← Book details Sihirin Kauna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 32

Sashe 29

Sihirin Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 10 min read

Shafi Na 29
Na INDO CE..
ELEGANT ONLINE WRITER'S
(Kyauta ne
Bismillahirrahmanirrahim
Ina mata yan kwalisa , mata masu aji ,KASAITATTUN mata masu malakan zuciyan me gida kuzo ga Ummu Abdullah tazo muku da mayikan gyara jiki, kala kala, da sabulai na gyaran jiki, da turarrekan wuta da na jiki Dana kaya da na tsuguno,da humra kala kala da shi'umar humra, da kayan chemical,irin su liquid soap, perfume,air freshener,, Hair cream,Shampoo etc tana kuyawa tana hada kaya ,domin Neman Karin bayani Sai ku tuntibi wannan lambar 07046858716
Mutane na
NADAWO
Tunowa da yayi cewarta zataje masarauta ta duba Mariama yasa ya mi
e zumbur yana cewa, "kenan can ta tafi duk da nace kar taje??"
nazari ya
anyi kafin yace, "anya kuwa? banajin hakane gaskiya akwai dai abunda yafaru, amma nakasa fahimtar komai su Ayiya dai sunce basuga fitar ta ba, anya kuwa ba sune sukai mata wani abun ba?"
Tambayoyi yai ta jerowa kansa sai dai yarasa amsar su, duk ya shiga damuwa ga tarin tunane tunane.
Yarinya ce ta dafa shi tareda cewa, "Shikenan Yaaye Yaya Minoji bazata dawo ba?"
Da sauri ya
ago ya zuba mata ido tareda cewa, "bangane ba ina ta tafi?"
Tsaf Yarinya ta bashi labarin duk abunda taji da wanda tagani tanayi tana kuka.
Tsabar ka
uwar da yayi ko motsawa yakasa yi sai ido kawai yake bin Yarinya dashi har tagama ro
onsa akan yadawo da Minoji tagaji ta fita daga
akin.
numfashi yaja tareda shafar kansa wanda yake juyawa tareda wani mugun ciwo, wasu zafafan hawaye ne suka fara shararowa kan fuskarsa duk da yana goge su amma sun
i tsayawa.
Minoji. da yamma li
is goshin magriba can wani sur
i ta tsinci kanta wanda ko a mafarki batasan gurin ba, firgigit ta farka daga dogon baccin da tayi ta shiga kalle kalle a wajen, idan ba bishuyu da tsuntsaye ba babu abunda take iya gani babu mutane a kusa bare gidajen su, da kyar ta lalla
a ta mi
e tsaye tana
ara
arewa wajen kallo, sai da tagama nazartar ko ina sannan tafara tafiya agalabaice tana tafe tana ha
a hanya har ta iso bakin wata babbar hanya lokacin tini duhun dare ya rufa ko ganin hanyar batayi sosai kawai tafiyar take, bata lura da cewar babbar hanya bace bare tayi tunanin wani abun kawai ta afka da mufin
etarawa ta cigaba da tafiya.
sam be ankara da ita ba har sai da ya buge ta tayi
ara.
an razane ya fito daga motar kafin ya iso inda take tini ta gangara gefe, "Subhanallah" ya furta sannan ya
arasa inda take yana haskawa da fitilar wayarsa,
are mata kallo yayi kafin yace, " gashi dai mace ce kuma da alamun ba mahaukaciya bace sai dai babu hijab ko gyale ajikinta ita kuwa wannan lafiya ce ta fito da ita?? karfa naje na
aukarwa kaina aljana, anya kuwa ba tafiya ta zanyi ba?naga koda na buge ta bataji ciyo ba kuma ba wanda ya ganni da na
aukarwa kaina ai gwara kawai na gudu"
Ido ya zuba mata cikin ransa yanata shawarwarin yadda zeyi da ita, dur
usawa yayi yace, "baiwar Allah Baiwar Allah?? jin shiru yasa yace kodai ta suma ne? gata kyakyawa kodai rabona ce? kai sai fa na tafi da ita duk wadda za'ai ayi"
Rintso ido yayi sannan ya kinkimeta ya nufi mota da ita.
Koda ya isa kuwa yayi sa'a Ziyada bata kusa dan haka ya kaita
akinsa ya kontar, babu aikin da yake sai kallonta duk da tayi wujiga wujiga hakan be hanashi ganin kyawunta ba, ruwa ya
ebo ya yayyafa mata dan ta farfa
bu
e idonta da ya canja launi tayi ta
an kalleshi sannan ta
ara rufesu tareda sake salon konciyarta ta cigaba da baccinta cikin kwanciyar hankali.
sakin baki yayi yana kallonta kafin yace, "wai dama bacci take? to kodai ban buge ta ba ma?"
Yana zaune yana sa
a da warwara Ziyada ta shigo
akin kanta tsaye batareda yasan ta shigo ba.
Ganin mace akan gadonsa yasa taja burki tareda cewa, "har yanzu baka dena ba kenan?? wannan wace irin rayuwa ce Usman?"
Fashewa tayi da kuka tana cewa, "ka fitar min da ita daga gidana ko in tara maka idon duniya yanzun nan wallahi nagaji da halinka Usman mayaudari macuci mazinaci Allah ya isa tsakani na dakai, wallahi ko ka koreta ko kuma nai mata shegen duka"
Usman yace, "haba Ziyada wace irin mummunar magana ce wannan ki saurare ni mana bafa yadda kike tunani bane"
Tace, "ba abunda zaka gaya min na yarda wallahi ha
uri na ya
are"
Tsaki yayi tareda cewa, "sai kiyi ai nace ki saurare ni kin
i me kuma zan miki? sai kiyi yadda kike so"
Ruwan da ya ajiye ta
auka ta watsawa Minoji sannan tayi kanta zata fara jibgarta, "Umar!!!!! ka temake ni kar su cutar dani wallahi banyi musu komai ba"
Minoji ta fa
a lokacin da ta farka daga baccin hakan yasa duk sukai sororo Minoji kuwa tana bu
e ido ta sake tabbatarwa kanta Umar
inta ne dan haka tayi saurin rungumeshi tana kuka tareda cewa, "Yaaye ka dawo?? dan Allah mu gudu daga gidan nan idan ba haka ba kashe ni zasuyi"
Kallon kallo Usman da Ziyada sukai kafin Ziyada tace, "ke dakata banason barikanci ya zaki zo kina rungumar min miji tsabar rashin kunya? ina ruwana dan an kashe ki? kije ki nemi Umar
in acan dan wannan mijina ne"
Cikin kuka tace, "
arya ne ni ka
aice matarsa bayan ni bashida wata Yaaye ka gaya mata dan Allah"
A tsawace Ziyada tace, "mayen mata kawai ba kuma zaka saketa ba? wannan ma inaga mahaukaciya ka
akko garin tsinannen neman mata"
Kafin ya janye ta daga jikinsa tayi zumbur ta tashi ta dire daga kan gadon tana karka
e jikinta gami da yatsine fiska.
Da mamaki Usman yace, "oo ga wadda aka buge da mota ta tashi tangaras kamar ma ba itace take kuka ba"
Minoji ta murmusa sannan tace, "kuyi ha
uri fa
ar uwa kiyi ha
uri a rashin sani ne ta
afe jikin mijinki tayi tunanin mijinta ne, Usman ita
in matar
anin ka Umar ce kuma kuna kama da juna ita
in kuma ba'a haiyacinta take ba batada lafiya"
Rasssss rassss gabansa ya shiga fa
uwa kansa yafara juyawa.
Ziyada tace, "wannan wasan kwaikwayon naki yayi ma
aryaciya karuwar banza"
Baya Minoji tayi ta fa
a jikin bango tareda rintse idonta har na
an wani lokaci kafin tace, "ina kikaje? meke faruwa? naga kina cikin damuwa"
Mariama tace, "
warai kuwa abu da dama sun faru nisan da nayi ne yasa akayi miki wannan cin zarafin kuma Yarima ne silar komai"
Sai kuma tafashe da kuka,
Hankali tashe Minoji tace , "me yai miki har yasaki kuka Sarauniya?"
Kamar bazata magantu ba sai kuma tace, "Yarima ya illata rayuwata ya rabani da mutunci da darajata ya keta min haddi na"
Kamar saukar aradu haka Minoji taji maganar da sauri ta girgiza kai gami da cewa, "a'ah meyesa? meyesa zeyi miki haka?"
Tace, "Yarima yayi mugun Alwashi akaina hakan ya
udure tin ba yau ba kuma ya aiwatar, yanada muradin rabani da mulki na kuma yana son tozarta ni a idon duniya kuma yayi nasara, ina hukunta duk wanda ya aikata hakan kuma shima dole hukunci yarataya akansa, nayi masa
aurin da be isa ya ku
uta ba na
aure shi a inda ba wanda ze iya gane inda yake koda Sarauniya Bilkisu da kanta zan cigaba da azabtar dashi har
arshen rayuwarsa baze
ara ganin idon rana ba acan ze mutu a
ashin u
uba ta"
A tsawace Minoji tace, " ya isa Mariama!!!! kin haukace ne???? idan ya aikata hukunci daidai da na
an kowa zaki masa bawai hukuncin son rai ba dan kawai kin tsane shi, kije kiyi tunani Mariama agani na ba da gaiya Yarima yai miki hakan ba yanada dalili kuma kiyi bincike zaki gane"
Mariama tace, "
arya ce Minoji bashida wani dalili wanda ya wuce wannan kuma ze
ana ku
ar sa, karki
ara fusata ni"
Minoji tace, "ya zama dole na gaya miki....."
Kasa
arasa maganar tayi saboda dakatar da ita da Mariama tayi.
Su Anti Ziyada kuwa tini an la
e abayan Usman sai rawar jiki take ganin al'amarin yafi
arfinta, shima Usman
arfin hali yayi kawai ya zubawa sarautar Allah ido yanayi yana
an addu'o'in sa.
Minoji ta kallesu tace, "kuyi ha
uri fa Minoji ta sa ina
aga muku murya kuma ta katse mun hanzari akan maganata, ina magana ne akan
an uwanka da ya ya da
e yana tsumayin ka yanzu zaka iya tuna shi???, ka tuna cewar kana da mata Sumayya wadda kuke kira YaaYa da
arka Kadija Yarinya, sunan mahaifiyarka Jamila kuna kiranta Ayiya
anin ka Umar kuna kiransa Yaaye sai autar ku Hafsa kuna kiranta Yayyi, yanzu ka tina da hakan?"
Ziyada tace, "ban fahimta ba fa wannan wace irin magana ce? Yanada mata fa harda
a kikace?"
Minoji tace, "idan ya dawo haiyacinsa ze gazgata miki zan gaya masa inda
an uwansa suke idan yana bu
ata"
Kafin Ziyada tace wani abu Usman yace, "ina mahaifiyata take?? na tafi nabarsu bansan halin da suke ciki ba, wane irin hali nafa
a haka??, Baiwar Allah ki temaka min ki kaini wajen su zan nemi yafiyarsu ba'a son raina na tafi ba wallahi kuma bazan
ara tafiya ba zan kasance tareda su"
Minoji tace, "yanzu kadawo nutsuwarka kenan? shikenan to sai ka ha
a da matarka waccan da wannan su zama biyu dan Sumayya ta
auka ka mutu har tafara ha
on mijin wata"
cikin sanyi yace, "wallahi ban mutu ba kawai na tsinci kaina acikin wata rayuwa ne"
sai da tayi masa kwatancen da ze gane sannan ta maida hankalinta kan Ziyada cikin ha
e fuska tace, "bani hijab zan tafi"
Ziyada da kanta yagama kullewa tace, "ina zakije?? keda baki da lafiya? nifa har yanzu kallon mahaukaciya nake miki"
Mugun kallonda Minoji tai mata ne yasa ta ha
iye surutan nata ta
akko mata hijab
in, tana zura hijab
in ta fice daga gidan.
Usman yace, "Ziyada maza ki shirya mutafi"
Tace, "zuwa ina?"
Yace, "idan
ata min lokaci zakiyi to ki gayamin zan
auki
ana mu tafi"
Badan taso ba ta tarkato yaran suka shiga mota shi dama tini ya gama komai sai tafiya.
Yaaye sai da yayi kuka me isar shi sannan yatashi ya fice daga gidan ba shi ya dawo ba sai
arfe 12:23am sai da yayi mamakin ganin basu rufe gidan ba batareda ya damu da hakan ba ya shiga sai da ya kulle
ofar sannan ya
arasa ciki yana mamakin surutan da yakeji.
Ayiya tana ganinshi ta mi
e tana murna tace, "Umar? Alhamdulillah yau gashi Usman yadawo gida abun Al'ajabi mun
auka ma shikenan mun rasa shi amma gashi yau harda iyali"
Kallon su kawai Yaaye yayi ya wuce batareda yayi magana ba.
Lototo Ayiya tayi da baki tana kallonsa cike da mamaki.
Yayyi ce tace, "Yaaye kafi kowa son ganin Yayan mu amma yau muna farin cikin dawowarsa naga kai baka damu ba"
Ayiya tace, "haba
annan farin ciki yakamata kayi fa kamar ba kaine Yaaye na ba?"
Cikin zubda
walla yace, "Ayiya ku kun samu naku farin cikin ni kuma kun rabani da nawa, inayin kowane
ari dan naga na faranta muku amma kullum shirin ku shine ku tarwatsa ni kun rabani da ita yanzu kunji da
i kukan da kuke so kuga nayi yanzu kun gani YaaYa ku cigaba da farin ciki nima na tayaku murna"
Kallon kallo Ayiya da YaaYa suka shiga yiwa juna,
Usman yace, "akan me kake magana ne
ani na?? kodai laifina ne da na tafi na barku, dan Allah ka yafe min Umar nima ba'a son raina nai hakan ba"
Girgiza kai yayi alamar aa sannan yace, "ina magana ne akan Minoji matata, dama sun tsane ta kuma sai da suka rabani da ita batareda tai musu laifin komai ba"
Caraf Ziyada tayi tace, "laa ai itace ta gaya mana inda kuke shine muka zo
azun ma tana gidan mu Usman ya tsinceta atiti ne batada lafiya ashe ma aljanu ne da ita"
YaaYa tai karaf tace, "kaji kwanan zancen to ba aljanu ne ma da ita ba itace aljanar da kanta"
Zaro ido Sumayya tayi a firgice tace, "kenan Aljana kaje ka
akko mana Abban Amira???"
Abban Amira kuwa kasa magana yayi saboda abun ya gama kulle masa kai, bazeyi jayayya ba dan kuwa yaga alamu duba da yadda take magana ita ka
ai tana bawa kanta amsa ita ka
ai dole zata kasance
aya acikin biyu ko aljanar ko me aljanu, amma idan hakane tayaya ze bar
an uwansa tareda Aljana hakan kuwa yayi???"
*INDO CE*
SIHIRIN K'AUNA
Chapter 29 · 0% Book details