← Book details Abban Sojoji Local reading mode
READING PART 72 OF 92

Sashe 72

Abban Sojoji · about 6 min read

yana sauke ajiyar zuciya bakomai idonsa ke marmarin gani ba face wannan Zararriyar yarinyar da ta faɗa masa a chest ɗinsa da ita ya yini a zuciyar shi, Ba shi kaɗae bane tare da Babban likita suka dawo gidan, saboda dama nan ne makwancinsa, Bayan sun shiga cikin main palor ɗin agajiye babban likita ya wuce side ɗinsa, yayin da Marshal Omar ya samu wuri saman 2 seater, Shigowa major ɗin nan yayi hannunsa ɗauke da laptop ɗinsa ya miƙa masa, Kar6a Omar yayi tare da furta "thanks," sannan major ɗin ya sara masa kafin ya fice, Tsit bakowa sai shikadae a falon, aza laptop ɗin yyi saman table ɗin dake a gabansa sannan ya zaro wayarsa daga trouser pocket ɗinsa, Zubawa wayar ido yayi yana tunanin wa zai kira ma domin a kira msa yaran yana son ganinsu kafin ya kwanta, bai son kiran goggon katsina don yasan halinta da rigima, gashi bai da numbar saude Zama.yayi shiru yana tunanin mafita, kamar daga sama sai ga jahad ta fito cikin sanɗa ashe batayi bacci ba komai ya fito da ita Oho, "Ke zo nan," Daram !! Taji gabanta ya faɗi rass jin muryar mutumin nan tsaya wa tayi a hankali tana kallonsa, Kafin ta tunkaresa zuciyarta na ɗar ɗar ta samu wuri ƙasa tazauna tare da lankwashe ƙafa ta gashe shi "Ina wuni," Bai amsa mata wannan ba sai ce mata yayi "where's your sister"? Jahad tace "Bacci take yi," "Je ki tasarmun ita, ina son ganinta," Mamaki ne ya kama jahad alamu sun nuna cewa marshal Omar fa yana iya banbance su tunda gashi ya nemi ta kira masa yar uwarta wato wadda ta faɗa masa ajikinsa, Kallo guda yayiwa jahad ya gane cewa ba ita bace wadda ta faɗa masa a ƙirjinsa ba, kaji masu aiki da kwakwalwa, farat ɗaya ya karanci wani abu a tsakaninsu daga ɗazu a asibiti zuwa yanzu, tashi jahad tayi cikin sauri ta shiga ɗakin kamar yadda tabar hosana haka ta same ta kwance a tsakiyar gadon ta lumbutse abunta, baki wangame sai sharar bacci take.tana hura hanci kamar SA, ɗan bubbugata Jahad tayi tare da cewa "Hosana !! Hosana ki tashi," Tsoki taja tare da juya mata baya "Leave me alone," a ƙule jahad tace "wai baxaki tashi ba," "Eh baxan tashi ba, in kinji haushi ki ɗauke ni mana," murmushi jahad tayi tare da cewa " to shikenan bari naje na ce masa kince baki zuwa," jin abunda jahad tace yasa ta yin wani irin juyi ta ƴunƙura cike da zumuɗi tace "Wa,? ƴar dariya Jahad tayi tare da cewa"mutuminki mai ƙarfi," 💪 Wani irin farin ciki ne ya bayyana a fuskar hosana, tasowa tayi daga saman gadon tana gaggyara rigar jikinta, hannu tasa ta ɗauki mayafinta dake anan saman gadon ta yafa, Sannan suka fito atare ita da jahad ɗin, ƙarasawa su kayi gabansa riƙe da hannun junansu, ɗagowa Omar yayi ya kallesu atare ya sauke idonsa kan Hosana wadda ke ta faman zabga mishi murmushi kamar gonar auduga, "Have a seat," ya umarce su Zama su kayi saman 2 seater ɗin dake facing ɗinshi, "What's Ur names,'? Ya tambaya yana ci gaba da danna laptop ɗinsa, Cike da zumuɗi hosana tace "Ni sunana Hosana ita kuma sunan ta Jahad," Jinjina kai Omar yayi kafin ya kuma cewa "Wacece mai ta6in hankali acikin ku,"? Ya tambaya tamkar bai gane ta ba, Cikin sauri hosana tace "Ni ce,' Murmushi kawai jahad ke yi shiriritar hosana nabata headache, "Au kece kenan,? Ya tambaya yana ɗan kallonta, Hosana tace "Eh nice bani da hankali but not always ynx ina cikin hankali na, ɗan ta6e lips ɗinsa yayi kafin ya kuma cewa "Ina iyayen ku suke,"? Shiru sukayi saboda sun rasa amsar da zasu bashi sai can hosana tace "Bamu da kowa, bamu son kowa ba, mu kawai muke rayuwarmu....' tunkan taƙarasa ya dakatar da ita tayi shiru , ci gaba da danna laptop ɗin dake gabansa yayi kusan 15 mins bai sake cewa komai ba sai dai ya ɗan ɗago da idonsa ya kalle su ya mayar, "A matsayin me zaku ɗauke "? ya tambaya yana kallonsu har haɗa baki sukeyi wurin cewa "Yayanmu,' Jinjina kansa yayi tare da cewa "Good, as frm now na zama yayanku, a shirye nake dana ɗauki dukkan wata ɗawainiya taku daga yanzu kun dawo ƙarƙashin kulawa ta, komai kke so just feel free ku sanar mun ko wani abu na damunku haka, sa'annan ku shirya tafiya gobe domin ba'a nan zaku zauna ba, zan mayar daku kaduna state gidan ƴaƴana, zaku samu kulawa sosae acan, Har haɗa baki suke yi wurin yi masa godiya, "No bana son wannan, bana son ana min gdy, zaku iya tafiya gobe ku tashi da shirin tafiya, Miƙewa su kayi atare har sun ɗanyi nisa sai kuma suka juyo suna kallon shi atare suka haɗa baki wurin cewa "Sai Allah ya kaimu yaya Omar," Ba ƙaramin daɗin sunan yaji ba, jinjina musu kai kawai yayi sannan suka shige, shima tashi yayi ya wuce can cikin part ɗin big doctor domin dama acan suke kwana in sun zo," "Hosana ya kika ji muryar mutumin nan na ɗazu wanda goggon nan ta bamu mu gaisa dashi a matsayin mahaifin mu? Jahad ce tayi wa hosana wannan tambayar ayayin da suke kwance su biyu saman gadon suna fuskantar junansu, "A time ɗin naji shine tamkar mahaifina Jahad banso ya kashe mun waya ba kuma yace zai kira da anjima amma bai kira ba," Ajiyar zuciya jahad tasaki kafin tace "Nima haka Hosana, tun da naji voice ɗinshi naji zuciyata ta karye, shiyasanya na miƙa miki wayar sbd kukan da yazo mun," Hosana tace "dama ace shine mahaifinmu ko? jahad tace "how that can be possible, we already ave our own father hosana, so stop expecting that pls," Shiru hosana tayi suka zuba ma juna ido na wani lokaci kafin Jahad tace "Allah Sarki Sehrish nayi kewarta sosae kullum tunani ya rayuwarta take, yaushe zamu sake sanyata a idonmu duk in na tuna hakan sai naji tsananin ƙunci da baƙin ciki araina, sehrish tasha wahala akan mu, tayi mana irin sadaukarwar da uwa ke yiwa ƴa'ƴanta, duk da kasancewar ko a wurin haihuwarmu Oumma ta faɗamin cewa sai da muka fara zuwa duniya da minti 30 sannan sehrish ta fito Allah sarki mai kyakkyawar zuciya insha Allah rayuwarki zatayi kyau Sehrish no matter what the situation is I wll neva stop praying 4 u, ta daka da maganar a yayin da hawaye ke zubo mata daga eyes ɗinta izuwa saman pillow ɗin da take kwance, Jikin hosana ne yayi mugun sanyi itama murya akarye tace "duk nice Sila jahad da ace ban jefa wayar nan ba, da yanzu muna nan muna waya da ita har ma yaya Omar yakaimu wurinta........' Kuka ne yaci ƙarfinta har ta kasa ƙarasa maganar da take yi, "Oumma ta faɗa min cewa mu ba ƴan uku bane ta haifa, amma Abba ya kwashe sauran ya siyar dasu saboda shegen son kuɗinsa, narasa wani irin uba ne shi ya azabtar da rayuwar mahaifiyarmu da kuma rayuwarmu Allah ya isa bazamu ta6a yafe mishi ba har abada.......... cikin kuka take magana itama hosanar kukan take yi domin komai ya faru arayuwarsu in suka tuna sai zuciyarsu ta karaya, mummunan Labari mara daɗin Ji Matsawa su kayi jikin juna suka rungume junansu suna ta faman shesshekar kuka Allah sarki kowa da irin tasa kaddarar, 😥 ___________________________________________Hafsat Bature Moh'd
Chapter 72 · 0% Book details