Sashe 58
Abban Sojoji · about 4 min read
"A tafi da twins ɗin nan, akai munsu gidan goggona, asanar da ita cewa zandawo later," Ya ƙare maganar da cewa "asan irin driving ɗin da za'ayi dasu," murmushi kawai major ɗin ke saki, aransa yace "Oga fa yayi kamu da alama, Allah yasa ayi da ran mu" 😇 A fili kuma yace "Consider it done Sir!!" Haka suka tasa ƙeyarsu hosana, waɗannan hot soldiers ɗin suka sasu agaba, har aka fice dasu marshal Omar bai dauke idonsa daga kan yarinyar ba, sai da yaji tashin motocinsu sannan, Haka motocin nan suka fice dasu, daga asibitin, 😊 Police ɗin nan yajima yana mamaki, daga cewa wanene marshal omar sai kawai yaga rundunar sojoji, sojojin ma bana nan ba tab, lallai ba ƙaramin Jan wuya bane, 💪 Murmushi kawai babban likita ke saki wanda ya rage a wurin tsaye, sai lokacin marshal omar ya lura dashi, cikin sauri ya ƙarasa tare da hugging ɗinsa yana cewa "Am sorry ban lura dakai ba wlh," Babban likita yajanye jikinsa tare da cewa "Shege Omar ! Mutanen U.S wlh yau ka bani mamaki, kayi matuƙar burgeni sai naga abun kamar ashirin film, shin wai ma ni dirar yaushe ? dama ka shigo garin kenan ? Ɗan ƙayataccen murmushi marshal omar yasaki tare da cewa "3 weeks kenan da zuwan mu, tare da Captain mu ka taho daga kd shi ya wuce zariya wurinsu ammi ni kuma na wuto nan kai tsaye, tomorrow insha Allah zan juya nima," Ruƙo hannunsa babban likita yayi suka tunkari office ɗinsa, domin samun damar tattaunawa dakyau, sai faman murmushi yake saki, Allah sarki ɗan uwa mai daɗi, yama rasa ina zai sa Marshal Omar saboda tsabar farin ciki, Yana lura da nurses ɗin dake ta faman leƙensa, wato sun ƙyasa koda yake dole ne abunda ya faru ya burge kowa, A office ɗinsa suka zauna, ga sanyin A.c komai tsaf tsaf, suka zauna suna facing juna, "Bari nasa akawo maka abunsha," acewar Babban likita, cikin sauri umar yace "A'a no need" "Wai ni kam ina SGR? wato shi bazai ajiye makaman yaƙin nan ba , yazo ya kawo mana ziyara ba ko"? ɗan murmushi omar yayi tare da cewa "rikicinsa da Ammi ne, kasan tace ita ƴa'ƴan fatima, ba jinin ta bane don haka bata buƙatar, waninsu ya sada zumunci da family ɗinta," . tsoki doctor yaja rai a6ace yace "wannan guyababban jarababbiyar tsohuwar bansan meke damunta ba, ƙiri~ƙiri ki tsani yara grand child ɗinki kuma? inace faɗanta da Aunty fatima ne ba da su ba, haba !!" ya ƙare mgnr cikin ƙunci Omar yace "Abun yana damuna nima, especially yadda take nunawa su junaid tsana batasan su ƙiri-ƙiri, yanzu ni ba wannan ba game da Twins ɗin can,' ya ɗan dakata da maganar, Murmushi big doctor yayi tare da cewa "me kake son sani game dasu"?. "Me ke faruwa dasu ne, kuma wacece bata lafiya acikinsu, sannan ina iyayensu ne "? Omar ya tambaya cike da son jin taƙaitaccen bayani, Gyara zama dr ɗin yayi tare da cewa" ita wadda ta faɗa maka ajikin ka, itace bata da lpy, she has a mental illness har aiki ma an ta6ayi mata, ina ji anan asibitin ne, sannan tana da asthma, bansan dae taƙamaiman labarinsu ba, amma ita ɗayar mai hankalin munyi magana da ita, ta gayamun cewa, basu da kowa a hannun wata tsohuwa suke, so tsohuwarce ta rasu kuma bincike ya nuna cewa poison aka bata, tace mun basu ne suka kashe ta ba, iya abunda nasani kenan," Shiru Omar yayi na ɗan wani lokaci kafin yace "zanyi binci ke akansu amma ba ynx ba, suna buƙatar kulawa ssae, ynx ita mara lafiyar, me take bukata," . "drugs ne kawai dama ake bata, ynx ma already na rubutamusu waɗanda zata yi amfani dashi, sannan suna buƙatar abinci mai gina jiki sosai tabbas, akwai yunwa atattare dasu,' babban likita ya kare jawabin yana kallonsa, Shiru yayi baice komai ba, yana wani tunani, " ynx ya zakayi da twins ɗin naji kace akaisu wurin goggonku," babban likita ya tambaye sa, . Ajiyar zuciya Omar yasaki tare da cewa "as frm now dukkan wani responsibilities ɗinsu ya dawo underneath ɗina ! ban damu da sanin su wanene parent ɗinsu ba ko family ɗinsu, saboda banga kowa atare dasu ba, that means anyi watsi dasu, don haka na mallakawa kaina su !!!!! Wani irin Murnushi babban likita yake saki yana kallonsa, wannan ƙarfin halin da ƙwarin guiwar Omar ba ƙaramin burgeshi su ke yi ba, . Sam bakinsa ya gaza rufuwa don murna cikin tsananin farin ciki yace"haƙiƙa Omar kai na dabanne ko acikin mutane, halin ka na musamman ne, ka cancanci fiye da komai ma, Allah yasa ka maka da mafificin alkhairi, ya ci gaba da ɗaukaka ka, sakamakon wannan ceton da kayi Allah yasa ka maka da gidan Aljanna first step," Murmushi kawai Omar ke saki, shikam babban likita ya gaza rufe baki addu'o'i kawai yake masa, a ƙarshe yashe "Allah yasa su zama Alkhairi agare ka," "Ameen" ya amsa mar,