita kuwa jahad Æ™iris yarage tasaki fitsari don tsabagen tsoro, gashi tayi tayi da hosana ta janye hannunta daga nashi amma taÆ™iyi, Hankali fa ya tashi, kowa da ke wurin so yake yaga fuskar marshal Omar, sun jinjinawa Æ™arfin ikonsa, . "Yalla6ai! dan Allah ka karbi wayarka, wlh zamuyi biyayya akan abunda kace," acewar wannan copral É—in,' sai lokacin Marshal Omar yasanya hannu cikin natsuwa, a hankali tare da zame face mask É—insa, Wow zo ka ga ido Cikin wannan Cool voice É—in tasa yace "Sunana Marshal Omar, U.s Army ni É—ane ga Chief of Army staff wato Abban sojoji,' tunkan ya idasa maganar tasa gaba É—aya police É—in dake wurin suka sara masa, hatta sauran mutanen dake tsaitsaye a wurin duk suka sara mashi jin sunan daya ambata, "Nayi muku uziri ne, saboda na lura bakusan koni wanene ba, duk da nayi mamakin hakan," Sauke hannayensu su kayi, Tabbas sai yanzu suka shaida shi, abunda yasa suka rikice sun san cewa Marshal Omar É—in da su ka sani suke yawan gani tare da SGR ba anan suke zaune ba, kuma basu ta6a tunanin zasu ganshi ido da ido ba, sun saba ganinsa a kafafen sada zumunta, shiyasa su kayi tsammanin ko raina musu hankali zaiyi, gashi kuma yayi hiden face É—insa da mask sannan, babu uniform ajikinsa shiyasa komai ya shige musu, "Ynz yalla6ai ya zamuyi kenan? Domim Case É—in yaran ya kai har wurin commissioner of police, cikin week É—in nan ma muke shirin miÆ™a su court don gudanar da shari'a, rashin lpyr yarinyar ne ma ya dakatar da komai," inspector É—inne ya kora masa bayani, "Ku bar komai a hannu na, zan yi magana da commissioner É—in, zaku iya tafiya," ya basu umarni Yayi magana tare da amsar wayarsa daga hannunsa, ba musu Æ´an sandar suka kama hanya tare da barin asibitin suna masu tsananin mamakin Æ™arfin ikon Marshal Omar lallai shi ba Æ™aramin jan wuya bane 💪💪💪 (Yanzu shikenan an kashe case É—in su Hosana da jahad kurmus ya mutu) ðŸ˜ðŸ˜¬ Mutanen wurin gaba É—aya murmushi kawai suke saki, kamar a shirin film haka suke kallon lamarin, haÆ™iÆ™a marshal Omar ya gama tafiya dasu, Ajiyar zuciya kawai Jahad ke saki tarasa me zatayi don farin ciki, sam bakinta taÆ™i rufuwa (shin bana faÉ—a muku ba? Cewa dukkan tsanani yana tare da sauÆ™i? Sannan bawani yanayi na arayuwa da yake kasance wa na dundundun ba? this is an example) 💞😊 Murmushi kawai hosana ke saki, sam taÆ™i barin jikinsa har sai da yace "My hand" sannan ta janye jikinta, daga nasa tana zazzare masa waÉ—annan kyawawan idanuwan nata, sai faman murmushi take zabga mashi, shi kam binta kawai yake yi da kallo, "Kowa ya koma bakin aikinsa!!" Marshal Omar ya faÉ—i yana kallon jama'ar dake wurin, cikin sauri doctors É—in dake wurin da nurses É—in da other peoples É—in suka watse, Ajiyar zuciya yasaki tare da mayar da eyes É—insa akan major É—in dake bayansa yace