Sashe 2
Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Lami cikin bala'i tace "to karki ci din cikin waye?",
Burgima Rahmatu ta shiga yi tana cewa "ni wallahi bazan ci wannan abincin ba". Lami nasan Rahmatu fiye da kowa cikin sauri ta dagata tana cewa "haba Rahmatu ya zaki dinga burgima akan wani abinci, uhumm?" Cikin shagwaba da sangarta tace "to ni ki bani kudi na siyo alala a wajen Abu don bazanci wannan abincin ba". Cikin lallashi lami tace "don wannan ai mai sauki ne " ta kunto kudi a jikin zaninta ta bata "ungu jeki ki siyo kinji" karba tayi ta ruga da gudu tabar gidan.
Bangaran Hibbah kuwa tana fita ta nufi kasuwa dake can take kaiwa, bayan taje ta zauna a mazauninta mutane suka fara zuwa siye.
Sale driver ne yazo yana...........
*by*
*Mamyn Najmah*
[10/26, 9:21 PM] Maman Najma Author P1: 📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*RAYUWA* page 3⃣
*NA*
*MAMYN NAJMAH*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*DEDICATED TO AYSHA ALIYU GARKUWA*
*Na sami dukkan sakonku masoyan A.A Garkuwa, kuma in allah yarda zan cigaba da rubuta wannan littafin.*
Yana wangale baki ya karaso kusa da Hibbah zai zauna da sauri Hibbah ta mike tsaye tana binshi da wani mugun kallo tare da nunashi tace "Kai sale mene haka baka da hankaline zakake kokari goga jikin ka da nawa?",
Kallon ta yayi yana kuma wangale baki yace "haba Hibbah mene waike yaushe ne zaki gane nufina to mene don na hada jikina danaki." Mugun kallo ta buga mai tare da daukar farantin ta zata bar wajen. Hijjab dinta ya janyo da karfi, baya tayo sosai tare da farantin hannunta hakan yayi sanadiyyar subucewar faranti daga hannunta.
Ya kife sauran abincin rabi ya zube a kasa rabi kuma a jikinta, Rahmatu da a gabanta akayi komi ta tsaya tana dariya don tasan koba komai yau Hibbah saita nadu a wajen inna .
Ita kuwa Hibbah iya kuluwa ta kulu zuciyarta tana mata wani irin radadi cikin zafin nama ta juyo tana binsa da mugun kallo tare da cewa "wallahi kaji Na rantse sale sai ka biya kudin abincin nan daka zubar don bazan dauki asara ba, don nima idan na koma ba afuwa Inna zata min ba bazaka jamin duka a banzaba wallahi" cikin zafin rai take magana.
Dariya sale yasa yace "ai nasan da haka kudin abincinki zan biyaki na nawa ne?" Kallon shi tayi a kaiksice tace "Na murtala shida da rabi ne",
Hannu ya zura a aljihunshi ya ciro Dari biyar ya mika mata, kallon shi tayi cikin tsiwa tace "mene na wani bani dari biyar bayan kasan bani da canji." Juyawa yayi yaga hankalin mutane baya kansu ya kalli Abu kawar Hibbah yaga bata kallonsu. Hibbah ta kalleshi duk yayi yanayin mara gaskiya sai wani waige yake tace "malam ni ka samu canji ka bani kudi na ka wani tsaya kana waige waige." Murmushin mugunta sale yakeyi yana kallonta yace "karbi kudin da daddare zanzo dandali cin gyda kafin nan kin samu canji saiki bani."
"Ni ban yarda ba kuma bazan karba ba kawai kaje ka samo ka bani ina zaune anan" Hibbah ta maida mai da amsa cikin sauri. "To yanxu ya kike so nayi kinsai dai babu wanda zai bamu canji a kasuwar nan koh?" Sale ya fada yana kallon kirjin Hibbah yana lasar lebe. Tsaki Hibbah taja "kaje ka samo ina jiranka a wajen Abu " tana gama fada masa ta tsugunna ta kwashe robobin da murafi tare dayin gaba, wajen da Abu ke zaune ta karasa ta zauna.
Da gudu Rahmatu ta kwasa tayi hanyar cikin gari. Da ido Hibbah ta bita cike da tsoro don tasan tana zuwa gida zata fadawa inna.
Abu ta kalleta tace "Hibbah ni a ganina dama ki karbi kudin kamar yadda yace da daddare idan mukaje dandali saiki bashi". Hibbah tayi shiru kafin tace "wallahi Abu ina tsoran sale ne kwata kwata na tsameshi na tsani halinshi bana son yana kulani KO kadan, shiyasa fa bana son ya dauki abincina, kina gani kullum don kar magana ta hada mu yasa bana karbar kudin abincinsa amma shi ki duba yarda kullum yake wani shige min." Ta fada cike da damuwa,
"Don kin tsane shi bazai hanaki karbar hakkinki ba a wajensa, sannan ki duba fa kigani kullum sai Inna lami ta dakeki akan bakya cika mata kudinta, gashi yanxu Rahmatu taga lokacin da ya zubar da sauran abincin na tabbata saita fadawa Inna kuma idan baki karbi kudinnan ba baki da wata sheda ta kare kanki a wajenta gwara kawai ki amsa." Shiru Hibbah tayi tana nazarin kalaman Abu tabbas gaskiya ta fada mata gwanda ta karbi kudin nan data komawa Inna gida ba sauran kudi. Kuma tasan tunda Rahmatu ta ganta tasan saita fadawa Inna.
Hibbah tace "to idan na karba yazo da daddaren kuma ba canji fa?" Abu tace "karki damu saina anso mana wajen gwaggo nasan tana da canji" Hibbah tace "to shikenan idan zamu tafi na amsa" mikewa Abu tayi tare da cewa "tashi mu tafi alalan ya kare ai" mikewa Hibbah itama tayi ta dora farantinta aka sannan ta karasa kusa da inda sale yake tace "Zan tafi gida ka samo canjin?", "ban samu ba gashi na amsa ko gobe ne idan yau banzo dandalin ba" sale ya fada yana kuma kallon girjinta tare da miko mata kudin.
"Ni dai wallahi babu ruwana idan na kaiwa Inna kudin tace baza ta bada canji ba" ta karba kudin, shi kuwa sale ya sha'afa da kallon lips dinta, jin bai amsa ba ta kalleshi tace "kadai ji Na fada" sale yace "ai ba komai saina fanshe" kallon mamaki Hibbah tayi masa tace "ka fanshe da me" cikin sauri yace "a'a ina nufin bakomai idan ma ta hana canjin."
Juyawa tayi taja hannun Abu suka tafi, muryar sale sukaji yana cewa "saina zo" basu waiga ba suka yi.............

*RAYUWA* page6⃣to7⃣
*NA*
*MAMYN NAJMAH*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*DEDICATED TO AYSHA ALIYU GARKUWA*
*الله اكبر الله اكبر الله اكبر*
*لااله الا الله، الله اكبر الله اكبر ولله الحمد*
*الله اكبر كبيرا*
*والحمد لله كثيرا*
*و صبحان الله بكرة و اسيلا*
_*Ina bawa mabiya littafin RAYUWA hakuri kasancewar yau zan dakata da yin typing sai bayan sallah idan Allah ya kaimu zan dora, allah yasa muyi sallah lafiya mugama lafiya.*_
_*Au na manta da sakon Aunty na ban fada muku ba, Aunty AYSHA ALIYU GARKUWA tace bayan sallaha karku manta ku tawo mata da nata naman😜.*_
Haka Hibbah ta yini tana kuka da tunanin yarda zata cigaba da *RAYUWA* a gidannan cikin wahala da ukuba. Sallah ce kawai ta tasheta daga inda take, alwala tayi tai sallar azahar sannan tayi la'asar kasancewar taji anata kiraye kirayen sallah bayan ta idar ta zauna ta rika kwararo addu'a tana kaiwa mai sama kukanta, addu'a take yi amma hawaye na zuba a idanunta. KO abinci ranar bata iya ci ba saboda tsantsar damuwar dake damunta na rabata da mahaifiyarta gatanta da akayi.
Umma kuwa suna zuwa gida Yaya Habu ya fadawa su gwaggo komi, sun firgita kwarai dajin kazafin da akayiwa 'yar tasu, ko kadan saki bai daga musu hankali ba saboda sunsan yanayin halin da 'yar tasu take ciki a gidan mijin nata. Kuma sun goyi bayan Yaya Habu daya tafi da ita cen Bunkure din zatafi samun nutsuwa sannan data gama iddarta idan Allah ya kawo miji tayi aurenta. Nan sukayi musu sallama suka huce.
Da daddare bayan sallar isha'i Hibbah na kwance a dakin ummanta zazzabi ya rufeta sai rawar dari take yi. Rahmatu ce tashigo dakin tana cewa "ke Hibbah kije sale driver na kiranki, cikin rawar baki Hibbah tace "Dan allah Rahmatu anso masa canjinsa wajen Inna, zazzabi ya rufeni bazan iya tashi ba." Harararta Rahmatu tayi "lallai ma ni zaki aika? Shima din abinda yasa kika nazo kudi ya bani amma badan haka ba babu inda zani, mtwss" ta karasa maganar dayin tsaki tayi ficewarta.
Tana fita dakin Inna ta shiga tana shan rake bako sallama ta haye kan gadon innar ta cigaba da shan rakenta, inna ta kalleta tace "me sunan baba me kike shane haka?" Shiru Rahmatu tayi bata amsa ba ta cigaba da shan raken. Inna ta kalleta tace "au saboda kar nace ki sammin shiyasa kikayi min shiru koh Rahmatu?" Cikin gajiyawa da maganar Rahmatu tace "ai dama nasan sai kince na sammiki bayan kuma kena fara cewa ki bani kudi na siya kika hanani" ta fada tana kuma gyara zamanta akan gadon innar.
Cikin yanayin lallashi Inna tace "haba me sunan baba ai ina baki kina siya, ki sammin kadan zansha." Turo baki Rahmatu tayi tare da mika mata tace "to gashi nan karki sha min dayawa, inkika sha da yawa allah saikin sai min wani," inna ta amsa tana cewa "bazan ma sha da yawa ba." Bantara tayi tasha zata kara, Rahmatu tayi saurin cewa "wallahi inna kika Kara saikin sai min sabo" mika mata inna tayi tana cewa "ai raken nakine akwai zaki, wa ya baki kudi kika siya?" Bata kalli inna ba tace "Sale direba ne yazo wajen Hibbah, shine zan shigo ya ganni yace na kira masa ita nace bazani ba shine ya dauko hamsin ya bani." Inna ta gyara zama tace "wai mene a tsakanin su ne dazuma kince ya bata Dari biyar a kasuwa, don ya barar mata da abinci kuma nidai nasan abincin dana dora mata na dari uku ne. Kinga kudin ma data zo tana ta uwarta bata ma yimin bayani ba ta bani kudin duka." Rahmatu tace "toni ina Zan Sani ni dai nasan kawai yana yawan kulata ko kuma yace zai tabata ita kuma ta haushi da masifa." Tana gama fadin haka ta mike tare da cewa "ni na tafi dandali" inna tace "sai kin dawo amma kafin ki tafi ki shiga ki kira min wannan shegiyar yarinyar tana nufin dan uwarta tabar gidan shine yau bazata fitar min da gyadata ba." "Inna tana can bata da lafiya" Rahmatu ta bawa inna amsa tana fita daga dakin. Murmushin mugunta inna tayi tare da bin bayan Rahmatu.