Sashe 39
Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Ya ilahi, babu tsimi babu dabara sai daga Allah, kansa kamar ya rabe biyu ga zuciyarsa data tsananta bugawa bai tab'a shiga tashin hankali irin na yau ba, ya rasa a wane hali yake ciki sai dai hakuri, don Faruq k'aninsa ne kuma babu yadda zaiyi don tuni ya yanke hukuncin sadaukarwa da Faruq soyayyarshi, sai dai son Hibbah ya illatashi ainun don allah ne kad'ai yasan yadda yake matuk'ar son Hibbah a ransa, ji yake inama bai furtawa Hibbah Kalmar so ba ya barsa cikin ransa, dominzata zama Matar k'aninsa kuma dole akwai abinda zai had'asu yasani tunda son gaskiya yake mata duk sanda suka had'u dole ne wani abu ya motsa zuciyarsa. Sai yaji wani abu marar dad'i domin yaci burin *RAYUWA* da Hibbah.
Ya katse masa tunani "baka ce komai ba Faheem" bai yarda sun had'a idanu da Daddy ba don zai iya fahimtar yanayinsa ya sauya, har shima ya ja masa bak'in layi kamar yadda ya yiwa Aysha yanzun nan, ya d'anyi gyaran murya don yawun bakinsa ya bushr akan harshensa "insha Allah babu matsala Allah ya tabbatar da alkhari" "ameen Faheem Allah ya yi muku albarka, ka gaishe min da abokina Nawaz" yayi murmushin k'arfin hali yayi musu sallama.
Faruq ya bishi da kallo yana wani tunani akwai abubuwan da ya jima yana nazari da son ganosu akan Faheem ya sanya mishi ayar tambaya, labarin zuciya a tambayi fuska ya gano Faheem baya son mu'amalarsa da Hibbah, yana ganin wani yanayi a tattare dashi a duk sanda ya gansa da Hibbah sai dai kawai bai tab'a fitowa k'arara ya nuna da'awarsa ba balle ya tofa wata kalma Mara kyau.
Aunty Aysha ce 'yar Hana ruwa guru saidai ta manta gaba da gabanta shima shiyasa ya kawo k'ararta wajen Daddy inda ko tak'i ko taso dole tabi, ko d'an shaid'an ne shi ba d'an bariki ba saiya auri Hibbah.
Ba k'aramin dad'i yaji ba shiyasa yake k'aunar tsohun nasu mutum ne mai jajircewa akansa baya k'aunar b'acin ransa, Daddy ya dafa kafad'arsa fuskarsa da murmushi, tunaninsa ya katse yayi dariya "na gode Daddy banson me nayiwa Aunty Aysha ba bata sona yanzu." "Ya isa banson wannan ba kaga nayi mata barazana da fad'aba kace zaka kawo mata raini babu ruwanka kabar ni, ni da ita tunda duk ni na haifeku kuma nasa albarka a cikin wannan aure nayi addu'a, Allah ya albarkaci lamarin ka kwantar da hankalinka idan kaga ba'ayi ba to Allah ne bai k'addara za'ayi ba. Amma ina Jan hankalinka ka nutsu ka gyara halayenka don shi aure nauyi ne da hak'k'insa zai d'oru a kanka ka gyara zuciyarka ka zama cikakken mutum ka duba misali akan d'an uwanka Faheem mana abin kwatancena da alfaharina a ko ina za'a girmamashi." Ya gyad'a kansa "insha Allah Daddy Allah ya k'ara girma" "ameen" Faruq ya mik'e shikam tafi nono fari don farin ciki ya cika zuciyarsa a yau.
K'wak'walwa ta hargitse ya fad'a motarsa gwuiwoyi a sab'ule, kamar an doke idanunsa sun k'ank'ance kansa yayi nauyi ya rasa meke masa dad'i a duniya yau zuciyarsa ta tunzura ta ya mutse "Hibbah" ya furta cikin wata iriyar murya ikon Allah abu biyu ne rak a kowane jarrabi na *RAYUWA* samu ko kuma rashi, nasara ko rashinta, amma rashin cikar abinda kake so yafi tada maka hankali don zakaji kamar ka rasa wani sashe na ruhinka. Wace irin rashin sa'a Gare shi wane irin so yake yiwa Hibbah gashi kuma ya sameta ta zama mallakinsa amma zai salwantar da soyayyarta don faranta ran mahaifinsa da d'an uwansa. Anya ma zai iya tuk'in nan kuwa?
Aunty ta bud'e motar ta zauna, waya fi jin bak'in ciki tsakanin ita da Faheem, sam bata ji dad'i ba Faruq yayi nasara, gabanta ya cigaba da harbawa ta had'iyi yawu dak'yar cikin damuwa, nazarinta da tunaninta baika ga fahimtar Faheem ba ganinta ta fishi bak'in cikinda shiga damuwa da tana da yadda zatayi to tabbas da saita hana wannan auren, kawai abinda ta d'auka Faheem baya jin dad'i ne.
"Baka jin dad'i ne naga yanayinka gaba d'aya ya sauya? Naga yanzu muke tare lafiya lau, ni maganar shashashan yaron nan ta dame ni" yayi shiru, hakan ya dad'a bata tsoro "Yaya karka tada min hankali wani abin ke damunka?" Ya sunkui da kansa shi kad'ai yasan me yake ji a zuciyarsa. Ya cira idanu ya dubeta saida gabanta ya fad'i ragagas, cikin razana ta fiddo ido tana mamaki bata tab'a ganinsa cikin wannan halin ba.
Ya dafa saman kujerar da take zaune " Aysha babu Wanda zai iyayi min maganin fitinar da nake ciki sai Allah na shiga mawuyacin hali Wanda ni da kaina tunanina da hangen nesa na bai tab'a hango min shiba, domin zuciya ta ta Gaza sarrafuwa naso dak'ile tasirin al'amarin amma baud'ad'd'ene a yanzu lokaci ya k'ure min, saidai ni da kaina ina tausayawa kaina zanyi k'ok'arin hakuri Allah ya bani jimiri." Ya dubeta cikin idanu "ina son Hibbah son da bazan iya misalta miki shi ba na fahimci na fahimci hakan saboda abubuwan da suke faruwa tsakaninta da Faruq shiyasa na kasa samun nutsuwa nasa Hibbah gaba na tambaye ta don ina son gano abinda ke tsakaninta da Faruq, amma bata nuna min akwai wata alak'a a tsakaninsu mai k'afi ba kamar yadda na sani dai shike zuwa wajenta, na sanya idanu da tsaro don sanin halin yaron nan bawai yana sonta tsakani da Allah bane, da ita yarinyar zatayi tunani bai kamata ta kuma sauraronsa ba ko don abinda yayi mata, tsoron kar wani abu ya faru na kasa b'oye abinda ke zuciyata da farko na gana da Ummanta d'ari bisa d'ari ta bani goyon baya kafin nace zan aureta, a lokacin tace na kirawo waliyina a d'aura mana aure saboda son da nake yiwa Hibbah ya rufe min idanu, ban kawo komai a raina ba na Kira Abba na fad'a mishi komai Allah ya taimake ni a lokacin yana gari, a ranar da yamma aka d'aura mana aure da Hibbah a masallacin unguwarsu. Bana son abinda zai b'ata ran daddy Aysha shiyasa na yanke shawarar zan barwa Faruq Hibbah ni zan hakura!" Ya had'iye bushshshen yawu "Aysha ki kaini asibiti wani abu yana tab'o min zuciya" ta runtse ido ga mamakinta hawaye ya zubo mata saboda tausayin d'an uwan nata.
"Haba Yaya wane irin hukunci ne wannnan ka yanke ma kanka, kai ne kawai is dace da aurenta domin kai mutum ne dana tabbatar baza ka tab'a wulakanta mace ba har *Abadan*, duk wani jin k'ai da tallafi zaka yiwa Hibbah a matsayin matarka saboda kyawawan halayebka haka matsalolin gidanka sun dakushe, amma Hibbah tasab komai kuma zata magance su da tafiyar da al'amuran iyalanka. Ta saba da Nawaz ta jashi a jiki tana tarairayarsa me yafi wannan kwanciyar hankali, gata mai ladabi kuma tana baka girmanka dayi maka biyayya bata tab'a tsallake maganarka, wallahi na tabbatar Hibbah xata amince da auren nan ko musu baza tayi ba, ko da ace bata ra'ayin aurenka maganar gaskiya kawai idan su dadday sukaje sukaji tana da aure sai mu fad'a musu kaine mijin, amma zancen sadaukarda soyayya ma bai taso ba." Ya numfasa "Aysha kinfi kowa sanin halayena bana son naga ko kad'an na b'atawa su daddy rai, kinsan yadda yake ji da Faruq kina ganin dai maganganun daya fad'a miki don kawai kince bazai aureta ba, to ina kuma ni Dana aureta gaba d'aya? Gobe idan sunji tana da aure a goben zan bar masa ita insha Allah, Aysha karki manta komai nufin Allah ne ki rik'e min wannan banason kowa ya sani sai gobe zan fad'a musu da kaina, Faruq d'an uwana ne banason hanashi auren Hibbah ina k'ausa sosai zan iya sadaukar mishi da komai."
Ta goge hawayenta tana girgiza kai "Yaya wata kusan tafi wata bazan iya had'a 'yan uwantaka ta dakai da shi ba, bazan iya jayayya da kai da mahaifinmu ba inda wani bare ne da saina hana yuwuwar abin amma tunda Kai ka yanke hukunci da kanka, Allah ya tabbatar mana da alkhari, muje na kaika kaga doctor." Ya yamutsa fuskq "ba komai kawai ki rakani gida bazan iya tafiya ni kad'ai bane, kinsan tuk'i saida nutsuw................
*by*
*Mamyn Najmah*
[10/26, 9:26 PM] Maman Najma Author P1: 📝🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓
*RAYUWA* page4⃣2⃣
*NA*
*MAMYN NAJMAH*
🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓
*DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION*
D.B.W.A
*DEDICATED TO AYSHA ALIYU GARKUWA*