← Book details Abban Sojoji Local reading mode
READING PART 87 OF 92

Sashe 87

Abban Sojoji · about 8 min read

Zaune suke suna yin breakfast ga delicious nan kala kala, Æ´an soye soye, Æ´an lashe lashe cike asaman table É—in gabansu,
Jikinsu na sanye da dogayen riguna na larabawa,kwaunan ba kallabi bare mayafi sai dai gashi da suka zubo dashi,
    gyaran murya aunty babba tayi tare da ajiye cup of tea ɗin dake hannunta ta kalli hafsat cikin natsuwa tace "daughter me kike tunani game da twins ɗin can da Omar ya kawo mana su zauna tare damu"?
     ɗagowa hafsat tayi ta kalle ta da murmushi a fuskarta tace "Mommy ke baki fahimci komai ba kenan"?
    Aunty babba tace "Eh gaskiya a tunani na,
     Hafsat ta jinjina kai tare da cewa "Lallai kam Mommy ashe brain ɗita tafi taki ja? to bari na faɗa miki ma'anar waɗancan Twins ɗin,
   tayi maganar tare da ajiye spoon ɗin dake hannunta cikin plate sannan tace "Mommy Omar ya kawo waɗancan Twins ɗinne domin su samu kyakkyawan kulawa a wurinki suyi kyau su fito ɗas, daga nan kuma kinsan me zai faru"?
   ta tambaya tana kallon Aunty babba wadda tayi zugum tana kallonta tace "Har sai kin faɗa"
Hafsat tace "waÉ—ancan twins É—in babban matsala ne agareki Mommy, domin kuwa sune Nakiyar da zata tarwatsa miki target É—inki akan Sgr da Marshal,"
    dafe ƙirji aunty babba tayi tare da faɗin "Kamarya kenan hafsat? Kaina fa ya shiga duhu i didnt understand u,
    dariya hafsat tayi kafin daga bisani taci gaba da cewa "Mommy kin shiga Uku domin kuwa a fahimtata Omar bakowa yake wa tanadin waɗancan kyawawan tagwayen ba face Shi Kansa Da BABBAN YAYA........' dakatawa da magana hafsat tayi ganin yadda aunty babba ta zabura tsaye tana zazzare ido tana cewa "Allah ka rabani da mugun ji da mugun gani! Nashiga uku Ni LAILA !!
   Dariya hafsat tayi tana cewa "Mommy Calm dowm ur mind,zauna mana,"
    Hankali tashe aunty babba tace "taya zan kwantar da hankali na? Ni ina nan sake da baki sam ban lura da hakan ba, Eeeye!! Ni za'ae wa Iya shege,
   tayi maganar tana komawa mazauninta, sam fa ta razana da maganar Hafsat,
    Hafsat taci gaba da cewa "Mommy yanzu fa wuƙa da nama suna hannunki sai yadda kika so zakiyi,"
    Cikin sanyin murya ta wanda ya ruɗe Aunty babba tace "Yanzu menene shawara hafsat? Don na lura kinfi ni kai,"
   dariya hafsat tayi tana kallon mommynta ta, sannan taci gaba da cewa "Mafita ɗaya ce !! Koda gigin wasa mommy karki bari yaya Omar ya bar gidan nan da Twins ɗincan ! muddin hakan ta faru duk wani planing ɗinki akan Babban yaya da Marshal ya tarwatse,
   Jiki na rawa aunty babba tace "taya ma zanbar hakan ta faru? Ae in kinga sunbar gidan nan gawarsu aka fidda Allah, yanzu sune enemies ɗina tabbas zasu ci Ubansu Allah,amma hafsat yaya zamuyi ? ta tambaya tana kallonta
   "Abunyi shine kisa a 6atar dasu ! A jefar dasu nesa da gari can bayan gari,' hafsat ta faɗi tana murmushin mugunta,
   Aunty babba tace "to idan Omar yazo ya tuhume mu fa? What will be the solution of it?
    ɗan tsoki Hafsat taja tare da cewa "Kibarmin aikin kawai mommy, ni zan fitar dasu a moto ɗina da nufin zamuje wurin saloon, daga nan kawai sai in zubar miki dasu a nema arasa,"
   Fashewa da dariya aunty babba tayi tare da cewa "Good Job, that's why am proud of having u as my daughter,yanzu abunda za'ai Dama Omar yace baya buƙatar kowa ya kashe kosisin shi akan yaran, komai suke buƙata ayi mashi list ya biya, don haka yanzu zan zuƙa mishi uban kuɗi ya biya, dama ina so nayi tanadin na ziyartar wurin bokana,
   "Hakan yayi Mommy, text kawai zaki tura mishi kice zan fita dasu Shopping za'a siya masu suturar sawa, sannan za'a kai su gyaran jiki da sauran abubuwa da mace ke buƙata, kawai mom kice mashi ya bada miliyan ɗaya da rabi, ina mai tabbatar maki da cewa sai ma ya ƙara wani abu akai,"
  Murmushi kawai aunty babba ke saki tana kallon hafsat, tabbas kuwa takawo mata shawara mai kyau domin kuwa ba ƙaramin kuɗi zata samu ba,
   Miƙewa aunty babba tayi tare da cewa "Bari na ɗauko wayar na baro ta saman pillow,
   Wuce wa bedroom ɗinta tayi cike da zumuɗi tana tafiya jikin na rawa dama akwai ƙiba don dae tana da tsayi,
  Wayar ta ɗauko a hannunta tafito da ita tana faɗin "ashe Hajjaju ma tayimun missed calls ban gani ba,ƴar duniyar ae ina nan inajiranta,
   Komawa tayi ta zauna saman dining chairs ɗin tana facing Hafsat wadda taci gaba da cin breakfast ɗinta,
   "mommy bani wayar ki gani, ni zan masa text ɗin,"
Miƙa mata wayar aunty babba tayi, bayan hafsat ta kar6a ta shiga Messages ta zauna ta tsara komai na kuɗin da Omar zai turo hada account number, sannan ta tura masa,
  "Yana ganin message ɗin zakiji Alert,"
   Aunty babba tace "Allah ko"?
Hafsat tace "ae yadda kikasan Central bank haka suke shi da Babban yaya, basa jin wuyar fidda kuÉ—i a hannunsu,"
  "Shiyasa nake so Hayaam da abrah su sami gurbi a zuciyoyinsu ta ƙarfi ta tsiya kin ga daganan zasu rinƙa tatso mana muma mu raya dangin namu koya kikace"?
  Dariya hafsat tayi tare da cewa "ki dai raya danginki mommy, domin kune talakawa donni Dangin Abban sojoji ce gaba da baya,"
  "To iya magana, gori zakimin sauƙin ma ae daga cikina kika fito,"
  Dariya suka yi gaba ɗayansu,

Allah sarki su hosana kuwa tun da asussuba suke faman zagaye zagaye a cikin store ɗin, wata irin baƙar yunwa ke addabarsu gashi ko sallah basuyi ba tunda aunty babba ta garƙamesu acikin ɗakin, idanun jahad sun kumbura jawur saboda rashin bacci, ga wani irin matsanancin ciwon kai da take fama dashi mai raɗaɗin gaske,ita kuwa hosana babban tashin hankalinta shine Yunwa saboda bata da jumurin yunwa ko misƙala zarratin, tuni ta soma kuka tamkar ranta zai fita,
Sarai su Aunty babba da hafsat suna sane dasu, don suna jiyo kukan Hosana amma ko ajikinsu,

______________________________________

A 6angaren sehrish kuwa tunda asuba data farka tayi wanka tayi salla, bata koma bacci ba, zama tayi zugudum saman gadon tana tunanin abubuwa da dama, har time ɗin shiga kitchen yayi sannan ta miƙe dama a kimtse take, fice wa kawai tayi ta shige kitchen, gyara kitchen ɗin tashiga yi tsaf, daga bisani azmee ta shigo itama suka fara girkin nasu, a nan ne sehrish ke bama Azmee labarin abunda yafaru jiya tsakaninta da Junaid, tasha dariya kamar kamar me,
"Bawan Allah ya bani tausayi gsky, amma aunty azmee Junaid wasa yake yi ko? Ba asiri zai tonamin ba,"
Fuska É—auke da murmushi azmee tace "Baya cikin hayyacinsa ne shiyasanya yayi maki haka,"
Ajiyar zuciya sehrish tasaki tare da cewa "Amma fa gsky junaid ya tsoratar dani daren jiyan nan,"
    "Naso ace nima ina nan abun ya faru dana kalli Comedy," acewar azmee,
  Suna aiki suna firarsu cikin jin daɗi,

Junaid
A hankali yasanya hannu tare da janye bargon daya lullu6a dashi yana kallon inda babban yayan nasu yake kwance, babu shi a wurin, ransa ne ya bashi cewa tabbas ya shiga cikin toilet, don haka cikin hanzari yayi wurgi da bargon ya diro daga saman gadon ya lalla6a cikin sanɗa ya fuce, bai wuce ko ina ba sai kitchen dama da wata baƙar yunwa ya kwana jiya,

"Ga fa mutuminki nan", acewar azmee cikin sauri sehrish ta juya don taga wanene karaf suka haÉ—a ido da Junaid wanda shigowarsa kenan,
    Batasan lokacin da ta fashe da dariya ba, cikin mamaki Junaid ke kallonta, mayar da idonsa yayi kan azmee yace "Aunty azmee meya faru ne naga duk fuskarku ɗauke da dariya "?
    "Kana nufin ka manta abunda ya faru daren Jira kai da sehrish"? ta tambaya tana kallonsa,
Shiru yayi yana son tuna abunda ya faru jiyan, can yasaki murmushi cikin jin kunya yana sunnar dakai ƙasa,
Daker ya iya cewa "Sorry sehrish ni ba'a hayyacina nayi wannan ba, kinyi hurting É—ina ne, so abun ya tsaya mun araina shiyasanya nayi maki hakan,"
  Murmushi sehrish tayi tare da cewa "babu komai ae ya wuce, amma fa ka tsoratar dani Allah,"
Dariya yayi tare da shigewa cikin kitchen ɗin yasamu wuri ya zauna saman dining chair ɗin dake a kitchen ɗin yana faɗin "Ataimaka mun da breakfast ɗina yunwa nake ji, in ma ba'a kammala ba ko fruits ne ina buƙata," yayi maganar da hamma a bakinsa,

"Sehrish ki haɗama mutuminki mana,"  murmushi sehrish tasaki jin abunda azmee tace,
  A cikin tray ta shirya mishi lafiyayyen breakfast takai masa, sai faman satar kallon juna suke yi cikin jin kunyar abunda ya faru jiya,
  "Ki haɗamun Cornflakes,Asa madara dayawa, a zuba sugar sosai" ya faɗi yana yakai hannu cikin plate ɗin dake ɗauke da Yam & eggs soup yana ci,"
     Cikin hanzari sehrish ta ɗebo ruwan dispenser mai zafi ta haɗa masa cornflakes ɗin, ta zuƙa mishi madara da sugar aciki sannan takai mishi
   "Thank u, amma ki sani wata rana saina tona miki asiri like i said,"
    Fashewa da dariya sehrish tayi, shima dariyar yake yi,
Wuce wa tayi suka ci gaba da kula da girkin da suke yi,

bayan junaid ya kammala ya wuce wurin abbansu, a tunaninsa zaiyi masa faɗa akan nemansa da sukayi jiya amma sai yaga akasin hakan, kyakkyawar tarba yayi masa sai faman jan shi yake da fira saboda yayi kewar surutunsa jiya, hakan ba ƙaramin daɗi yayiwa junaid ba don baisan kowa ya tambaye shi about yesterday night,"
Chapter 87 · 0% Book details