← Book details Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 54

Sashe 28

Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Hankalinta a tashe ta shigo ta ganshi yana barci ta zauna tana shafa sumarsa tayi ajiyar zuciya cike da tausayin d'an nata wani mummunan tunani ya fad'o mata _yanzu idan Nawaz ya mutu yaya zanyi?_ ji tayi k'irjinta tayi mugun bugawa.
Ta dubi Faheem yana rik'e da hannun Nawaz da aka Sanya mishi k'arin ruwa don kar ya motsa ya goce, kamar yasan abinda take tunani wani abu ta hango a cikin idanunsa tsabar damuwa ce kawai, Faheem yana son yara sai dai babu yarda zaiyi ne yabar abin a zuciyar shi.
In banda yahudanci da sab'awa Allah, bawa yace shi zai zab'awa kansa yaran da yake son ya Haifa wannan ai halaka ne, ka manta Allah shi ya halicceka shiyake da hurumin zab'a maka komai na rayuwa, kuma yarda yaso haka za'ayi don haka tun anan imanin mutum yayi rauni kenan.
Ta kewaya hannunta a bayanshi ta sunkuyo ta gefen kunnanshi da sigar lallashi "dear menene ka damu da yawa zaiji sauk'i insha Allah, baka walwala cikin kwanakin nan meke saka damuwa ne haka uhmm?" Ta janyo kujera ta zaune suna fuskantar juna, "kinfi kowa sanin damuwata, dole ne na damu don ni bansan dad'in mace ba, saboda bamu da mahimmanci a gurinki aikinki ya fimu a wajenki baki da lokacin iyalinki, duk wani hakuri nayi a kanki gashi nan saboda ciye ciyen restaurant yaro na ya samu matsala cikinsa ya gurb'ace, kullum ni kenan yawo gidajen abinci sunan ni magidanci ne ina da mata, wani abin bana k'ate bane nifa na gaji mafita zan samawa kaina," ta d'ora kanta akan cinyarsa don tasan ta tab'oshi kuma ya fita gaskiya "kayi hakuri naji lefina na d'auka zansa momy ta nemo mai dafa masa abinci," yayi shiru maganar ta kuma Bashi haushi wato ita dai baza ta zauna ta kula da gidanta ba kenan.
Nawaz ya farka yace "Daddy" ya rik'oshi yana shafa kansa "Nawaz sannu cikin ne?" Ya girgiza kai, "zaka sha yogurt?" Ya kuma girgiza kai yace "aunty Hibbah" suka kalli juna, tsaki taja "har yanzu bai manta wannan yarinyar ba sai kace mayya ko kurwars ta kama ne, haba abin yayi yawa," bai kulata ba ya zubo mishi yogurt a cup yana bashi amma surutun Hibbah yake tayi musu, Kausar ta kama mita don haushi taji wai duk kwashe kwashen Faheem ne da Aysha sai da ta nuna rashin amincewarta akan zaman Hibbah a gidan k'ila ma mayya ce.
Yayi murmushi "hmmm ki Sani ita zuciya nason mai kyautata mata shi yake sanya shak'uwa har mutum ya ji bazai iya rabuwa da mutumin nan ba domin rashinsa wani gib'ine a rayuwarsa, kinga d'anki ma kenan k'aramin yaro yasan mai tarairayarsa mai k'aunarsa har rashinta ya sakashi damuwa, ina tabbatar miki da kece bakyanan bazai damu haka ba don bai saba ganinki a gida ba bare ki rumgume shi ya shak'u dake kamar ko wace uwa da d'anta, 'yan awoyi kad'an kike bamu sauran duk na aiki ne agogo sarkin aiki, to idan mafarki kike ki farka don wallahi kinji na rantse na kusa sama mana mafita," Kausar taji zafin kalaman Faheem ta wurga masa wani kallo tama kasa magana sai huci take ta warto jakarta ta fita fuuuu babu ko sallama. Ya tab'e baki, ya cigaba da kula da Nawaz yana ta biye masa suna surutu har bacci ya d'auke shi ya gyara mishi kwanciya.

Washe gari da sanyin safiya ta shigo tana cika tana batsewa, sai da taga jikin Nawaz da sauk'i ta d'anyi saki ranta, doctor ya shigo ya dubashi ya d'an jinkirta Bashi sallama don a cewarsa karsu tafi wani abu ya faru saiya tabbatar da lafiyarsa.
Dak'ar Kausar tayi masa magana tana wani kumbure kumbure ta tambayi lafiyar Nawaz, shima a ciki ya amsa mata don ganin wajen aiki zata tafi, azaton shi yau dai zata zauna ta kula da d'anta domin lafiya tafi kud'i, mai makon ma ta dafo wani abu da tasan mara lafiya zai buk'ata ta kawo musu sai tazo musu k'iyau miyau. Sai takardu a hannu sai kace wadda zata kadance kundin ilimin duniya, shi yasan duk wannan aikin da take yi d'anta ya fishing daraja a matsayinta na 'ya mace bata da abinda yafi d'anta mahimmanci a wajenta.
Ta dubi agogo "Zan wuce wajen aiki su momy suna zuwa da abinci munyi waya da Safiyya," ko kallon ta bai yi ba "basu da hakkin bani abinci wannan aikinki ne ba nasu ba kuma baki damu ba zaki tafi uzurinki, akwai ranar k'in dillanci, shiyasa wasu 'ya'yan sam basa tausayin iyayensu kuma ba komai ke janyowa ba sai irin wad'annan abubuwan, baka san wahalar d'an daka haifa ba, shi zaiji k'anka bayan ke ba haka iyayenmu suka yi miki ba," ta d'aga mishi hannu cikin hayayyak'owa "bafa tsoranka nake ji ba da zaka dinga fad'amin abinda kaga dama, ka fad'amin ayar da tace don ka aure ni na ciyar dakai cewa akayi a ciyar dani, kuma ni haka tsarina yake bazan canza ba," "ke kuma akace kimin biyayya don ki samu aljanna to idan na nemo abinda Zan ciyar dake yana cikin biyayyar aure ki dafa min, to don haka ki kiyaye yimin ihu aka kinsan ni ba sa'anki bane sannan a k'ark'ashi na kike kin gane koh?" A fusace ta fita, ya cije leb'e wato yayi shi kad'ai ita bazata saurareshi ba.
Duk iyalan gidan sunzo momy, daddy yake yana gari da Faruq su Saudat suna makaranta shiyasa basu zo ba, suna zuwa Faheem yace zaije ya d'an kintsa a gida, momy tayi mamaki da Faheem yace mata wai Kausar ta tafi aiki.

Da yamma ya kasa jurewa ya nemo number Aysha, ringing biyu ta d'auka bayan sun gaisa tace "Dan Allah yaya kayi hakuri ina tafe an jima zan shigo ya jikin boy d'in nawa?" "Karki samu damuwa da sauk'i sosai," "to harna ji dad'i Allah ya k'ara sauki, yauwa yaya don Allah ina son ganin Hibbah zamu d'an tattauna akan maganar Jabeer wallahi ya dameni yana so a yi auren nan kasan wajen aikin mu d'aya,"
Gaba d'aya ji yayi wani abu mai Kama da bugun guduma a tsakar kansa, ransa babu dad'i yayi ajiyar zuciya wani abu na nuk'urk'usar zuciyar sa, "yaya kana jina dai ko?" "Hmmm ina sauraronki, bata nan taje gida ne kwana biyu bata dawo ba bansani ba ko lafiya, bani address d'in gidan nasu,"
"Oh to Allah yasa lafiya don nima ban nemeta ba kwana biyu, ai gidan Alhaji sani ne gidan nasu fa," "Alhaji sani dai wanda na sani?" Faheem ya tambaya "eh shine yaya," sukayi sallam.
Sai ya samu kansa da............

*by*
*Mamyn Najmah*
[10/26, 9:24 PM] Maman Najma Author P1: 📝🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓

*RAYUWA* page3⃣4⃣

*NA*
*MAMYN NAJMAH*

🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓

*DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION*

D.B.W.A

*DEDICATED TO AYSHA ALIYU GARKUWA*

```Tabital pulaaku group ina kuke? Wannan wannan page d'in d'ungurungun nakune, Allah ya barmu tare cikin so da k'aunar junanmu.```
Chapter 28 · 0% Book details