← Book details Abban Sojoji Local reading mode
READING PART 53 OF 92

Sashe 53

Abban Sojoji · about 8 min read

Fashewa da dariya yusif yayi, tare da sa wayarsa a saitin mouth É—insa yana karewa, saboda gudun kar babban yayan yakai masa naushi,
"Yi mai Isarka," Babban yayan ya faÉ—i yana shafa damtsen hannunsa da right hand É—insa alamar zaiyi bugu,
yusif yace "Ai ni na wuce bugu ko Abba," ya faÉ—i yana kallon abban nasu wanda shima dariyar ya keyi,
Da ƙarfin gaske babban yaya ya yunƙura zai kaiwa Yusif punch a face ɗinsa, jiki na rawa abbansu ya taso yayi saurin rikosa, duk da yasan wasa ya ke ba bugun nasa zaiyi na, yusif ihu yayi yana faɗin "Abba dont let him punch me,"
Dole yusif ya tsorata, shifa Babban yaya a ƙa'ida ya naushi mutun a cheeks ɗinsa, sai haƙori ya fita 😳
In kuwa yakai ma zazzafan naushi a saitin zuciyarka, sai dae uwar mutun ta haifi wani, bugu ɗaya sai lahira 😳😳😳
Murmushi kawai sehrish ke saki domin komai ke faruwa a idonta, duk da akwai tazara sosai amma tana hangensu ta cikin kitchen ɗin, bakomai ya burgeta ba, fa ce yanayin yadda Sgr ya ƴunƙura ya dunkule hannu zai kaiwa yusif naushi, sumar kansa da ta yarfo ta gefen forehead ɗinsa ba kamin tafiya yayi da ita ba,
"Bari na shirya miki abunsha ki kai musu," muryar azmee ce ta katse ta daga kallon nasu,
É—an zaro ido tayi jin ance zata kai masu abunsha, ga tsoran tunkararsa ga kwaÉ—ayin son ganinsa da take yi,
A tray ta shirya mata cups masu ɗauke da coffee, ta miƙa mata jiki na kerma, sehrish tasa hannu ta kar6a, a hankali take tafiya zuciyarta cike da fargabarsa,
Da sallama ta isa inda su ke, duk suka amsa, miƙa wa abbansu tafara yi, da fara'a fuskarsa yasa hannu ya ɗauki cup ɗin tare da cewa "Yawwa madallah sannu da ƙoƙari," murmushi ɗanyi tare da juyawa wurinsu heart ɗinta na beating, tsoro yasa tafara miƙa wa yusif cikin sauri yusif yayi mata alama da hannunsa tafara miƙawa babban yayan, Saboda ba'ayi masa haka sam, wato afara mika wa nakasa dashi abu kafin a bashi, hakan laifi ne a wurinsa,
Ita kanta batasan tana da irin wannan natsuwar ba, sai da taje gabansa, ji ka ke tsit hatta zuciyarta sai da ta lafa da bugawa cikin sauri, daddaɗan ƙamshin turarensa ne ya gauraye hancinta, zuba mishi ido tayi tana kallonsa,
Idonsa nakan screen ɗin wayarsa, jin alamar mutun ƙiƙam akansa yasa shi ɗan dagowa, tray ɗin hannunta yaci karo dashi,
cire hannu yayi yasa a hankali ya ɗauki cup ɗin, bin hannusa tayi da kallo, wasu irin zira-ziran yatsun hannu, dogaye farare ƙal, ga fatar nan sai ɗaukar idon tsiya, mutun kamar ya lashe, agogon hannunsa tabi da kallo tazauna masa raɗau sai kyalli take,
Mayar da idonta tayi akan sumar kansa mai É—an bala,in kyau sam sehrish tagaza matsawa daga tsayen da take akansa, batasan bayason Kallo ba, a hankali yake kur6arsa a mouth É—insa,
Abun ya daurewa abbansu da kanal yusif kai, ganin yadda mai aikin nasu Ya tsayawa Babban yayan akai kamar sai lashe sa, duk da sun cewa shi abun kallo ne, dole akallesa,
"Miƙo mun mana,' kanal yusif ne yayi maganar don yayi saurin dakatar da mai aikin nasu daga kallon ƙurullan dayake wa Babban yayan nasu, kafin ya fusata,
Lokacin da mgnr kanal yusif ta dira a ears ɗinta, jiki na rawa tadawo hayyacin ta, tare da matsawa ta miƙa masa shima ya ɗauka sannan jiki a matse ta koma kitchen, har ta shiga cikin ƙamshin turarensa ne ke ɗawainiya da ita,
Sam tarasa sukuni, sai faman sauke ajiyar zuciya ta ke, kamar wadda tasha gudu,
Muryar azmee ce ta katseta da cewa "tun da mun kammala, mu bari sai after magrib ayi arranging É—insu a dining,"
Sehrish ta amsa da "Toh aunty azmee,"
tana ganin lokacin da suka kammala firar tasu, su ka kuma fita atare,

........*Junaid*.........................

Da tunanin sehrish ya yini, kasancewar ya fita gidan wani friend É—insa daya jima shima bai lpy, yaje duba sa, a can ya yini yana ta jansa da fira, hakan yasa ya jima, bashi ya dawo gida ba sai wuraren magrib ya shigo da motarsa, zuciyarsa cike da son ganin sehrish É—insa, da murmushi ya shiga ciki, bakowa duk sun je sallah da alama,

Bedroom É—insa ya wuce, cikin sauri ya shiga toilet ya watsa ruwa ya fito, shirt yasanya tare da dogon wando, kullum ya kalli kansa a mirror sai ya furta wannan kalmar wato "Mallakin sehrish,"

(Sai naji dama ni yakewa tanadin kansa da ban bari yasha wahala ba, dama ƙopa a buɗe take musamman ga irinsu Junaid masu kyawun hali) 😅

Jin takon takalminsa yasa sehrish É—agowa, wadda ke tsaye tana ta faman jera abincin a dining, ita ta riga azmee fitowa bayan sun gudanar da sallar la'asar, zuba mishi ido tayi atlease tayi kewarsa sosai don tun safe rabon da tasa shi a idonta,

Shima farin ciki ne ya dabaibayesa ganin muradin ransa, ƙarasawa yayi yaja kujera ya zauna yana kallonta,
Cikin sauri tace "me zan zuba maka,"
"duk abunda yayi miki," kai tsaya ya faÉ—a,
Jim sehrish tayi shiru ta tsaya da jeran da take yi, maimaita maganar da yayi yanzu acikin zuciyarta tayi wato daya ce "duk abunda yayi miki amaimakon yace duk abunda yayi maka tunda amatsayin namiji take,"

É—an É—agowa tayi ta saci kallansa, har ynx idonsa na akanta fuskarnan É—auke da murmushi,

Jiki a sanyaye ta zaro plate haɗaɗɗiyar jallop din taliya ta zuba masa, tare da haɗa masa da Cokali aciki ta miƙa masa,

"Thanks" ya furta tare da soma cin abincin, ganin yana ɗiba da zafinta yasa tace "ka bi a hankali kana ka ƙone,"

É—agowa yayi ya kalle ta da buÉ—en bakinsa sai cewa yayi "kada ki damu zan kula"

daram taji gabanta ya ƙara faɗuwa, yau junaid yasaki layi sai kiranta ya ke da sunan macen ta,

Jin ƙarar dirar motoci ya tabbatar mata da cewa sun dawo, nan da nan taji zuciyarta ta bada wani sound, saboda tasan hada mutumin ta aciki,

Shigowa su kayi atare suna ta faman fira, kamar ba'a tare suke ba,

fawan da khaleed ne suka fara shigo wa tare da su Irfan da jabeer banda su twins,

tayi tunanin shima zai shigo ne amma babu shi, haka abbansu ma, da kanal yusif,

kai tsaye suma suka wuce izuwa dining É—in suka ja kujera kowa ya zauna,

"Sannun ku da dawowa" acewar junaid,

Su ka amsa su duka, cikin sauri sehrish ta shiga yin saving É—insu,

"Ina yaya Ayaan da Jahan su ke, banganku atare ba? Su basu dawo ba ne?

Junaid ne yayi wannan tambayar,
Fawan ne ya basu amsa da cewa "taya muma zamu sani? mun jima da rabuwa dasu, su sukansan inda suka je"

Jabeer yace "ko tsoro basa ji, babban yaya ya neme su, su basusan su kame kansu ba, kamar yadda mukayi,"

"Ka rabu da shaggun jiki magayi," acewar irfan,

~Hafsat bature~ ✍️

Keep sharing 😘*💋💋💋ABBAN SOJOJI💋💋💋*

~🔥the father of soldiers🔥~

_💞Romantic Love story between Hosana& Marshal Omar💞_

*💋HAFSAT BATURE BOSS LADY💋*

*page 69&70* 💋

"Ka rabu da shaggun jiki magayi," acewar irfan,
haka su kayi ta fira suna zuba abinci acikinsu,

Bayan sun kammala sehrish ta kakkwashe dishes É—in da sauransu duka tayi kitchen dasu, har time É—in azmee bata fito ba har sai da ta kammala wanke komai da su kayi amfani dashi sannan tashigo agajiye tana faÉ—in"kin ji shiru ko wlh bacci ne yayi awon gaba dani shiyasa ban fito ba,
"Babu komai aunty azmee kwarama da kika huta sbd kina aikatuwa ssae,"

Azmee tace" hmmmm nasaba ne, bana gajiya da aiki,

shiru su ka É—ayin kafin rishi ta kuma cewa "Su babban yaya basu shigo ba, shi a part É—insa za'a kai masa abincinsa ko anan down ?

murmushi azmee tayi tace " a can ake kai masa amma in yakasance dinner ne, wani time É—in kuwa anan su ke haÉ—uwa suci gaba É—aya, ke zaki kaimasa ?

"Eh zan kai masa,' cikin zumuÉ—i sehrish ta bata amsa,

"Shikenan amma akwai wani abu da zan faÉ—a miki u ave to know it,"

Sehrish ta É—an yi jim kafin tace "menene shi"?.

"Babban yaya fa, baya son kallo sai fa kin kiyaye, because in ana kallonsa yana ji ajikinsa, sannan in ya tambayi abu ko menene kawai ki ce akwai, karki kuskura ya ce yana buƙatar wani abu akawo masa ki ce bamu dashi, ya tsani wannan ki kiyaye ! Sannan baisan kwaratsi ko kaɗan, sannan shi mutun ne mai tsaftar gaske, ko da gigin wasa kada ki kuskura ki bar abun ƙazanta a part ɗinsa ko min ƙanƙantarsa ko da ajikin ki ne, ke ma ki ƙara tsaftarki abisa wadda ki ke yi don daga yanzu ke ce zaki rinƙa kula da part ɗinsa,"

Wani irin daɗi ne ya rufe sehrish, jin cewa itace zata rinƙa kula da part ɗinsa, koba komai zasu samu kusanci da juna, 😇

Azmee ta ci gaba cewa "and then he doesnt repeat words in yayi magana, dole yayi magana aji farat É—aya, sannan in yana bacci ba'a tashin shi, don naushi ya ke kaiwa bana wasa ba......'

Katse ta sehrish tayi da cewa "In time É—in sallah ne fa? Shima ba'a tashin sa? ta tambaya tana kallon azmeen wadda ke daga tsaye,

Azmee tace "Abun ajinin sa ya ke ! muddin lokacin sallah yayi dakansa ya ke farkawa, sometimes kuma alarm ke tashinsa,

Jinjina kai sehrish tayi aranta tace"akwai matsala, Anya kuwa zan iya ? ta tambayi kanta,

Muryar azmee ce ta dawo da ita "zaki iya mana, matukar ki kasa natsuwa,"

Wata tambayar sehrish ta ƙara jefa mata,
"Aunty azmee wai babban yaya É—an wrestling ne?

"Meyasa ki ka tambaya"?

sehrish tace "naga yanayin kirar jikinsa ne, wlh irin ta tasu ce,"

Hmmm azmee tace "shi da ya ke soja, sojan ma bana wasa ba, wanda ya amsa sunansa ae fiye da wresting ma yana yi,"

Murmushi sehrish tasaki Aranta tace "a shirye nake dana zama tamkar baiwarsa wurin yi masa biyayya sau da ƙafa, zan yi komai zan yi iya ƙware wata don naga yasan da zamana acikin gidan nan,
tayi maganar atime É—in da take jera dishes din da takammala wanke wa, a cikin shelves ,
Chapter 53 · 0% Book details