Sashe 66
Abban Sojoji · about 4 min read
ya sake shigo wa da ƙarar gaske, Ayaan ne yafarka cikin kasalalliyar murya ta wanda ke cikin shauƙi da jin bacci yace,"babe ur phone is ringing pls get up and pick the call, its disturbing my ears," ya ƙare maganar yana bubbuga ƙafadar Jahan da hannunsa, daker jahan ya buɗe idonsa da su kayi jawur ya kallesa da su kallon so da ƙauna yace "Honey bazaka gane bane, ko yatsana bana ji zan iya motsawa, wata irin kasala nake ji kasan fa mun jima muna yi," lumshe ido Ayaan yayi tare da ƴunƙurawa ya tashi shi, yakai hannu ya ɗauki wayar, jahan na cewa "Yawwa honey duba ka ga wane ɗan takurar ne, ke kira na, natsuwa yayi yana dubawa, cikin tsananin tashin hankali yace "Jahan!!!! wlh Babban yaya ne ke kira !!!" yayi maganar da ƙarfin, Ae tuni Jahan ya miƙe garas jin an ambaci sunan Babban yaya, jiki na rawa yasanya hannu ya karbe wayar dake hannun Ayaan yana kallon sunan da ya bayyana akan screen ɗin wayar," Wani irin kallo jahan ke bin Ayaan dashi cikin kashe murya ta masoya yace "Ayaan ka daina mun irin wannan abun Allah! kamin kowane irin wasa amma banda wannan,' Tuntsirewa da dariya Ayaan yayi yana masa gwalo tare da cewa "Ni zaka cema wae kasala kake ji ko yatsa ba ka iya motsawa, shiyasa namaka wannan wasan," Pillow Jahan ya wawura dake gefensa ya kifa masa a fuska, nan suka shiga wasa da junansu, A ƙarshe suka koma suka kwanta, ba tare da sun bibiyi kiran da ake masu ba, Jahan ne ya kwanta yayin da Ayaan ya kwantar da kansa a ƙirjinsa, shi kuma jahan ɗin yana shafa masa sumar kansa, cikin sanyin murya Ayaan yace "Jahan! anya kana tunanin ranar da asirin mu zai to nu? wane hukunci za'a mana," "Kisa," kaitsaye Jahan ya bashi amsa, cikin tsananin tsoro Ayaan ya janye jikinsa daga na jahan ya tashi zaune saman gadon yana kallonsa a tsorace yace "Jahan dagaske kisa ne? Kashe mu za'ayi,"? Tashi zaune shima Jahan yayi tare da cewa "Am serious Ayaan kai fa mai ilimi ne ! Sarai kasan hukuncin waɗanda ke aikata homo a addinin musulunci,! munsan da hakan kuma muke aikatawa tabbas duk ranar da Babban yaya yasani wlh kashe mu zaiyi bazae ƙyale mu ba, duk son da yake mana hakan bazae hana yaƙiyi mana hukuncin daya dace damuba domin nema mana sauƙi wurin Allah," Wasu irin hawaye ne ke zuba a fuskar Ayaan cikin tsananin tsoro yace "Jahan ni banso na mutu yanzu, banso na mutu ina aikata wannan mummunan zunubin wlh banso, Jahan kullum babban yayanmu yana ja mana kunne akan mu riƙe mutuncin mu, mu ji tsoran Allah mu guji sa6a mashi domin muyi kyakkyawan ƙarshe kuma mu tsira ranar gobe ƙiyama amma meyasa zamu zama na farko da zamu karya masa zuciya duk irin soyayyar da yake nuna mana"? cikin ƙunar rai Ayaan ke maganar yayin da idonsa ke zubar da hawaye masu raɗaɗi, Jikin Jahan ya gama mutuwa shima idon nasa cike tab da hawaye yace "Ayaan yaya zamuyi? bamu da za6i, kaima kasan bada san ranmu muke aikatawa ba, Ayaan....kafi kowa sanin azaba da raɗaɗin da muke sha in har mu ka wuce 24 hours bamu sadu da junanmu ba,' Cikin shesshekar kuka Jahan ke kora masa bayani, cikin sanyin murya ayaan yace "Babban yayan mu yazame mana komai arayuwa, ya sama mana rayuwar farin ciki, kullum yana ja mana kunne akan kar muja masa abun magana a family roƙonsa kenan amma mun gaza cika masa hakan, ko da yaushe dangin abbanmu suna cewa ƴa,ƴan momyn mu basu da kunya fitsararru ne, tabbas sunyi gaskiya tunda gashi nan, bamu tsoron Allah muna aikata zunubi irin wannan,......." . "Ya isa haka !!! Nace ya isa Ayaan , kadaina cewa bamu tsoran Allah, mu bayin Allah ne kuma masu tsananin tsoransa, Allah yana sane damu kuma asannu zai kawo mana ƙarshen matsalarmu, zai warware mana duk wata masifa dake damun mu," Jahan ne yayi wannan bayanin a yayin da ya komar da jikinsa ya kwanta tare da jan bedsheets a lullube jikinsa yana sharar kuka, . Shima ayaan ya kifa kansa jikin pillow yana matsar kwalla, suna masu danasanin rayuwarsu da tazo musu a haka," 😥 'Shin meke damun su TWINS ne ? da son ransu suke aikata hakan ko kuwa akwai wani abu a ƙasa ne? Nifa na rikice ina buƙatar ƙarin haske game da waɗannan bayin Allah,' . 😥