← Book details Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 54

Sashe 23

Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Washe gari Monday ta tashi da ciwon kai sakamakon kukan da taci jiya da dadaddare, ta tashi tayiwa Nawaz wanka ta shirya shi school bus na zuwa ya tafi, ita kuwa bata da niyyar zuwa saboda ciwon kan dake damunta don tana gama shiryashi ta koma ta kwanta sai wajen sha d'aya ta tashi tayi duk ayyukanta tana cikin yin mopping taji motsin mutum a bayanta tana waigawa taga Ashe Faheem ne tace "barka da safiya daddy" bai ma jita ba dun ya sha'afa wajen kallonta tunda suke zaune da ita sai yaune ya tab'a k'are mata kallo lokaci d'aya yaji wani abu a zuciyarshi, hazak'ar Hibbah da ayyukanta suna burgeshi sam bata nuna gajiyawarta akan duk abinda Kausar zata sata ga d'awainiyar da take yi masa da yaro. Ta kuma cewa "daddy barka da safiya," ya d'anyi firgit ya kalleta "lafiya" ya huce d'akinsa ya shiga ya d'auko takardun daya manta ya huceta, ita kuwa ko a jikinta ta k'arasa aikinta tayi wanka ta shirya tsam kamar mai fita wajen party ta shiga kitchen ta d'ora musu abinci yana yi ta juye ta jere a dinning ta koma d'aki ta d'an kwanta a hankali bacci yayi awon gaba da ita.
Cikin barci kamar a mafarki taji ana shafata taji kamar an danneta a hankali ta bud'e idanunta wa zata gani Faruq ne a kanta wani wawan ihu ta saki tare da tattaro k'arfinta ta tunkud'eshi ya fad'i k'asa da gudu ta ta fito parlor kicib'is sukayi da Faheem daya dawo hannunsa rik'e dana Nawaz da gudu ya rumgume ta, ita ma ta rik'eshi sai zare ido take yi. Faruq ya fito yana binta da mugun kallo, Nawaz ya k'arasa kusa dashi "uncle yaushe kazo?" "D'azu nazo Nawaz," ya kallo d'aya yayiwa Faheem ya fice abinsa. Faheem Wanda ke tsaye yana kallonsu kamshi ya d'aure me ya kawo Faruq gidanshi yanxu bayan yasan baya gidan, mene a tsakaninsa da Hibbah kodai itama tana biye masane? Da Sauri ya girgiza kai a'a Hibbah tana da halaye masu kyau, ya kalli Hibbah cikin b'acin rai yace "me kike aikata min a gida?" Da sauri ta girgiza Kai "a'a daddy wallahi bansan ya shigo ba ina kwance naji shi.......," nauyin k'arasawa tayi sai ta saki kuka.
Tsayawa yayi kallon ta zuciyarshi ba dad'i sam baya son wannan kukan, ya d'aga mata hannu "tashi ki tafi bana son hayaniya," mik'ewa tayi ta nufi d'akinta tana kuka akan gado ta zube tana ta kuka yanzu shima zarginsa zai d'ora a kanta abinda ta tsana kenan Faheem yaga laifinta shiyasa take jure duk wani wulakanci da Kausar zata yi mata, tashi tayi ta d'auro alwala tayi sallar la'asar a wajen ta zauna tana addu'ar allah yasa Faheem kar ya zargi wani abu tsakaninta da Faruq, kuka ta cigaba dayi Nawaz ya shigo "aunty yunwa nake ji," ta mik'e ta nufi dinning ta zubo masa a plate ta kawo masa gabansa ta tura masa ta koma gefe tayi jugum tana tunani yace "aunty ke baza kici ba?" Ta k'ak'alo murmushi "nak'oshi Nawaz," "aunty dama kinci kafin na dawo ko?" "A'a Nawaz na k'oshi ne," bai kuma yi mata magana ba don shima wani lokacin kisan halinsu d'aya da daddy'nsa haka yaci abincinsa yana gamawa ya fice parlor.
Faheem ya gani parlor ya k'arasa kusa dashi yace "daddy aunty Hibbah tak'icin abinci sai kuka take," Faheem ya kalleshi "kuka kuma Nawaz," "eh daddy tun d'azu take yi," ya mik'e ya nufi d'akinta yana zuwa ya tura k'ofar d'akin ganinta yayi a zaune akan sallaya ta kifa kanta.
"Hibbah saboda me kika k'i cin abinci saboda abinda ya faru?" Da sauri ta girgiza kai, "to menene kisani ni bana zarginki akan komai, amma ki sani babu Wanda zai ganku a d'aki Ku biyu gida kuma ba kowa bai zargi wani abu ba, ki fita harkar Faruq fatan kin fahimce ni," ta gyad'a kai. "Shikenan ni bana son b'atawa mutum banson na ganki kina damuwa don haka ki samo abinci ki ci kinji ko?", ta kuma gyad'a kai to.
Ya rufe k'ofar, sai ta samu kanta tana bin umarninsa, ta d'ebo abincin tana ci sai taji ta samu nutsuwa hankalinta ya kwanta, Nawaz yasa ta a gaba Allah sarki shima ya damu yace "Aunty Hibbah daddy bai tab'a dukana ba kema bazai dake ki ba," tayi dariya yaro yaro ne, ahankali ta wantstsake har tayi musu girkin da dare.
Washe gari da wuri ta tashi tayi komai don zata je skul.

*by*
*Mamyn Najmah*
[10/26, 9:23 PM] Maman Najma Author P1: 📝🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓

*RAYUWA* page3⃣0⃣

*NA*
*MAMYN NAJMAH*

🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓

*DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION*

D.B.W.A

*DEDICATED TO AYSHA ALIYU GARKUWA*

*Facebook groups ina ganin sak'on nin ku da k'arfin gwaiwr da kuke k'ara min ako da yaushe kuma ina godiya Allah ya saka da alkhari ina k'aunarku har cikin raina.*

Yau da yamma ta gama komai da wuri tana zaune a d'aki taji wayar ta na ruri ta d'auko dan ganin wake kiranta bak'urar number ta gani da kamar karta d'auka sai kuma ta d'auka a tsorace "hello!" Ta furta a hankali. Daga d'ayan b'angaran taji yace "Hibbah bak'on ki ne gani nan k'ofar gida ina jiranki," ta dafe k'irgi "wai wa kenan ban gane mai maganar ba," yayi murmushi mai sauti "ai baza ki gane ba tunda ban tab'a kiranki ba, Jabeer ne wannan mutumin mai nacin nan, kiyi min hakuri Hibbah kar kice baza ki fito ba don Allah," Hibbah ta d'anyi shiru sai can tace "to ganin fitowa" ta kashe wayar.
Ta sanya wata abaya bak'a mai mugun khair gami da lullub'e kanta da mayafin rigar, ta shafa powder da lipstick ta feshe jikinta da daddad'an turarukan da aunty ta bata, ta rik'e hannun Nawaz d'an kad'afi duk inda ta cire k'afa ya maida sawunshi, shiyasa suke kuma shak'uwa.

Yana zaune cikin motar ya kasa d'auke idanunsa daga kanta ashe duk ganin da yake mata bai gama ganin baiwar da Allah yayi mata ba, tayi masa kyau shi dai yana k'aunarta a ransa, tak'i goguwa a zuciyarsa wani d'an sataccen murmushi tayi masa, ikon allah sai yaji ta tafi dashi gaba d'aya.
Ya fito ya jingina da motar komanta ya burgeshi ya rik'o hannun Nawaz yana kallon kyakykyawan yaron, a kunyace ta gaisheshi don itama d'in yau ta k'are masa kallo. Bak'ine kyakykyawa wato irin black beauty d'in nan hancinsa dogo har baka shi ya dad'a fito da sigar kyansa ga shiga da tsari, yana sanye da wani laushashshan boyel yayi matuk'ar kyau ga nutsuwa da allah ya bashi.
Ya kalleta da murmushi a fuskarsa yace "Hibbah naji dad'in ganinki da baki fito ba bazanji dad'i ba sai na tafi zuciya ta tana wasi wasi kina jin sak'ona wajen Aunty Aysha na dameta da batunki, Hibbah ki godewa Allah dan ba k'aramin so nake miki ba," tayi murmushi "uhm to na gode itama tana fad'amin," ya kuma murmushi "Aunty sarkin yak'ina ce koda yake itama tasan irin son da nake miki so ne na tsakani da Allah, gashi kuma rowar magana kike yi min so nake naji muryarki dad'i take yi min," ta d'an kalle shi "to me kake so nace?" "Hibbah kenan nidai fatana ki amince min muyi aure, amma fa ban b'oye miki ni mutum ne magidanci mai iyali da mata na da yara na uku ban miki tsufa ba dai ko?" Ta kuma murmushi "aure nufi ne na Allah," "nasan hakan kina nufin kin amince kina so na kuma zaki aure ni?" Tayi shiru, ya karyar da kai yace "hmm Hibbah kinyi shiru har cikina ya d'uri ruwa fa," tayi dariya "sai kace wani mai lefi?" "Ai gara ace lefi nayi zuciyata ta kasa nutsuwa," tad'an sauke ajiyar zuciya "to ka bari sai naje na fad'awa ummana."
Ya dubeta a nutse "shikenan iyaye sune gaba da komi Hibbah na baki dama Amman dai ki tausayawa bawan Allah nan, Zan Kira ki a waya naji yarda kukayi," ya bawa Nawaz kud'i "Nawaz rik'ewa Auntyn ka ko?" A daidai sanda motar Faheem ta sanyo kai ko kallonsu baiyi ba ya shige cikin harabar gidan, 'yar hantar ta saida ta motsa sukayi sallama da Jabeer ya huce sukuma suka tawo gida.

B'angaran Faheem kuwa yana shiga ya zauna kan gado gami da jefar da takardun yayi jim zuciyarsa zafi take da tana tafasa sai yaji gumi ta kowanr kofofin gashinsa kamar Mai had'iyar wuta, ya kasa sanin wannan abu ciwo ne ko lalura ne ya rasa meke masa dad'i, ya huro iska mai d'umi a bakinsa zafi dad'a k'aruwa yake a ko ina na jikinsa, mik'ewa yayi ya shoga toilet ya sakarwa kanshi shower snyin ruwan ya ratsa shi had zuciyaarsa, bai san iya lokacin da ya d'auka ba sannan ya fito ya kunna AC ya kwanta ya d'ora kansa bisa pillow ya lumshe idanunsa.
Yana tunanin wai shin me yasa ya damu kansa da yarinyar nan? Shi fa ba sabgarta yake shiga ba don me yake jin zafo don ya ganta da wani ina ruwanshi da sabgarsu? Don me zai tunzura haka don ta fit a bada izininshu bane ko kuwa metayi masa ya b'ata ransa har hankalinsa ya tashi haka?
Ji yayi anyi masa kiss gami da shafo sajensa, juyowa yayi ya rumgumota yayi ajiyar zuciya, ya lalubo abinshi duk lefinta ne da bata tarairayarsa bare ta kwantar masa da hankali in ya shiga damuwa.
Juyowa tayi suna kallon juna abinda ta gano a idanunsa ya tabbatar mata akwai rikici wani abu ya tab'o mata shi. Ta kuma k'ura masa ido "dear me yake damunka ne naka ka sauya ba kamar yadda nake dawowa na sameka ba," bai fad'a Mata abinda me zuciyarsa ba sai dai yace Mata wai baijin dad'i tunaninta da kewarta suke damunsa, nan ta shiga yi masa kisses masu zafi don k'ok'arin mantar dashi dan tasan lefin tane Sam bata bashi kulawa kullum ita tana wajen aiki kamar agogo..

***
Chapter 23 · 0% Book details