← Book details Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 54

Sashe 19

Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Motar wani abokin Sagir d'in suka shigaa akwai shi da surutu, ita kuwa Hibbah tunda ta shiga motar batai magana ba tana dai ta Danna wayarta ta bud'e pulse d'in da aunty ta bata kud'ine sababbi 'yan hamsin bandir d'aya tayi murmushi a ranta tana yiwa aunty godiya, ta cigaba da sauraron duk hirar dasuke yi shida su Saudat da haka suka k'arasa wajen dinner d'in,waje yayi kyau an k'awatashi.
Su Hibbah akace karsu shiga har sai Amarya tazo, suna nan a jikin wata mota saiga Amarya da angonta cikin shiga ta alfarma suka shiga da su, kowane sit na mutum hud'u ne dan haka su Hibbah suka samu d'aya daga ciki suka zauna.

Suna zaune wannan Wanda ya kawosu d'in yazo ya zauna yana cewa "na zamo cikon na hud'un kenan," ya kalli Hibbah yace "y'ar beauty waike bakya magana ne?" Ta kalleshi tace "sannu ka," ta d'auke kai, ya kalli Saudat yace "Saudat 'yar beauty nan bata magana ne?" "Tana yi mana, ai indai kaga tana magana to tana tare da aunty shiyasa ma nake ce mata jelar aunty," suka sa dariya ita da fauzy. Hibbah ta harareta, shi kuwa murmushi yayi yace "mene sunan beautyn tawa ne," Hibbah ta maimaita a ranta beautyn tawa? A ina na zama tashi? Fauzy ce ta katse mata tunani, ji tayi tace "sunanta Hibbah," da murmushi a saman fuskarsa yace "Hibbaaaaahhh!" Ya wani ja sunan tare da sakin ajiyar zuciya ya kalli Hibbah yace "Hibbah sunanki yana da dad'i kamar yadda kema kike da kyau sunan ya dace dake," Hibbah tace "na gode," yace "da farko dai sunana Jabeer ni abokin sagir ne, kuma ba maganar b'oye b'oye tunda na ganki naji kin shiga zuciya ta Hibbah," Hibbah ta mik'e tace "to na gode da sonda kake min" ya kalleta yace "ina zaki kuma Hibbah? Ina son muyi magana ne," Hibbah ta Fara tafiya tace "inason zanje nayiwa Auntyna lik'i ne," ta fad'a tare dayin gaba.
Jabeer ya kalli su fauzy yace "wallahi da gaske nake Saudat ina son Hibbah tun dana ganta kuma aurenta zanyi" Saudat ta mik'e tace "Ya Jabeer indai kana son ka samu Hibbah cikin sauk'i to ka kama k'afa da aunty" yace "allah ko Saudat" fauzy tace "wallahi ya Jabeer don aunty ce kad'ai zata iya fad'awa Hibbah taji," suka kalli wajen rawa, Hibbah suka hango tana ta zubawa Auntyn ta kud'i, Jabeer yayi murmushi tare da yin wajen rawar su fauzy ma suka mara masa baya.
Yana zuwa ya shiga zubawa Hibbah kud'i yana mata lik'i, ta d'ago Kai ta kalleshi yayi mata murmushi ya cigaba da yi mata lik'in, kallo sai ya koma Kan Hibbah, su Saudat mazari tuni aka fara rawa ta rik'e hannun Hibbah wai sai tayi rawa, ita kuwa Hibbah ba gwanar rawaba ta dai tsaya tana kallon yadda suke ta rawar su.

Haka yayi ta mata lik'i daga baya aka tashi daga wajen dinner ango ya d'auki amaryarsa suka huce, abokan ango suka kwashe 'yammatan suka huce dasu. Ita kuwa Hibbah tana ganin zaa tashi taje ta cewa Adamu driver ya kaita gida tayiwa Aunty sallama, aunty ta jata gefe tace "Hibbah dan allah kiyi hakuri da duk abinda Kausar zata yi miki nasan kina da hakuri ki k'ara akan na da, kuma nasa Adamu d'azu yakai miki kayanki duka gidan saina gobe dazaki sa kawai ya bar miki suna d'akina," Hibbah ta share hawayen daya zubo mata "insha allah aunty na gode," da haka sukayi bankwana, aunty ta kawar da kanta don bata son Hibbah taga hawayenta, Hibbah itama ta huce tana share hawaye don ta shaku da aunty fiye da kowa, Adamu ya tafi kaita.
Shi kuwa Jabeer shida su Saudat sai nemanta suke yi daga baya suka gaji ya d'auki Saudat ya kaita gida ita kuma fauzy driver'n su ne ya kaita.
Hibbah tana zuwa taga gidan babu kowa duk 'yan bikin sun watse sai su aunty Kausar da safiyya a zaune a parlor suna maida gajiya, Hibbah ta shigo da sallama babu Wanda ya amsa Kausar ta bita da wani mugun kallo tace "'yar aiki kawai..............

*kuyi hakuri da wannan, muna asibiti ne 'yar hatsaniyar da taa faru a fagge ne ta ritsa da nephew na yanzu haka ma muna asibiti bashi da lpy, ina bukatar addu'ar ku pls🙏.*

*by*
*Mamyn Najmah*
[10/26, 9:22 PM] Maman Najma Author P1: 📝🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓

*RAYUWA* page2⃣7⃣

*NA*
*MAMYN NAJMAH*

🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓

*DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION*

D.B.W.A

*DEDICATED TO AYSHA ALIYU GARKUWA*

*Wannan page d'in nakune MASOYA RAYUWA GROUP na gode da k'aunar da kuke nuna min Ana mugun tare🤝😍.*

*Fans na gode da addu'o'in ku Allah ya saka da alkhari.*

Hibbah ba tace komai ba ta nufi stairs da niyyar hawa, fincikota Safiyya tayi tana mata wani mugun kallo tace "haba madam da kenan kafin aunty tabar gidan nan, yanzu baki da 'yancin hawar mana stairs ba tare da izinin mu ba don haka kisan nayi," Hibbah ta d'ago ta kalli Safiyya sannan ta kalli Kausar ta juya da nufin ta fiya taji muryar momy, "Hibbah hayowarki ki rabu dasu don Aysha ta bar gidan nan hakan ba yana nufin na daina kula dake ba kenan," Hibbah ta juyo ta kalli momy tana daga sama take magana momy tayi mata murmushi, hawa Hibbah ta shigayi direct ta huce d'akin Auntyn ta.
Momy ta wurga musu wani kallo tace "ke Safiyya ki kiyayeni wallahi ki fita a ido na, naga kanki yana rawa ko zan daidaita miki shi zan d'auki babban mataki akanki, ke kuma Kausar saboda zubda girma har dake ake yiwa yarinyar nan rashin mutunci ko? Ku cigaba," Kausar tayi k'asa da kai Safiyya tace "kiyi hakuri momy," harararta momy tayi tare da yin ciki.
Safiyya ta kalli Kausar, Kausar tace "Safiyya dafa matsala kalli yadda momy take mana fad'a kan waccan banzar," Safiyya tace "hmm ai sainayi maganinta," Saudat ce tayi sallama ta k'araso kusa dasu ta xube a kujera tace "wash Allah wallahi na gaji, Safiyya kun jima da dawowa kenan," Ta fad'a tana kallon Safiyya, Safiyya tace "eh tun kafin Aunty su huce muka tawo," Saudat tace "kuna nan a zaune tunda kuka dawo?" D'aga mata kai Safiyya tayi tace "eh mene kike tambaya?"
Saudat tad'an kishingid'a tace "kunga shigowar Hibbah? Tun d'azu da aka tashi muketa nemanta amma bamu ganta ba," harararta Kausar tayi tace "Saudat wannan wane irin maganar banzane, kinga munyi miki kama da masu gadi ne daza kizo kina tambayar mu wata banzar 'yar aiki," Saudat taji haushin furucin Kausar dama kuma ba shiri suke ba, Saudat tace "kinga dai aunty Kausar bada ke nake ba kiyi hakuri kiyi min shiru," Safiyya ta kalleta tace "ai gara ita ta tanka miki ni kina tunanin zan tanka miki ne yarinyar da a kanta momy tayi min fad'a, kuma ki fad'a mata tunda tasa momy tayi min fad'a sai tayi data sanin zuwanta gidan nan" Saudat ta buga tsaki tare da mik'ewa ta kalli Safiyya tace "aikin banza don momy tayi miki fad'a saiki huce a kanta? To bismillah," ta kalli Kausar data d'ora k'afa d'aya kan d'aya tana karka d'awa, Saudat tace "a shawarce da zaki daina biyewa wannan daya fiye miki, kinfi kowa sanin halinta matarda ko gidanta bataso aje shine kike mak'ale da ita, duk soyayyar da zata miki a gaban su momy ne kina zuwa gidanta zakiga bambanci ," tana gama fad'in haka ta hau stairs, binta da ido sukayi musamman ma Kausar tayi mamakin Saudat, kuma ta kasa cewa komai, suka kalli juna Safiyya a ranta ta yarda da kalaman Saudat don kafin aunty tayi aure saida tazo tana fad'awa momy.
Ita kuwa Saudat d'akin aunty ta nufa donta duba ko Hibbah ta dawo, shiga d'akin tayi da sallama ta k'arasa kusa da Hibbah tana murmushi tace "shine kika gudo koh? Mukaje can muna ta nemanki." Hibbah tayi dariya tace"wallahi gani nayi wannan mutumin yana neman takurani ne shiyasa," Saudat ta d'an matso kusa da ita tace "Hibbah baki fahimci Ya Jabeer bane yana da halaye masu kyau ki tsaya ki fahimce sa," Hibbah ta d'an kalleta tace "kinga Saudat nifa bacci nake ji ki rabu Dani da halin mazan nan duk Wanda yazo wajenki buk'atarsa d'aya ce ya nemi jikin ki," "a'a Hibbah karki yanke hukunci" Saudat tayi saurin katseta, Hibbah tayi murmushi tare da mik'ewa ba tace komai ba ta nufi toilet ta d'an watsa ruwa ta d'auro alwala sukayi sallama da Saudat, tayi addu'o'in ta ta kwanta.

Kamar yadda ta saba tashi haka yauma ta tashi, ta d'auro alwala ta zo tana ta nafilfili tana rok'on allah ya k'ara mata juriya da hakurin zama da Kausar, tana nan zaune har akayi assalamu ta tashi ta gabatar da sallah, ta d'auko Qur'anin aunty ta shiga karantawa, bayan ta idar ta d'ora da azkar har gari yayi haske sannan ta ajiye ta sauko k'asa ta nufi kitchen.
Hadiza ta gani tana kiciniyar had'a breakfast, ta gaisheta suka shiga had'awa tare. Suna ta hira har suka gama suka kai dinning Hibbah ta jere kayan, Hadiza dama ta ware nasu daban ta koma sukaci sunata hira.
Chapter 19 · 0% Book details