← Book details Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 54

Sashe 16

Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da daddare bayan su momy sun dawo lokacin ma har sun gabatar da dinner d'insu, momy ta Kira Aunty bedroom d'inta take tambayarta mene ya faru a gidan, aunty bata boye mata komai ba ta fad'a mata tun sanda Hibbah tazo gidan har kawo yanzu abinda ke faruwa tsakaninta da Faruq. Momy ta girgiza k'warai dajin k'udirin Faruq akan Hibbah, wayarta ta zaro ta shiga dialing number Faruq saida ta kusan katsewa ya d'auka yana karawa kunnansa yaji momy tace "kazo sama ina son ganika," ta kashe wayar.
Yasan aunty ta fad'awa momy komai shiyasa ko d'ar baijiba. Saman ya hayo ya nufi bedroom d'in momy ya shiga da sallama ya samu waje ya zauna, momy cikin fad'a ta fara magana"yanxu Faruq abinda kayi ka kyauta kenan dama baka canza halinkaba?" Nan momy ta shiga yi masa fad'a sosai ta inda take shiga ba tanan take fita ba, sai da ta wanke shi tas sannan ta Fara yi masa nasiha mai ratsa jiki saida ta tabbar nasihar ta ratsasu sannan ta sallame shi, babu Wanda yayi tunanin Faruq zai kuma magana saboda yadda ya nutsu.
Yana tashi yace "ai dama nasan gidan nan babu mai sona daddy ne kawai da Ya Faheem ke sona suma yanxu gashi basa nan, k'iris ake jira nayi laifi to gobema zan koma hutu kuma yasin na tafi sai kun ganni don bazan kuma dawowa ba saina gama," ya fita yana 'yar mita momy tace "allah ya shiry............

*# JUMMA'AT MUBARAK TO YOU ALL😍*

*by*
*Mamyn Najmah*
[10/26, 9:22 PM] Maman Najma Author P1: 📝🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓

*RAYUWA* page2⃣4⃣

*NA*
*Mamyn Najmah*

🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓

*DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION*

D.B.W.A

*DEDICATED TO AYSHA ALIYU GARKUWA*

*Gagara tarkon mahassada AYSHA ALI GARKUWA ki shige gaba muna binki abaya sawun giwa ya take na rak'umi farin gani farar aniya dashe daga rabba idan zaki yai kuka baza a tsaya ba, Allah ya barmu tare cikin so da k'aunar juna🤝😍*

Washe gari da sassafe Faruq ya had'a kayansa ya huce Abuja gidan Abba wai acan zai k'arasa hutunsa, sai bayan ya sauka ya huta ma sannan wajen k'arfe d'aya na Rana ya Kira momy yake fad'a mata yana Abuja, daya fad'awa momy tad'anyi mamakin wannan tafiyar tashi babu sallama amma daga baya sai ta rakashi da addu'a da fatan samun nasara.
Washe gari Hadiza ta kawowa momy sabbin 'yan aiki mata biyu, saidai su ba kwana zasu dinga yi ba suna gama aikinsu da dare yayi zasu tafi, momy taji dad'in zuwan 'yan aikin nan ba kamar ma aunty don ita bata so taga Hibbah na aikatau shiyasa tayi murna sosai da zuwan 'yan aikin.

Kwanci tashi babu wuya a wajen ubangiji yau gashi har Hibbah tayi wata bakwai a gidan su Auntyn ta, wanda tayi *RAYUWA* a cikinsa mai tsafta da ganin gata tamkar itama 'yar gida ce, babu wanda zai kalli Hibbah yanzu yace itace Hibbah 'yar k'auye, don ta waye sosai jikinta yayi kyau fatarta ta kuma laushi sai sheki take, gashinta ya kuma samun gyara yayi kyau. Ita dai babu abinda zata cewa Auntyn ta da momy sai godiya da fatan alkhari dan duk sanadinsu ta samu wannan gatan, bata da wata matsala yanzu ta *RAYUWA* tasamu gatan da bata samu a wajen iyayenta ba ga ilimi na addini Dana zamani, bata tab'a tunanin zata samu wannan ilimin ba sai gashi ta sanadiyyar aikatau da aka kawota birni yanzu she can speak english for more than 5mnts.

Yau ya kama ranar Monday kuma ayau ne d'alibai suka koma makaranta ciki kuwa har dasu Saudat bayan hutu da sukayi na k'arshen zangon karatu, yanzu sun shiga new session a ranar ne za'a kai Hibbah makaranta.
Da wuri Hibbah ta shirya saboda tasan da yau za'a kaita makarantar boko shiyasa taketa zumud'i har Saudat na tsokanarta wai indai school d'insu ne da k'afarta zata gudu dan idan suka taxi tun safe baza su dawo ba sai shidana yamma", ita dai Hibbah saidai tayi murmushi a ranta tace kaida ka samu gata da dama har zakayi karatu ina kake da k'afar guduwa saidai kayi fatan allah ya shige maka gaba.
Bayan su Saudat sun tafi aunty ta shirya da kanta zata rakata don ansai mata file anyi mata komi, dayake makarantar islamiyyarsu ce kuma basu da nisa a bakin layinsu take da k'afa ma suke tafiya. Bayan sunje makarantar Aunty suka gaisa da malaman direct office d'in principal suka huce bayan ta gaishe shi ta fad'a masa Hibbah itace sabuwar d'alibar dama da aka kawo, sannan ta buk'aci sannin class d'in daya bata, yace "ai bata da takardun primary bamuga sakamakonta ba, JS 1 kawai zamu kaita," nan aunty ta shiga Neman alfarma a kaita SS 1 ajinsu Safiyya, principal yak'i yarda, dake abune na kud'in tana cikashi da su dak'ar principal ya yarda za a kakta JS 3, nan akayi mata komi suka bata uniforms Kala Kala, aunty ta kalleta cikin kulawa tace "Hibbah nasan kinada k'ok'ari da hazak'a pls karki bani kunya, ki mai da hankali akan duk abinda ake koya miki babu ruwanki da k'awaye karatu kikazo yi kuma shi zakiyi, ki kula da kanki Hibbah makarantar nan makaranta ce da take cud'anya da maza kuma 'ya'yan masu kud'i zasu iya rud'arki da abubuwa da dama don haka ki kiyaye, duk da nasan Hibbah na bamai kwad'ayi bace tana jin magana," Hibbah taji dad'in kalaman aunty sosai tace "insha allah aunty zan kiyaye kuma bazan watsa miki k'asa a ido ba, zan maida hankali sosai kan abinda ya kawoni, ke uwa ce a gurina ya zamemin dole nayi miki biyayya," Aunty ma furucin Hibbah yasata farinciki, ta janyo Hibbah ta rumgume ta da d'an wani lokaci kafin suyi sallama aunty ta tafi don itama tana d lectures.

Principal da kanshi ya kai Hibbah class lokacin da suka je da malami acikin class d'in dan saida malamin ya dakata principal ya gabatarwa da students ita as a new comer, ya mik'a amanarta a hannun class rep mace kuma yayi mata mazauni a kusa da class rep din.
Ta maida hankalinta ga malamin suka cika cigaba da d'aukar darasi, sai bayan ya fita class rep d'in ta mik'awa Hibbah hannu cikin harshen turanci tace "barkanki da zuwa bak'uwar mu ni sunana Fauziyya Usman Aliyu zaki iya kirana da fauzy," ita ma Hibbah ta mik'a mata hunn cikin harshen turanci tace "naji dad'in had'uwa dake ni kuma sunana Hibbah Mukhtar Muhammad, fatan zaki rik'e ni amana kamar yadda nima Zan rik'e ki" fauzy ta girgiza kai tace "sunanki na da dad'i kuma zan rik'e amana insha allah," Hibbah tace "na gode kema sunanki yayi dad'i," da haka sukayi ta hira sauran students suka zo suna yi Mata sannu da zuwa da haka wani malamin ya shigo.

Haka Hibbah ta cigaba da zuwa makaranta tana fahimtar abubuwan da ake koya mata, Wanda ya shige mata duhu bata fahimta ba takan tambayi malamai ko fauzy, idan a gida ne kuma sai ta tambayi Auntyn ta idan bata nan ta tambayi Saudat bata tambayar Safiyya saboda babu fuskar tambayar.
A haka har su Hibbah suka k'are zango karatu na farko tare da fito da result d'in data bawa kowa mamaki, ta d'auki 5th position a class.
Aunty tayi murna sosai da result d'in hakan ya kuma bawa Hibbah k'arfin gwaiwa tare da d'aura d'amarar cigaba da farantawa Auntyn tata, satinsu d'aya dayin hutu Abba ya turo a ka d'auki su Safiyya, gidan sai ya koma shiru gashi Hadiza itama ta tafi ganin gida, sai gidan ya zama daga Hibbah sai momy sai kuma 'yan aiki shiyasa Sam Hibbah bata jin dad'in gidan sai dai idan aunty ta dawo.
Ganin yarda Hibbah take takura yasa Aunty ta nemi shawarar momy akan sukai Hibbah gidan kawunta inda ummanta take tayi hutu a can.

Ranar asabar da daddare Aunty suna zaune da Hibbah a d'akinta, dayake Hibbah ta koma d'akin Auntyn tun sanda Hadiza ta tafi ganin gida, aunty ta kalli Hibbah tace "Hibbah ni kuwa akwai wata shawara da muka yanke ni da momy ban Sani ba ko zaki bamu had'in Kai," Hibbah da take duba wani littafin makarantarta ta kalli Aunty tace " Aunty bani da bakin yin jayayya daku duk abinda kukayi a kaina dai dai ne, nasan bazaku tab'ayin abinda zai cuceni ba," aunty taji dad'in furucin Hibbah tace "Hibbah kalamanki da sanin ya kamatanki sune suke kuma dasa k'aunarki a zuciya ta, dama shawarar da muka yanke da momy cewa mukayi tunda gidan nan ya zama ba kowa sai ke kad'ai kuma kema bajin dad'in zaman kike yi ba, shine nace ko zamu kaiki gidan kawunki can wajen ummanki ki k'arasa hutun a can." Da sauri Hibbah ta d'ago kanta tana kallon Aunty sai kuma ga hawaye tace "aunty ina tsoron zuwa wallahi nasan halin inna lami zata iya kasheni, dan allah ki barni a nan d'in," Aunty ta janyota jikinta tace "ki kwantar da hankalinki Hibbah ai Umma da inna lami kince min ba k'auyensu d'aya ba kuma mu iya kacinmu k'auyen da Umma take kawai zamuje," Hibbah ta goge hawayenta "aunty na gode allah ya k'ara d'aukaka, ni dama inna lami nake jin tsoro amma nima inason naga ummana," aunty tayi dariya tace "Hibbah na kin cika tsoro da yawa, ki shirya gobe da safe zamuje don bani da lectures goben," Hibbah ta kuma ruk'unk'ume Auntyn tace "na gode Auntyna allah ya k'ara d'aukaka ya barki da Uncle d'ina," ta fad'a tana tusa kanta jikin Auntyn nata wai kunya taji. Auntyn tayi murmushi tace "ameen Hibbah, tashi mu had'a kayan tafiya." Mik'ewa sukayi suka shiga had'a kayan.
Chapter 16 · 0% Book details