← Book details Abban Sojoji Local reading mode
READING PART 89 OF 92

Sashe 89

Abban Sojoji · about 6 min read

Jiki a mace jahad ta zauna yaraff !! agefen hosana tana cewa "babu ma hanyar da zamu gudu wlh na tuna sojoji ne ke tsaron gidan Ya Salam ya zamuyi yanzu,
Itama hosanar tashi tayi zaunen ido luhu luhu ga jirwayen hawaye a kumatunta sun galabaita sosai,
"Jahad meyasa har yanzu mutuwa bata zo ta É—auke mu ba? Jiran me take yi ne?
"Hosana lokacin mu ne baiyi ba, kuma ni bana so in mutu ynx, Ina so naga Sehrish........ta ƙarasa maganar tana shesshekar kuka,
"Nima inaso naganta jahad, amma kina tunanin zamu ƙara ganinta a rayuwarmu ? Yaushe zamu isa gare ta ? tayi maganar tana kallon jahad gaba ɗaya hawaye sun zuzzubo musu
"Nima bansani ba.....bansan yaushe ba, jahad ta bata amsa,
. shiru su kayi zugudun ba mai magana,

A dai dai time ɗin motarsu Aunty babba ta shigo gidan Ash colour ƙirar vibe, hafsat ce ke driving ɗin yayin da aunty babba ke gefenta, sai fira suke suna kwasar dariya,
"Gsky mommy da abun dariya kke, amma kinsa me mom? Yaran nan fa sun ga samu sun ga rashi Allah, kalli fa uban kayan da mu kayi purchasing kai kace na Amarya ne,'
Dariya aunty babba tayi tana cewa"Hmmm ke dae bari, ae baki sani ba da ace Abuja direct Omar yakai yaran nan wlh ba ƙaramin gata zasu samu ba, kinsan Abba da son ƴa'ƴa gashi kuma bai da ya'ya mata toh Allah ina faɗa maki Omar nakai yaran nan can gida, Da mun shiga uku, zasu zo su samu matsayin da mu bamu samu bama,'
"Gsky ne Mommy, muna nan sake da baki sai dae muji sun aure yaya Omar da Babban Yaya,
"Ae wlh dana binne su da ransu" acewar aunty babba,
Fashewa su kayi dariya, yayin da Hafsat tayi parking motar a parking space É—insu,
Atare suka fito gowns É—in É—azune ajikinsu sai mayafi da suka yayyafa a kawunansu,
BuÉ—e boot hafsat tayi tana sauko da wasu jigunannun akwatina kamar na lefe, manyan gaske guda biyu launinsu maroon colour, sai É—an kit,
Cikin sauri wani sergeant ya ƙaraso yana musu sannu da zuwa, sannan ya karbi akwatinan don yashigar musu dashi ciki,
A palor ya ajiye masu akwati nan, sannan ya fuce, su kuma suka shigo hafsat na cewa "Mom ni zan shiga ciki na watsa ruwa, kuma yunwa nake ji,
aunty babba tace "kai daughter harfa restaurant muka biya duk abunda kika ci, bai ishe ki ba? to Allah ba girkin da zan É—aura, don agajiye nike nima,'' ta faÉ—i tana wuce Upstairs,
ta6e baki hafsat tayi tare da wuce wa nata room É—in dake anan down,

Bayan aunty babba ta shiga, rage kayan jikinta tayi sannan ta shiga toilet tayo wanka, tafito É—aure da towel, closet É—inta ta buÉ—e ta É—auko wata rigar kuma doguwa tasanya mara nauyi, tunkan ta idasa sanya rigar Wayarta dake acikin purse É—inta take faman ringing,
Cikin sauri ta idasa zura hannun rigar ta ƙarasa inda purse ɗin take saman gado inda tayi throwing ɗinta time ɗin da tashigo,
Zama tayi saman gadon sannan ta sanya hannu ta É—auki purse É—in ta buÉ—e , kuÉ—aÉ—e ne aciki sabbi fal Bugun abuja, sauran wanda suka ciro a banki ne na siyayyar da sukayi,
Wayar ta ciro ta duba mai kiran nata sunan *AMANI* ne ya bayanna akan screen É—in,
Murmushi tasaki domin dama tun jiya take son kiranta,
É—agawa tayi tare da karawa a kunnanta tana faÉ—in " Dama tun jira nake son na kira ki abubuwa sun min yawa,'
On the other hand , Amani tace "Aunty laila kenan kin manta ni kin share ni,'
Aunty babba tace "Ke dallah ba dole in manta ki ba, ke bakisan me ya faru ba, akwai labari zazzafa
Cikin zumuÉ—i amani tace "Bani nasha, am so eager to hear it,
Dariya aunty babba tayi tace "Idan ma a tsaye kike to ki zauna,"
Amani dake a tsaye gaban mirror, taja kujerar dake gabanta ta zauna tana faÉ—in "Na zauna Auntyna, Ina sauraron ki '
Nan aunty babba ta zayyana mata komai game da su Hosana da jahad da Omar ya kawo mata hada kuÉ—in da suka kar6a a wurinsa da purchasing É—in da su kayi masu kaf ta faÉ—a mata,'
Shiru Amani tayi jikinta yayi mugun sanyi, muguntar aunty babba ta razanata, bakomai ya tsaya mata arai ba, face da tace Yaran suna acikin store tun jiya ba abinci, tuni idonta sun ciko da kwalla saboda ita takasance mai tausayi ce sosai, aranta tana cewa meyasa Omar bai kawosu nan ba tabbas ya aikata babban kuskure domin kuwa tasan tabbas Aunty babba bazata ƙyale yaran nan ba, azabtar dasu zatayi............
Sam ta manta waya suke har sai da muryar aunty babba ta ratsa ta da cewa "Kinyi shiru baki ce komai ba....?
Cikin sauri Amani tace "Ae daɗi ne ya hanani yin magana Auntyna, gsky naji daɗin labarin nan da kika bani kamar kamar me, kin ga yanzu wuƙa da nama suna hannin ki sai yadda kika so zakiyi da yaran, domin kuwa matsala ne a target ɗinmu, babban ma abun burgewar ta kuɗin da kika samu a wurinsa kin ga mun fara samun na ziyartar wurin bokan..........'
murmushi aunty babba tasaki tare da cewa "aikuwa dae kuÉ—i fa sun fara samuwa, yanzu dae shawararki nake nema akan yaran nifa bazan bari sukai labari ba!
Shiru amani tayi tana sauraranta aranta tace "baƙar muguwa, in sun tashi kai labarin ki hana su mu gani, mtssw haɗamammiyar banza,'
A fili kuma tace "Auntyna kinsan me?
"A'a saikin faÉ—a" acewar aunty babba,
Amani tace "shawarar da zan baki shine, kada kice zakiyiwa yaran horon yunwa sam wannan bai ma taso ba, saboda kinsan Marshal Omar mutunne mai kaifin basira, wlh muddin yazo kallo guda zaiyi masu ya gane cewa akwai yunwa ajikinsu kuma zai tuhume ki akan hakan, sannan muddin kina so target ɗinmu ya tafi yarda muke so dole fa atlease ki jure ki ɗan basu kulawa ina nufin Kayan da kika ce anyi musu siyayyarsu arinƙa basu suna sanyawa, sannan ki rinƙa barinsu suna yin wanka ko sunyi haske...............
dakatar da ita Aunty babba tayi tare da cewa "Amani me kke Nufi? Ni zan basu kulawa har haka, Allah yakiyaye wlh, ke nifa natsani yaran tun da nagansu, saboda raina nabani cewa nan gaba sune zasuyi sanadiyar tarwatsa mun plan É—ina,"
Cikin lallami Amani tace "Aunty na lura baki fahimce ni ba !! Abun da nake ji maki tsoro shine Omar zai iya yin zuwan bazata nan kaduna, kwatsam ya faÉ—o What will u do?
Ajiyar zuciya amani tasaki ta wani 6angaren maganar Amani gaskiya ce don haka tace "Shikenan zan duba nagani, amma fa Allah saina sa an zubar da twins É—in can,'
"Dama wannan ae Wajibun ne Auntyna," acewar Amani acikin zuciyarta kuma tace "Muguwa in Allah ya yarda bazaki ta6a cin nasara akan hakan ba,'
Sun jima suna fira kafin daga bisani su kayi sallama da juna,"

Bayan amani ta ajiye wayarta ta asaman mirror É—in gabanta,

tace" dama ni Omar ya kawowa twins É—in tabbas da sun samu kulawa, iya kaci kuÉ—ine nima zan kwasa, tunda nima Lashe Money ce,
Ta miƙe tana Zagaye acikin ɗakin ta wani 6angaren taji daɗin ɗaukar shawararta da Aunty Laila tayi koba komai Yaran zasu samu salama, dama wayau tayi mata don ta taimaki yaran da taji tace tun jiya suke acikin store garƙame, haƙiƙa ta tausaya musu,
_______________________________________
Chapter 89 · 0% Book details