Sashe 8
Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Washe gari Hibbah bata tashi ba sai wajen k'arfe 9 na safe, bayan tayi sallah asuba data koma abinda bata tab'a yiba kenan barcin safe, shima tayi ne saboda jiya da dare bata samu tayi isasshe ba saboda zazzabin daya rufeta kuma alhamdulillah yanxu ya sauka don garau take jinta.
Bud'e ido tayi tare dayin salati tayi addu'a ta kalli gwaggo dake zaune kan sallaya tana jan casbaha tace "ina kwana gwaggo?" D'aga mata kai gwaggo tayi saboda bata magana idan tana lazimi. Tashi tayi ta wanko fuskarta da bakinta tare da d'auro alwalar sallah walha ta koma daki tayi sallah bayan ta idar ta jima tana kaiwa Allah kukanta akan matsalolinta kafin ta shafa.
Bayan ta idar inna ta ajiye mata kwanon koko da k'osai ga kuma na d'umame a gefe wai taci wanda take so rabon da Hibbah taci irin wannan cimar har ta manta, kokon da k'osai taci taji harma ta k'oshi.
Inna lami kam gari na wayewa ta zari mayafi tayi gidan Inna delu aminiyarta, bayan sun gaisa Inna lami cikin happy tace "uhumm albishirinki aminiyata," itama Inna delu cikin zumud'i tace "Kai muguwa nasan wata muguntar kika shirya tunda har kika kasa jurewa kikazo gidana, to goro bani nasha." Inna lami tace "hmm ai kedar bari, yafa saketa," gud'a delo tasa tace "Kai lami gaskiya kin iya mugunta to ita kuma waccen aljanar 'yar fa?" Lami tayi murmushin mugunta tace "itama a jiyan da daddare uban yace tabar mai gidansa," da zumud'i delu tace"ita kuma me kika yi Mata," shewa lami tayi ta shiga fad'a mata duk abinda ya faru sannan ta d'ora da cewa "shima da uban naga kamar yana jin tausayintaa na fututtuke nace zan bar masa gidansa ba shiri yace ta tafi." Delu ta kalleta tace "gaskiya lami kin fini iya tuggu amma fa kinyi kuskuren korar yarinyar nan daga gidan" cikin alamar tambaya lami tace "kamar ya kuskure bayan itama zata kawo min matsala idan na barta a gidan, saboda idan na barta kinga itama fa tana da gado banda gidan ma ga kuma gonakinsa fa," murmushi delu tayi tace "ai ke baza ki gane ba ai cikin salama zakiyi komi batare da kowa ya zargeki ba".
Inna lami tace "kamar ya?" Kuma murmushin mugunta delu tayi tace "ai kawai aikatau zaki turata birni, kinga kin samu riba biyu kenan ga kudin aikinta gashi kuma ta bar miki gida cikin salama," cikin happy inna tace "Kai delu shiyasa fa nake sonki amma kuma yanxu lokaci ya kure ya kenan?" Delu tace "a'a aminiya lokaci bai kureba, yanxu ita Hibbah tana ina?" Cikin nuna rashin damuwa lami tace "ya huce gidan kakarta tana da inda yafi nan ne?" Delu tace "yauwa kinga ya kwana gidan sauki, kawai turawa zakiyi kice tazo nasan tunda yarinyar nan na sonki babu abinda zai hana ta zuwa." Inna lami tace "Kai delu kin yi dabara to yaushe zaki kaita kenan?" "Ai dama in anjima zan shiga garin kano, Zan anso kudin wata yarinya kinsan wata ya kare," delu ta bata amsa. Lami tace "to kuma kudin nasu yana kaiwa nawa?" Delu tace "eh to ya danganta da yanayin gidan da aka kaita da kuma yanayin aikin da take musu," lami tace "Kai amma fa zan cafki kud'i" delu tace "kodai zamu cafka?" Lami bata amsa ta ba tace "yafa kamata mukoma wajen boka don kar fa malam ya kawo min cikas a lamurana, kamar yarda na fada miki jiya ma fa yaso ya kwafsa," delu tace "bakya sanya lami baki da sauk'i da kinga ya fara warewa saiki kuma d'aureshi" dariya inna lami tayi tace "ina fa zanyi sanya, yanzu dai yaushe zamu je?" Delu tace "eh to muje yanxu, bara na k'arasawa Musa d'umamencan sai mu je?." Lami ta d'an yatsina fuska tace"nikam musan nan idan wani yaji yarda kike masa saiya zata shine mijin naki ai," dariya delu tayi tare da cewa "kamar yarda kike yiwa Rahmatu ba," "ai gara ni macece kuma idan nayi mata ma ai koya mata nake," lami ta maidawa delu. Delu tace "oho dai nima koya masa nake yi" ta fada tana mikewa.
Bakin murhu ta nufa taje ta sauke tukunyar takai d'akin Musa, sannan ta zaro mayafinta suka nufi gidan boka.
Wani daji suka nausa canciki sunma fita daga kauyen *katsalle* sun shiga dajin k'auyen *Gomma* wani dogon dutse naga suna hawa saida suka hayeshi tas, sai kuma suka cire mayafansu da d'an kwalayensu da takalma suka fara tafiya da baya da baya baya har suka k'arasa bakin wata bukka.
Zagi suka shiga yi sai ga wani mummunana gardin mutum ya bayyana a zaune a wajen yana dariya yace "halakarku kun zo ku kuma halaka?" Ya k'alk'ale da dariya, lami ce tace "yauwa boka dama........" Katseta yayi da cewa "na sani! kamar yarda aka Saba ga wannan," ya mika lami wani kullika yace "kici gaba da tsarki dashi, wannan a abincinsa wannan kuma turare," ya kwashe da dariya. Karba tayi tana godiya, yace "wannan yarinyar daza ku turata aikatau karku bari ta kuma waiwayar k'auyen nan don idan kika bari ta dawo gida da akwai matsala gagarima. Ku tashi ku tafi na sallame ku." Yana gama fadin haka ya b'ace, kallon kallo suka shigayi kafin su tashi subar wajen, kayansu suka d'auka suka sa sannan suka sauka daga dutsen kowacce da abinda take sakawa musamman ma lami.
Bayan sun shiga cikin k'auyensu lami ta kalli delu tace "me kike ganin zamuyi akan abinda boka yace?" Delu tayi shiru kafin tace "mafita d'aya ce kawai idan na kaita gidan nace basai ta rink'a zuwa ganin gida ba zan dinga zuwa ganinta." Lami tace "kina ganin hakan ba matsala" delu tace "babu wata matsala ai nace zan dinga zuwa dubata kuma su gidan gaba ta kaisu." Lami tace "Hmm to shikenan bara na huce gida saikin zo." Delu tace "ai kawai mu shiga ki aika a kirata mu huce don ba lallai na dawo ba," murna fal cikin lami suka shiga cikin gidan.
Suna shiga gidan sukaci sa'a Rahmatu na nan, delu tace "shikenan nan ma Rahmatu nanan kinga saita shiga ta kirata koh," kallonta lami tayi tace "toh allah yasa taje kema kinsan halinta." Delu dai batace komi ba suka k'ara cikin gidan.
Kujera delu taja ta zauna hakama lami amma ita tata kujerar kusa da Rahmatu ta kaita tare da kwantar da murya tace "yauwa Rahmatu Dan allah shiga gidansu Abu ki kira min Hibbah kice tazo yanxu." Kallon ta Rahmatu tayi a wulak'ance tace "tab ni wallahi na gaji babu ida zani" matsowa lami ta kumayi kusa da ita tace "haba autar inna kije mana don Allah" Rahmatu ta zumburo baki "wai me zakiyi mata ne bakince ta bar gidan ba, kuma kince ta tsaneni to me kikeso kuma tayi mana a gida?" Lami tace "aike baxaki gane ba aikatau za'a kaita birni kinga kenan duk kudin da aka bada na aikinta namu ne daga nan ma saina saimiki wayar da kikace kina so koh?" Daga Kai Rahmatu tayi cikin happy tace "eh wallahi inna ammafa kinyi dabara bara naje" ta fada tana mikewa da gudu tabar gidan. Lami tace "oh ni lami naga Randa Rahmatu zatayi hankali" delu tace "gaskiya kam."
*by*
*Mamyn Najmah*
[10/26, 9:22 PM] Maman Najma Author P1: 📝🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓
*RAYUWA* page1⃣5⃣to1⃣6⃣
*NA*
*MAMYN NAJMAH*
🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓
*DEDICATED TO AYSHA ALIYU GARKUWA*
*DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION*
D.Z.W.A