Sashe 20
Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Sama Hibbah ta koma tayi wanka ta shirya cikin wani material Orange tayi masifar kyau ta gyara fuskarta, wayarta ta d'auka tanata game har wajen sha d'aya sannan taji motsin 'yan gidan.
Tana zaune wajen sha biyu Hisham ya turo k'ofa ya shigo, ya k'araso gaban Hibbah yace ""aunty Hibbah kizo inji daddy'n Nawaz," ji tayi gabanta ya fad'i duk da bata sanshi ba, mayafinta ta d'auka tasan tafiya zasuyi k'irjinta na bugawa ta fita.
A parlor'n k'asa taga 'yan gidan a zazzaune harda su momy ita da mamy amma banda aunty Kausar da alama tana tare da mijin nata ko kuma tun jiya ta huce ta gaishe da su, momy tace "yauwa kije yana waje yana jiranki, ki kula da kanki Hibbah ki d'auke kanki akan duk abinda za'a yi miki, can yana da bambanci da nan kinji?" D'aga mata kai Hibbah tayi k'aunar momy na kuma shiga ranta, tace "na gode momy allah ya saka da alkhari," momy tace "ameen Hibbah," mamy ta kalli su Safiyya tace "ku tashi Ku rakata mana," Saudat ce ta fara mik'ewa taja hannun Hibbah suka fita, ita kuwa Safiyya dama danna wayarta take yi data fito ma cigaba tayi da abinta.
A mota suka tarar dashi motar a bud'e shi kuma ya zuro kafarsa d'aya waje yanayiwa Nawaz wasa, suka k'araso wajen inda yake suka gaishe shi ya amsa tare da d'agowa ya kalleta, ji tayi gabanta yayi wata muguwar fad'uwa ganinsa tayi kamar Faruq komai nashi irin na Faruq bambancinsa da Faruq kawai girmane amma hatta maganarsu ma iri d'aya ce.
Ya kalli Nawaz yace "boy shiga mota mu tafi gida," yaron d'an kyakykyawa yace "to daddy," ya kalli su Saudat yace "Aunty Saudat wace wannan?" Saudat tayi murmushi tace "sunanta aunty Hibbah," ya kalli Hibbah yace "aunty Hibbah," Hibbah ta kalleshi tana murmushi. Ya kuma kallon Saudat yace "aunty Saudat aunty Hibbah tana murmushi don na Kira sunanta," Faheem ne ya katseshi da cewa "Nawaz ka shiga mota mu tafi mana," da sauri yaron ya juya ya bud'e motar tare da shiga yana yiwa su Hibbah murmushi, Saudat ma ta bud'ewa Hibbah gidan baya ta shiga sukayi sallama, Faheem ya tashi motar suka huce. Safiyya na ganin sun tafi ta komawarta gida dama ita Danna wayarta take.
A mota Nawaz sai surutu yake tayi shi kad'ai, yace "daddy aunty Hibbah gidan mu zamu da ita?" Faheem dayake tuk'i yace "eh Nawaz ita zata dinga zama tare da kai idan ka dawo daga school, tayi maka wanka ta koya maka homework ta dafa mana abinci," Nawaz jin ya ambaci homework yasaki ihun murna "yeeeh daddy nima na samu aunty," ya juyo yana kallon Hibbah yace "aunty Hibbah har unguwa zaki dinga zuwa dani momy na bata zuwa unguwa dani wai nayi girma, ai banyi girma ba ko aunty?" Hibbah ta d'aga masa kai tana murmushi tace "eh Nawaz zan dinga zuwa dakai," lokaci d'aya taji k'aunar yaron ta shiga ranta, shi kuwa Nawaz cigaba yayi da wasanshi har suka k'araso gidan Mai gadi ya bud'e gate d'in gidan yana yiwa Faheem sannu dazuwa.
A parking lot ya ajiye motar suka fito, Faheem yayi gaba shi kuma Nawaz ya zo ya rik'e hannun Hibbah suka parlor yana ta yi mata surutu. Suna shiga suka tararda Faheem a parlor yana k'ok'arin kunna TV, bai kallesu ba ya kunna TV ya dawo ya zauna yana kallon labarai, a k'asa Hibbah ta zauna Nawaz yana kan cinyarta, Faheem yad'an kalleta kad'an ya kawar da kansa yace "Hibbah sunanki ko?" Hibbah ta d'aga kai "eh" yace "Hibbah aikin ki a gidan nan shine girki, gyaran gida sai kular min da Nawaz pls ki rik'e amana," Hibbah tace "insha allah daddy," Faheem ya cigaba da kallo yace "sannan maganar zuwa school d'inki idan kika gama aikin da wuri sai kije yanzu dai samo min wani abu naci," Hibbah ta mik'e ya kalli Nawaz yace "son nuna mata d'akin da zata zauna da kitchen," Nawaz ya mik'e ya rik'e hannun Hibbah ya kaita har d'akin dayake yasan suna extra daki ta ajiye mayafinta, sannan ya kaita kitchen. Gaskiya ta raina tsaftar matar gidan kitchen duk yayi datti kaya duk a barbaje komai a wulakance yayi kaca kaca, nan ta shiga gyara kitchen d'in ta d'auke kayan ta wanke ta share tayi mopping kitchen din yayi fes, sannan ta d'ora girkin..........
*by*
*Mamyn Najmah*
[10/26, 9:22 PM] Maman Najma Author P1: 📝🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓
*RAYUWA* page2⃣8⃣
*NA*
*MAMYN NAJMAH*
🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓
*DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION*
D.B.W.A
*DEDICATED TO AYAHA ALIYU GARKUWA*
*Ina taya duk musulman duniya murnar shiga sabuwar shekarar Muslunci, allah ya bamu alkharan wannan shekara ameen.*
*Ina kuke DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION FANS wannan page d'in nakune muna godiya da k'aunarku.*
Nan da nan gida ya d'auki k'amshin girki, ta had'a lemon kwakwa, bayan ta gama ta juyo shi a kula ta kai dinning ta ajiye ta koma d'auko lemon ta tawo da plates da spoons sai kuma cups tazo ta ajiye akan dinning d'in, ta zubawa Faheem daban ta zubawa Nawaz shima nashi ta rufe ko wanne da wani plate d'in. Ta dawo parlor ta tsugunna a gaban Faheem tace "daddy na gama ga abincin can a dinning," ba tare daya kalleta ba yace "ke kin d'ibi abincin?" Ta girgiza kai alamar a'a yace "kije kici" "to" ta fad'a tana komawa wajen dinning din, ta d'ebo a plate d'in tazo zata huce Faheem yace "ina zaki?" Tace "daddy a d'aki zanci," ya d'aga kai tare da mik'ewa Nawaz na biye dashi suka k'arasa dinning.
Yana bud'ewa wani daddad'an k'amshi ya daki hancinsa ya lumshe ido tare da kai lomar farko bakinshi, kuma lumshe ido yayi gaskiya yaji dad'in abincin rabon dayaci irin wannan abincin tun yana gidan momy, ya kuma kai wata lomar bakinsa tare da kurbar lemon, Subhanallah ji yayi ya kuma rikicewa gaskiya yarinyar nan ta iya girgiki abinda yake fad'a kenan a ranshi.
Nawaz sai da ya gama wasansa sannan ya fara cin abincin yana ci yace "daddy abincin aunty Hibbah ba irin wanda kake siyo mana ba," Faheem yayi murmushi yana shafa kan Nawaz yace "haka ne Nawaz abincin Hibbah yayi dad'i, amma kaci abincinka banda surutu kar ka kware kaji," yace "to daddy amma kullum ita zata dinga yi mana abinci ko?" Faheem ya d'aga masa kai, ya cigaba da cin abincin har suka gama, suna gamawa Nawaz ya ruga d'akin Hibbah lokacin itama ta gama ci, ya shigo yana cewa "Aunty Hibbah abinci da dad'i daddy ma yace da dad'i," Hibbah tayu murmushi taji dad'in furucin Nawaz tace "Nawaz idan aka shigo d'aki sallama ake fara yi kafin ayi wata magana," Nawaz ya d'an karyar dakai "to kiyi hakuri aunty abincin ne yayi dad'i," Hibbah tayi murmushi tace "to naji amma tashi kaje kayo sallama tukunna," Nawaz ya mik'e ya fita yaje yayo sallama, ta amsa masa sannan ya shigo ya zauna akan k'afae Hibbah yace "aunty Dan Allah ki cigaba da yi mana irin wannan abincin yayi dad'i," Hibbah ta kalleshi tace "da gaske daddy yace girkina da daddy Nawaz?" Nawaz ya d'aga Kai "eh aunty yace da dad'i," tace "Nawaz ai dole na cigaba da yi muku irin wannan abincin," Nawaz yayi ihun murna "yeeeh zamu dinga cin abinci me dad'i," Hibbah ta d'anyi dariya tana kallon yarda yake murna tace "daddy ya fita ko yana parlor?" Nawaz ya mik'e "bara na duba," ya fita jimawa kad'an ya dawo "aunty baya nan ya fita," Hibbah tace "yauwa Nawaz," ta mik'e zata fita Nawaz yace "aunty ina zaki?"
"Zan wanke kayan aka b'ata ne Nawaz" "Aunty idan kin gama zaki yimin assignment d'ina ran Monday zamu koma school," ta d'aga kai tare da fita.
Ta had'o kayan ta wanke ta gyara ko ina parlor ma tasa turaren wuta sai k'amshi ke tashi ta koma d'akin nata taga Nawaz ta tattaro littattafansa na makaranta ya barbazasu, tana zuwa ta shiga nunnuna masa yaron akwai k'ok'ari nan da nan yake fahimta, bayan sun gama Nawaz ya dinga yi mata shirme tana biye masa, yaje ya d'auko mata wani hotonsa ya ajiye mata a gefen gadonta wai yabata haka dai yayi tashirmensa har yamma.
Bayan tayi sallar la'asar ta shiga kitchen tayi musu dinner, ta koma d'akin tayi wanka ta canza kaya tana nan zaune akayi kiran sallar maghrib ta tashi tayi sallah. Shi kuwa Nawaz yana gani ta shiga kitchen ya fita wajen iliya mai gadi yana ball.