← Book details Abban Sojoji Local reading mode
READING PART 11 OF 92

Sashe 11

Abban Sojoji · about 8 min read

A cikin 2 weeks sehrish ta gama fita hayyacin ta, a tunanin zata huta a wannan katafaren gidan amma ashe ba haka bane, aikinsu Junaid kamar zai kashe ta, ga wani karen tsana da twins dinnan Jahan da Ayaan suka sa mata, yini take tana aiki tun safe har dare basa so suga tana hutawa sunfi so suga tana aiki kamar ansa mata battery, kullum sai azmi ta turata taso su suzo suci kalacin su na safe, haka Zata bi dakin kowannansu daya bayan d'aya, kowa taje tadawa da irin wulakancin da zata kwasa saboda jan kunnanta da suke yi har fatar kunnan tayi jawur, ga gyaran dakunansu, wanke toilet dinsu, gugar kayansu duk ita ke yi, wani lokacin ma idan suka ga babu aiki tana hutu sai su tattaro kayansu dake cikin laundry basket su bata ta wankesu tas, in azmi tace musu ba da injin wanki suke amfani ba dak sai suce ae wankin hannu yafi fidda kaya suyi kyau,

Baiwar Allah lokaci guda ta zama wata zararriya wani sa'in ko bacci take yi sai ta dinga jin muryoyinsu nayi mata gizau a kunnanta suna cewa "tukur tukur tukur kur "

Girki kad'ai azumi ke yi saboda sunce sauran aiyukan bana ta bane na d'an uwansu namiji ne wato tukur mai aikinsu,

Akwai lokacin da suka shigo atare suka same ta, ta kammala goge goge tayi aiki ta gaji, ta samu wuri saman 3 seater ta kwanta tana hutawa asalima batasan bacci ya dauke ta ba,

Kayan wanki suka shiga suka dauko kowa dana sa, bata yi aune ba sai dai taji ana zazzage mata jibgin kaya a jikinta, haka take faman hakuri dasu,

Yau ba ta makara wurin shiga kitchen ba, azumi ta taras tana gyara naman kaji, ba qaramin mamaki azmi ke bata ba sam ba ta gajiya da aiki kamar engine, gashi ta kware a wurin iya sarrafa abinci ta iya girki

"Barka da safiya aunty azmi" ta fada tana kallon ta , da murmushi a fuskarta tace "yawwa mlm tukur ya gajiyar jiya? Sehrish ta ce "Alhamdllh"

"Yau ba a makara ba kenan" azmi ta tambaya, sehrish ta ce "eh"

Zame hannun tayi daga gyaran naman da take yi, can cikin kitchen din tashi ga kofar da store yake ta bude, wasu manyan doyoyi ne ta dauko guda 3 lafiyayyu, tazo ta ajiye a saman table din da suke yanke yanke a saman sa da sauransu, " gasu nan a fere su da kyau in ka gama ka shiga store za ka ga crack din kwai ka debo 20 a cikin roba a farfasa su,"

Amsa wa kawai take da toh, wuka ta dauko ta fara daddatsa doyar , a natse take ferewa , junaid ne ya fado mata a ranta tunaninsa ta soma yi "har yanzu nagaza gane masa ni bansan meyasa ya ke da shagwaba ba kamar karamin yaro gashi da shiga rai uwa uba ga kyau kai dukkansu ma kyawawa ne idan har akace mun na zabi daya cikinsu to tabbas zanyi ruwan ido, amma fa gaskiya junaid na daban ne inason namiji mai shagwaba mai kyakkyawan murmushi domin murmushi alama ce dake nuna cewa mutun nada saukin kai, matsala da shi son jikin tsiya shi a tunaninsa ni namiji ce baijin komai ya rika ruko mun hannu baisan yana sani cikin yanayi ba.

Muryar azmi ce ta katse mata tunanin nata "sai kayi sauri fa tukur naga alamar yau shiririta kake ji,"

Mayar da hankalin ta tayi ta ci gaba da ferar doyar, bayan tagama tayi mata shape, gaban tap taje ta zuba ruwa ta wanke ta tas, ta dawo kan eggs din da cokali ta farfasasu ta dauko Whisk abun ƙaɗawa ta k'ada shi ya haɗe jikinsa, kayan kamshi azmi ta miƙa mata ta karba ta zuzzuba a ciki, bayan tagama ta shiga soya wa da doyar.

A kalla suna yin abinci kusan kala 8 na breakfast hada kayan snacks irinsu bugger, donuts, pancake, soyayyiyar ayaba (plaintain) chips doya da kwai, chicken pper soup, pasta wit stew , coffee , slide bread, gasasshen kifi, fried meat tarkace iri iri ,

Mafi rinjayen aiki azmi ke yi hakan ba karamin taimakon sehrish ta yi ba saboda bakomai ta iya ba,

"Ka je ka fara tado su lokaci karya kure tunda mun kammala da wuri" A cewar azmi da take shisshirya kayan abincin wanda zata je ta jera a dining,

fita sehrish tayi da sauri gaban ta na É—ar É—ar gudun abunda zata taras wurinsu,

Dakin kanal yusif ta fara zuwa, bayan ya bata iznin tashigo, ganin shi daga shi sai short towel a west dinsa ya sa ta yin Æ´an kame Kame da alama daga wanka ya fito duba da yadda ruwa ke É—igÉ—iga daga jikinsa,

Sam ta gaza control É—in kanta har sai da ya juyo ya kalle ta dayake a gaban dressing mirror yake, ganin yadda mai aikin ya zuba masa ido yasa shi jan dogon tsaki tare da cewa "Stupid ! Why are you Looking at me? Ina namiji kana namiji amma kake kallo na anya kai ba É—an iska ba ne?

Sunkuyar da kanta ta yi tare da cewa, "An gama shirya...' Bai bari takarasa ba ya ce "Na ji but this is the last warning da zan yi maka as from today bana bukatar sai an zo an sanar da ni in sauko in ci abinci,"

Cikin girmamawa ta amsa masa da ta toh insha Allah hakan bazai sake faruwa ba, fi ce wa tayi ta wuce dakin khaleed har cikin zuciyarta taji dadin abunda yusif ya ce mata saboda ita hutu ne a gare ta,

Shima khaleed kusan hakance ta faru ya ce baya bukatar ana zuwan masa É—aki da safe haka indai ba shi ya bukata ba,

Wuce wa tayi dakin twins kwankwasa tayi taji shiru ba a bata izinin shiga ba amma kofar a bud'e take, a matsayin ta na me ragaggen hankali sai ta kutsa kai tashi ga kwata kwata babu su a saman gadonsu sai dai wani abu daya tayar mata da hankali, gurnani da wani irin nishi tadinga ji daga cikin toilet dinsu alamun akwai mutun ciki kona ce mutane ciki, tamkar ana sukuwa saman doki yanayin sautin.

Hakan ba karamin firgitar da ita yayi ba sai ranta ya riƙa bata cewa kodai wani ne bai lafiya a cikin toilet ɗin da bukatar tayi sauri taje ta sanarwa azmi abunda ke faruwa, juya wa tayi da sauri zata fita sai taji ana koƙarin buɗe kofan, tsayawa tayi tana kallon kofan toilet ɗin taga ikon Allah, a tare suka fito daga toilet din Ayaan ne ya fara fito wa sai jahan biye a bayansa dukkansu sanye da gajeran towel a ƙugunansu,

Gaba É—aya tabi ta firgita sam basu lura da ita ba don haka ta lallaba ta fice cikin saurin,
Jikin ta a mace take tafiya abubuwa iri iri ne suke zo mata a ranta " dama mutum biyu na shiga toilet a lokaci É—aya, menene dalilinsu nayin hakan? Shin nishin da naji da gurnanin nan na menene ? Allah wa alamu ta tambayi kanta sam ba ta kawo wa ranta wani abu ba amma hakanan take jin tabbas da akwai matsala a tattare da twins din nan.

Bedroom din fawan ta wuce tun kan tashi ga take jin sa yana waya, tsayawa tayi bakin kofan tana saurarinsa "baby nifa bana so a samu matsala bakisan halin yayyen mu ba muddin suka gane cewa ina mu'amala da mata to tabbas sai sun kusa kashe ni,"
Rass taji gabanta ya faÉ—i " mu amala da mata kuma wata irin mu'amala kenan?
Ta jefa wa kanta tambaya zuciyar ce ta bata amsa "duk wata mu'amala da mutun ke gudun a san yanayin ta to tabbas ba mai kyau bace,"

Wani irin miyau ta haÉ—iye lokacin da ta samu amsar tambayarta , sai da ta samu natsuwa sannan ta kwaÉ—'a sallama, jin muryar mai aikin nasu yasa fawan saurin yin rejecting kiran ya yi throwing phone É—in nasa saman gefensa, rai abace yace " wai wanene "

Ko izinin shiga ba ta samu ba, murya na rawa ta ce "tukur ne dama an kammala shirya breakfast ne"

Wani irin dogon tsoki ya ja tare da cewa" Naji sai me"?
Jiki a sanyaye sehrish tabar kofan É—akin nasa ta wuce na irfan, ita kanta ta shaida cewa yau babu sa'a ynx fargabanta me zata taras É—akin sauran.

*_Hafsat Bature_*
~(Boss Lady)~

Page 15-16

Kwankwasa kofar É—akin nasa tayi , da wata irin kakkausar murya taji ya amsa mata da cewa"Uban wanene" kai kanaji kasan yasha ya bugu har takai masa aka.

Saboda tsoro bata basa amsa ba ta yi gaba da sauri, tun a lokacin ta gane cewa tabbas akwai matsala kuma sam bai kamata tana bin kowannan su ɗaki don tayar dasu ba, ta gama yanke shawarar sanarwa azmi cewa baza ta ƙara zuwa ba, tun da cikinsu ne in suna jin yunwa dakansu zasu fito su nema.

Gaba É—aya a firce take da lamarin kan ta ya gama É—aure wa, É—akin Jabeer ta wuce tana sa hannu ta kwankwasa kofa , tana jiyo har mutsinsa ta ciki sallar karya ya kabbara , shiga ciki tayi abun saiya daure mata kai, Sallah karfe 9 na safe.
Har zata juya idon ta ya hango mata kwayoyi na shaye~shaye ga kwalabe kuma a gabansa.

Shi duk a tunaninsa yayansu ne kanal yusif amma jin shiru yasa shi katse sallar ya ɗago ya kalle mai aikin, wani mugun kallo ya wurga mata tare da nuna mata hanyar fita ya ce " karka kuskura ka ƙara zuwan min ɗakina in ba haka ba saina canzama kamanni shashasha,"

Abun da bai sani ba ita sam ba ta san kwayoyin menene a gabansa ba, a tunaninta bai da lafiya ne shine ya ajiye magunguna zai sha.

Ficewa ta yi a ranta tana cewa" Allah ya ba ka hakuri,"

Saura É—akin shagwababben sarkin murmushi, har tsoran zuwa ta ke yi saboda manne mata da yake yi,
Chapter 11 · 0% Book details