← Book details Abban Sojoji Local reading mode
READING PART 15 OF 92

Sashe 15

Abban Sojoji · about 4 min read

Zube wa kasan tiles É—in tayi tana kuka jikinta har jijjiga yake yi,
Sam bata ji shigowar azmi ba sai dai mutyarta taji ta dirar mata a kunne" Ya sunanki ? ta jefa mata tambaya ,
yunkurawa tayi ta tashi tsaye tana matse hanci ta ce "SEHRISH"
Jinjina kai azmi tayi tare da ƙarasawa inda take, tafin hannunta ta sa tana share mata hawaye, sam sehrish bata yi tunanin hakan ba,
sannan cikin natsuwa ta ce" nayi takaici dana sa wannan kyakkyawar fuskar zubda hawaye am so sad," cike da mamaki sehrish ke kallonta, azmi ta ci gaba da cewa "kiyi hakuri ko kusa bazanso na raba ki da aikin ba! duk da ina tsoran abunda zai biyo baya, amma zan iya jurewa don ganin na taimaka miki," jin wannan bayani yasa sehrish sauke nannauyiyar ajiyar zuciya,
mayar da hannunta tayi a saman shoulders É—inta taci gaba da cewa" da farko ina so ki fadamun dalilin dayasa ki kayi basaja a matsayin namiji"?
Muryar na rawa ta soma magana cikin sheashekar kuka" ƴan uwana ne basu da lafiya rai hannun Allah an kwantar dasu asibiti, kuma doctor ya ce aiki za'a yi musu, shine nake kokari naga nasamu ƙudi na biya musu, ɗayar ma dr yace in har ya wuce 5 ga watan da zamu shiga sai dai a fidda ita Qasar waje ko tarasa ranta.....' kukan ne yaci ƙarfin ta,
Cikin lallashi azmi ta ce "daina kuka ya isa haka, na fuskanci matsalarki, duk da ina buƙatar bayani amma bani da enough time, riƙe wannan zamuyi magana an jima yanzu dai taimakon da zan miki shine, zaki ci gaba da aiki a matsayin Namiji kamar yadda kike yi, ko da gigin wasa karki bari su gane cewa ke maca ce ! sannan maganar kuɗi kuma nawa ne ake bukata ?
Azmi ta tambaya tana kallon ta, sehrish ta ce "dubu ɗari tara ne" a tunanin ta azmi zatayi shock in taji kuɗin amma sai taji tace"zan iya ansar miki albashinki na wata na shekara ɗaya da rabi ! a baki a ɗunkule amma inaso ki sani ! duk runtsi duk wuya duk kuma duk irin wahalar da zaki fuskarta da wulaƙanci a wurin masu gidan nan, dole kiyi haƙuri ki jure! kiyi musu biyayya sau da ƙafa, ba maganar barin aiki , in kuma har kika ce zaki bari toh sai fa kin biya sauran kuɗin da kika ƙarba kin amince!!? 😰
taji ma tana nazari kafin tace"Eh na amince !!! zuciyarta na wani irin bugawa ba kowa ya faÉ—o mata a rai ba face Ayaan da jahaan , ynx ana nufin ta É—aura aure da kaddararta na zama cikin gidan nan! ya ilahi,
"Yanzu account number zaki bani na wanda za'a turawa kuɗin aikin nasu," azmi ta faɗa tana kallon cikin idonta, tsananin farin ciki ta gani a fuskar sehrish 😇
cikin jin daɗi tace "babu a wuri na amma zuwa anjima ko gobe zan samu na kawo miki," azmi ta amsa da toh sannan ta kama hanyar fita har takai bakin kofa xata buɗe ta juya ta kalli sehrish dake ta faman sakin murmushi tace "kada ki manta ynx kina ƙarƙashin Iko na! komai zakiyi saida umarnina, idan har kika saba hakan, hmmmm,
bata ida ba ta fi ce,
sam sehrish bata damu da hakan ba, ita dai indai akan sisters É—inta ne toh ko fiye da hakan ma zata iya jurewa,
Jiki na rawa baiwar Allah ta shige toilet ta dauro alwala taci gaba da zabga nafilfilin miƙa godiya wa ubangijin mu Allah subhanahu wata'ala,
Matsalar su husanna tazo ƙarshe, sauran damuwa ta kau, shin yaya kke tunanin rayuwar sehrish zata kasance a gidan ABBAN SOJOJI ? 😢
yinin ranar da fara'a a fuskarta hakoranta a washe kamar mai tallar maclean, cikin jin daÉ—i suka gudanar da aiki a kitchen tare da azmi don shirya dinner,
tunanin yadda zata sake ɗaukar wayar junaid takira husanna ta ce su turo mata account number, har zuciyarta take jin ƙaunar azmi saboda tayi mata rana ! Har abada kuwa ji take bazata taba sa6a mata ba! tayiwa kanta alkwarin zatayi mata biyayya bazata taba bijire mata ba ko taci amanarta ba,
Chapter 15 · 0% Book details