← Book details Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 54

Sashe 4

Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

A can gida kuwa bayan umma ta sauke tukunyar daga kan murhu ta dauki tukunyar takai kofar inna tare da cewa "Inna gashinan na gama." Inna Na cikin daki bata ce mata komi ba tayi banza da ita. Umma ta saba da hakan don haka bata damu ba taje daki ta dauko roba ta ajiye a kusa da tukunyar.
Buta ta dauka ta shiga bayan gida ta fito ta daura alwala ta shiga daki, sallah tayi bayan ta idar ta zauna tana kaiwa ubangiji kukanta, bayan ta shafa ta zauna ta cigaba jan carbi.
Muryar malam taji yana kwalla mata kira cikin fada "ke Aysha, Aysha ina kike fito munafika maci amana." Cikin sauri Umma ta fito tana cewa "malam lafiya.........?" Bata Ankara ba taji saukar yatsun malam a fuskarta. Rike kuncinta tayi tace "malam me nayi don Allah ka fada.........." Kuma katseta yayi da wani gigitaccen mari Wanda yayi sanadiyyar faduwarta kasa, binta yayi ya cigaba da dukanta baji ba gani yana binta da muggan kalamai "Allah ya isa tsakanina dake Aysha bazan taba yafe miki ba, kin cuceni kuma sai kinga sakayya, ki rasa dame zaki saka min saida bin maza" yaci gaba da dukanta. Lami wadda taji duk abinda ya faru tana daki tanata dariya domin kuwa tarkonta ya kama malam, da gudu ta fito daga dakin ta karaso kusa da malam tana cewa "haba malam dukan mace kamar wani mara hankali me tayine malam?" Bai saurareta ba ya cigaba da bugunta. Itako Aysha ganin babu mai cetonta yasa dakyar ta mike ta koma dakinta da gudu. Yana kokarin binta malam Habu wan Aysha daya shigo ya tareshi da sauri "haba malam Mukhtar me yayi zafi haka dukan matarka da hannunka? Da hankalinka kake dukan mace ai fada ya dace kayi mata ba duka ba." Mugun kallo malam Mukhtar yayi masa yana cewa "eh ai dama dole kace nayi mata fada tunda kanwarka ce koh? Kuma na tabbata kasan irin tarbiyyar da kuka bawa 'yarku don haka kadau keta ku tafi na saketa."
Ba malam Habu kadai ba har umma dake daki saida ta tsorata, ta fito a rikece tana kallon su malam Habu yace "saki fa kace malam Mukhtar me yayi zafi haka? Ai idan tayi maka wani laifi ni ya kamata kasamu sai mu magance matsalar a sasanta komai, bawai kadinga dukanta ba daga karshe kuma kace ka saketa ba" malam Mukhtar ya kalleshi cikin bacin rai yace "a sasanta me? Ai babu a abinda za'a sasanta kawai ka dauki fasikar kanwarka ku barmin gida" cikin mamaki Umma ta dafe kirji tace "fasika fa kace malam, Inna lillahi wa Inna ilaihirra ji'un allahumma ajirni fi musibati wa akhlifnii khairan minha." Umma ta fada cike da damuwa, malam Habu ya kalleta ya kalli malam Mukhtar yace "Mukhtar fasika fa zina fa kenan, ka nufin matarka na aikata zina? Ka ganta da idanunka ko kuwa zargi kakeyi Mukhtar?" Cikin hayayyakowa malam Mukhtar yace "eh ai dama baza kaga laifinta ba tunda kanwarkace jininka ce, ni dai na gama magana ka dauki kanwarka Ku barmin gida". Lami data nuna damuwa a fuskarta a badini kuwa ta shiga tsananin farin ciki tace "fasika malam gaskiya bazan boye maka ba don ko jiya naga inuwar wani katon mutum da daddare ni wallahi dana ganshima ba karamin tsoro naji ba ashe gurinta yake zuwa" malam Habu kallonta yake cikin mamaki yake kallonta, ita kuwa umma rushewa tayi dawani kuka mai ban tausayi tana cewa "wallahi malam sharri akayi min tunda nake ban taba aikata zina ba kayi bincike kafin ka yanke hukunci......." Katseta yayi da cewa "wane bincike zanyi bayan gashi nasan gaskiya babu wani bincike da zanyi kawai ki fitar min a gida na sakeki......." Furucin malam yayi daidai da shigowar Hibbah, sallama tayi amma babu wanda ya amsa ta kallesu dukansu basa cikin nutsuwa.
Lami tadanyi murmushi tace "malam Saki nawa kayi mata?" Malam yace "saki daya nayi mata" saki daya kuma malam fasika ce fa koka manta, kenan zaka dawo da ita nan bada dadewa ba." Lami ta tareshi da fadin haka. Malam yace "wa? Allah ya tsareni da kuma zama da ita, dama can saboda ban samu haihuwa bane yasa Na aureta yanxu kuwa allah ya azurtani. Ni ina ma shakku Anya wannan yarinyar jini nace kuwa?"
Cikin tsananin kuka umma tace "wallahi 'yarkace malam jininka ce" ta juya ta kalli lami cikin kuka tace "Yaya kiji tsoron allah ki rinka tunawa da mutuwa da kwanciyar kabari, kinyi min sharri akan abinda ban aikata ba kisani sai allah ya bi min hakkina akan abinda kikayi min..........." Kukane yaci karfinta. Hibbah ce ta matso kusa da umma itama hawaye na bin fuskarta, ta shiga sharewa umma hawayenta, rumgume ta umma tayi tana cewa "ya allah ga amanar 'yata nan, Allah ka kareta daga dukkan sharri na mutum kona aljan Allah ka tsareta daga dukkan abinki kasa tafi karfin makiyanta" ta fada cikin kuka. Malam Mukhtar yace "ai da 'yarki zaki tafi baza ki barmin ita a nan ba" cikin sauri lami ta katse shi "a'a malam ka barta a nan kanaso tajene ta kwaso irin halayenta?" Malam yace "ai bana zaton 'yata ce shiyasa gara ta tafi da ita kawai" "a'a malam gara ka barta anan koba komai zaka tserar da ita daga halakar fadawa zina"
Malam Habu ya kalli Umma da Hibbah yarda suka kuma kamkame juna suna kuka sai yaji sun bashi tausayi, yace "Aysha taso mu tafi gida kiyi hakuri kinji" cikin kuka mai ban tausayi ta kalleshi tace "Yaya tayi min sharri ta rabani da farincikina Hibbah, yanxu kowa a garin nan kallon fasika zai rika yimin alhalin ni ban taba zina ba......." Wani kukan ta kuma saki tana kuma rukunkume Hibbah.
Hibbah kuwa hankalinta ne yayi mugun tashi ta shiga tunani _zina? Umman nawace ke aikata zina? Me yasa Inna lami bazata taba kaunar ummana ba? Me tayi mata a *RAYUWA* da har ta tsaneta haka_ Malam Habu ya katse mata tunani da cewa "kiyi hakuri Aysha ki saka aranki wannan itace kaddarar da allah ya aiko miki kiyi kokarin cinye wannan jarrabawar, *RAYUWA* ce wata rana sai labari kinji? Kuma maganar mutanan gari kuma dama ni na yanke shawarar zan tafi dake can bunkure ki zauna, yanxu idan mun shiga gida nayiwa su gwaggo bayani sai mu huce" Kai ta daga masa sannan ta mike tana kallon Hibbah. Murmushi ta kakalo tace "Hibbah zan tafi nasan zaiyi wuya na dawo nan kusa, Dan allah ina rokonki Hibbah ki kula da kanki ki zamo mai hakuri da juriyar duk abinda zaayi miki. Nasan zaman daza kiyi a gidannan sai yafi na baya kunci da wahala, nasan kina da hakuri to ki Kara akan wanda kike dashi kinji allah yayi miki albarka yasa kifi karfin makiyanki ya kareki daga dukkan mugun mutum." Rike hannunta Hibbah tayi cikin kuka tace "Umma Dan allah karki tafi ki barni wallahi idan kika tafi Inna kasheni zatayi don allah ki zauna" ta kuma fashewa da kuka. Umma cikin hawaye tace "kiyi hakuri Hibbah mahaifinki yana zargina da aikata zina, sanadiyyar haka ya sakeni kuma koda bai sakeni ba aure da zargi bazai yuyu ba. Ki hakuri Hibbah Zan tafi amma zan rinka zuwa dubaki." A hankali umma ta zare hannunta daga na Hibbah sannan tace "kirike addu'a itace makamin mumini, karki manta da azkar na safe da maraice sannan alwala kafin ki kwanta kamar yarda kika saba, da yardar allah saikinfi karfin duk wani mai nemanki da sharri." ahankali Umma ta rinka ja da baya tana tafiya, da gudu Hibbah tazo ta rumgume ta tana rokonta karta tafi.
"Kiyi ki barmin gida kafin nadawo", malam Mukhtar ya fada yana fita a gidan. Ita kuwa lami guda ta Saki tace "saika tattara kanwarka Ku kara gaba ai dama duk wacce tayi gigin hada miji dani sai taga abinda yafi haka", ta fada tana kuma shekewa da dariya. Mamaki da al'ajabin abin ne ya hana malam habu magana ya kalli Umma yace "kiyi hakuri mu tafi yamma nayi." Haka suka rabu su biyun duka suna kuka.

Bayan fitar su umma haka Hibbah ta zauna tanata rusa kuka mai ban tausayi, lami ce ta kalleta ta tabe baki tace "ni bani kudin sana'ata, gara ma ki daina yi mata kuka don kema kin kusa barin gidannan." Mika mata kudin tayi, fizgewa lami tayi tai gaba. Ita KO Hibbah saboda tashin hankali tama manta bata fada mata akwai canjin sale ba.............

*by*
*MAMYN NAJMAH*
[10/26, 9:22 PM] Maman Najma Author P1: 📝🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓

*RAYUWA* page 8⃣to9⃣

*NA*
*MAMYN NAJMAH*

🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓

*DEDICATED TO AYSHA ALIYU GARKUWA*

*ina neman afuwarku na kuskuren danayi a last page na, fatan za'a yimin uxuri*

*Ina mika sakon barka da sallah ga dukkan masoyan aunty na _AYSHA ALIYU GARKUWA_. Ina kuma baku hakuri na jina kwana biyu da banyi typing ba, abubuwa ne sukayi yawa don ko na happy sallah bansamu damar yi muku ba. Masha Allah yanzu komai yayi normal kuma insha allah zaku cigaba da jina. ~Aci gaba da gashi~.*
Chapter 4 · 0% Book details