← Book details Abban Sojoji Local reading mode
READING PART 16 OF 92

Sashe 16

Abban Sojoji · about 8 min read

A 6angaren junaid kuwa, bayan ya tashi daga bacci da jimawa ya wuce masallaci daya dawo ya tsaya a filin da suke buga ball na gidan tare da wasu daga cikin sojojin dake tsaron gidan,
yunwa ce tasa shi shigo wa ciki after magrin prayer, muryasa suka dinga ji yana kiran "tukur ! ,
Wani irin farin ciki ne ya lullu6e sehrish, cikin É—auki ta ajiye wanke wanken da take yi agaban fanfo, na kayan da suka yi amfani dasu,
Karasawa tayi wurinsa yana zaune saman 3 seater, yana daddana wayarsa, cikin girmamawa tace"gani ya ya junaid" ta kirasa da hakanne saboda ya hana ta ce masa yalla6ai, girman jiki ne kawai dashi da kuma tsawo fuskarsa ce kawai zata nuna maka cewa yaro ne sharkaf,
ta6e baki yayi tare da É—an jefa mata kallo ya ce" Æ´unwa nake ji, " ya faÉ—a a shagwa6e, yana kallon ta
cikin zumuÉ—i ta ce " a shirya ma abinci a dining ko nan zan kawo maka,?
ta tambaya tana kallon wayar hannunsa kamar ta fisge ta saboda ita take bukata,
É—an yatsina fuska yayi kafin ya ce" No a tsarin gidan nan bama iya cin abinci in ba tare da junan mu ba, duk yunwar da mutun ke ji dole sai an tattara an haÉ—u a table aci a tare, don haka kawo min coffee kawai, zan jira brothers É—ina su dawo sai mu ci dinner a tare,"
Wannan haɗin kan nasu ya burge sehrish sosai, suna son junansu, juya wa tayi, taje da tadawo hannunta dauke da cup din saman ɗan plate ɗin da ake aza sa, miƙa masa tayi tana kallon fine face ɗinta,
Ƙarba yayi tare da faɗin"thanks"
komawa dining room É—in tayi, tana goggoge chairs É—in dake kewaye dashi, daga inda take tana satar kallonsa shi da yake zaune a falo,
Bayan ta kammala ta koma kitchen ɗin, azmi ta samu tana a ciki tana ganin ta ta ce "yawwa mlm tukur ayi maza a fara jera abincin a dining ko," sunnar da kai ƙasa sehrish tayi cikin jin kunya, azmi tace "gsky hajjaju yar daru ce! da ita duk aka shirya wannan ƙaryar," murmushi kawai sehrish take yi tana wasa da yatsun ta,
Ba tare da bata lokaci ba, suka soma shirya abincin, tana kaiwa tana jera masu,
Ƙiris ya rage a fara kiran sallar magrib, bayan sun girma shiryawa azmi ta wuce ɗakin ta , sehrish kuwa falo ta wuce, anan ta samu Junaid yana sharar bacci, ya mimmiƙe kafafuwansa a saman doguwar kujerar, Alhamdulillah thanks to Allah ta fadi hakan, ƙyalle ido tayi ta ga inda ya ajiye wayarsa saman chest ɗinsa,
Cikin sanɗa ta soma tafiya a hankali a hankali take takawa, har ta idasa isa gabansa, leƙa fuskansa tayi kyakkyawa mai annuri, dimples ɗin nan nasa a lotse, kamar ba bacci yake yi ba,
Hannu takai a hankali ta ɗauki wayar tasa cikin rashin sa'a ta zame daga hannunta ta faɗi kasa ta daki haɗaɗɗen tiles ɗin dake kasa, har cikin zuciyarta taji faɗuwarnan, tsadaddiyar waya irin wannan, dafe ƙirjin ta tayi tana kallon wayon, ƙarar faɗuwar wayar tasa junaid yunkurin buɗe idonsa daga baccin da yake, cikin sauri ta boye bayan hannun kujerar tana sauke ajiyar zuciya, gyara kwanciyarsa yayi ya ci gaba da bacci, jin sakin ajiyar zuciyarsa yasa ta gane ce ya koma baccin nasa, hannu ta zura ta janyo wayar tana kallon screen ɗinta, Alhamdulillah ta fada ganin ba abunda ya same shi,
Yunƙurawa tayi ta tashi tsaye, tana kallon sa, ya aza hannunsa ɗaya a saman stomach ɗinsa, ɗayan kuma a saman kansa, abun yazo mata da sauƙi, don haka cikin sauri ta jona wayar a yatsarsa, nan take wayar ta buɗe,
murmushin jin daÉ—i ta saki, wannan hoton ta sake gani a wallpaper É—insa na wannan haÉ—aÉ—É—en matashin saurayin, har ranta so take tasan wanene wannan sarkin kyawun nan,
Ja da baya tayi a hankali tayi nesa dashi, izuwa gefen stair ta tsaya, contacts dinsa ta shiga ta rubutu numbar goggo, bugu É—aya wayar ta shiga kuma aka É—aga, cikin sa'a muryar jahaad taji tana kwaÉ—a sallama, da farin ciki ta ce"Jahaad ni ce Sehrish! banda isasshen lokaci pls listen to me," a can 6angaren jahad ta natsu tana sauraron abunda sehrish zata ce mata"Nasamu kuÉ—in aikin account number zaki turomin cikin gaggawa saboda na fadamiki wayar ta yaron gidan ce nake dauka shi kansa baisani ba,"
tsananin farin ciki ne yasa jahad yin ihu da fadin Alhamdulillah a cikin wayar tasu, ta ce "narasa inda zansa kaina don farin ciki Æ´ar uwa kice mun kusa barin asibitin nan dama wlh nagaji da zamansa...." sehrish ce ta katse ta ganin zata ja masu lokaci ga tsoran kar junaid ya farka "ke ba surutu zakiyi mun ba ki anso acct number É—in likitan yanzu yanzun nan ki turamin kada fa ki 6ata lokaci asiri na zai tonu,"
Tana gama faɗan hakan ta yi rejecting kiran, ta tsaya nan tana jiran shigowar saƙon jahaad, jikinta har rawa yake gudun kar junaid ya farka, har leƙen sa take yi taga ko yana motsi,
Safa da marwa tashiga yi kamar mai ɗawafi, Allah Allah take jahaad ta turo saƙon tayi sauri ta kwafa ta mayar masa wayarsa,
tana nan tana jira, tajiyo ƙarar shigowar motarsu Ayaan,da wata irin jiniya motocin nasu ke shigowa, aiko nan take junaid ya soma motsi , saboda tsabagen ruɗu 😳, maimakon taje ta ajiye masa wayar ta ruga , sai ta haɗa da wayar duka ta watsa aguje sai bedroom ɗinta.
Ana dara ga dare yayi ?😳
tashi zaune yayi tare da yin miƙe, da hamma lokaci guda hannu yasa ya rufe bakin nasa, wayarsa ya soma lalube yaga bata nan bai kawo komai aransa ba sai yayi tunanin ko ya barta a room dinsa ne,
Shigowarsu brothers ɗin nasa ne yasa shi, sakin fara'a , a jere suka shigo su 7, ƙarasa wa kanal yusif yayi ya russuna tare da rungumesa yace"barka da hutawa my bro ina fata kana cikin koshin lafiya," da fara'a ya amsa masa da cewa "am fine bro kun dawo lpy," kanal ya masa masa da eh, kafin ya wuce, shima khaleed karasawa yayi inda junaid ɗin ke zaune ya rungume sa tare da cewa"My sweet bro ya enjoyment," bai basa amsa ba sai murmushin da yayi masa, haka irfan da jabeer duk suka rungumesa kafin suka wuce ɗakunansu,
Ya rage saura twins da fawan, harara fawan ya sakar masa tare da wuce wa ta gabansa yana rera waka cikin zolaya yake cewa"Lalatacce lalatacce ne ko a gidansu wannan haka yake," É—aure fuska junaid yayi don ya tsani tsokanarsa da fawan ya ke yi,
A tare Ayaan da Jahan (Masoya 😂) suka ƙarasa kowanne ya manna masa kiss a cheeks ɗinsa kafin suma suka wuce ciki,
Shima junaid É—in tashi yayi ya shiga ciki domin É—auro Alwala saboda liman na ta kwaÉ—a kiran sallah,
A bangaren sehrish kuwa, tana nan maƙale da wayar junaid a hannunta, zuciyarta na harbawa, sai zagaye ɗakin take tana faɗin, nashiga ukuna ynx ya zanyi in junaid ya nemi wayarsa ya rasa, in kuma ya ganta a hannuna nasan dukan tsiya zan sha, kuma su kore ki daga aiki ace mun 6arauniya, yanzu ya zanyi ni nasamu na mayar masa da wayarsa wayyo Allah na,
Ƙarar shigowar message ne taji ƙirrrr! da sauri ta duba, account number ne jahad ta turo mata, cikin sauri ta laluba cikin drawer chest, inda ta ajiye diary din da take rubutu acikinsa Wanda tazo dashi , biron da ta saka a tsakiyar littafin ta dauko ta bude page tayi copying numbers ɗin, tana gama wa , ta mayar ciki ta ajiye,
Sannan ta yi hanzarin deleting sakon daga wayar tasa, fitowa tayi daga É—akin tana leken ko akwai mutun, duk basu kai da fito wa,
har tasa hannu zata koma ciki taji alamun mutun, junaid É—in ne ya fito yana naÉ—e hannun rigarsa, da alama masallaci zai wuce,
Ba karamin dadi taji ba, yana fi ce wa, ta lallabawa cikin sauri ta shiga É—akinsa ta ajye masa wayar a saman nightstand,
Fito wa tayi tana sauke ajiyar zuciya, yanzu abunda ya rage mata takai ma azmi acct number É—in,
É—aki ta koma, ta É—auki diary É—in ta yago papern data rubuta numbar, ta fito ta tunkari É—akin azmi, dayake ba nisa yana kusa da nata, wannan ne karo na farko da ta fara shiga É—akin ta,
Sallama tayi, azmi dake zaune saman sallaya ta amsa da "wa'alaikum salam shigo ciki,"
Cikin natsuwa sehrish ta shiga ciki, wuri ta samu ta zauna kusa da ita ta lankwashe kafarta tayi zaman cin tuwo,
Cazbaha take ja, a hannunta É—an murmushi tayi tace"wai malam tukur ne yau a É—akin namu kodai mafarki nake ne? Cikin jin kunyarta sehrish ta É—ukadda kai tana murmushi,
"tabbas kuwa shine to mara ba lale marhaban daga ganin wannan gashin bakin naka akwai magana," dariya ce ta kubce ma sehrish, ta shiga 6a66aka ta,
daga bisa ni ta tsagaita tare da cewa "aunty azmi dama acct number ɗin ne na kawo miki," ta karasa maganar tana miƙa mata paper ɗin, karba azmi tayi tare da fadin"kin tabbata ta likitance? Sehrish ta ɗaga kai tare da cewa "Eh tashi ce,"
"Toh shikenan kije kawai insha Allah zuwa gobe za'a tura masu kudin,"
Azmi ta fada tana adana takardar a saman carpet din.

~ABBAN SOJOJI~

Written by
~HAFSAT BATURE~
~Boss Lady~

Page 20 to 21
Chapter 16 · 0% Book details