Sashe 22
Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
Sun isa gidan aunty inda ta tarbe su cikin farin ciki suka rumgume juna suka zube kan kujera suna gaisawa, Aunty ta cika musu gaba da abinci kala kala sunaci suna ta hira har lokacin sallah yayi suka tashi suka gabatar da sallar.
Ba wani aiki auntyn take yi ba a gidan daga gyaran d'akin mijinta sai girki don haka suka kuma zama a parlor suna ta hira, sallamar su sagir ce ta katsesu suka amsa musu, Hibbah ta gaishe da sagir dana bayan shi dan bata ga fuskarsa ba. Jabeer ya saki sassanyar ajiyar zuciya tare da amsawa muryarshi data jini ne ta gane wanene ta d'ago kanta duka kalli juna, Jabeer ya sakar mata wani murmushi mai cike da ma'anoni.
Ta kawar da kanta kefe suka cigaba da hira da aunty ita kuwa aunty ta fahimci abinda ke tsakaninsu, ta taya Hibbah murna sosai ta kuma yi farin ciki da hakan ta mik'e ta nufi d'akin mijinta ta had'a masa ruwan wanka tare da fito masa da kaya marar nauyi, shima sagir biyota yayi donya watsa ruwa.
Parlor'n ya rage daga Jabeer sai Hibbah sai kuma Nawaz daya ke ta wasanshi jikinta, Jabeer ya kalleta yana murmushi "Hibbah ba magana," ta sunkui da kai "ai na gaishe da ku," "Hibbah gaisuwa daban maganar da bake so kiyimi da ban," ta d'ago tad'an kalleshi ta mayar da kanta k'asa don bata da amsar bashi, gani take yi kamar zai yaudareta tana yiwa maza kallon halinsu d'aya shima hankali zai buk'aci jikinta.
Ta kuma yin k'asa da kanta yace "Hibbah ki yarda dani wallahi inna k'aunarki kuma ni auranki zanyi pls ki karb'i buk'atata," Hibbah dai bata ce komai ba sai wasa da take yi da zuben hannunta, Jabeer yayi suru kawai yana kallonta, ita kuwa Hibbah duk a takure take dan bata son yawan kallo yana takureta. Aunty ta dawo parlor'n tana dawowa Hibbah tace "aunty bara mu tafi yamma tayi," aunty ta harareta "me kike nufi? Wai yanxu zaki tafi?" Hibbah ta d'an karyar da kai "aunty daddy fa yana nan kinga bazai so kukai dare ba, ga girki ma da zanyi yanzu idan na koma," aunty tayi murmushi "to shikenan na karb'i uzurinki," Hibbah ta d'auki jakarta Nawaz ma ya mik'e "aunty zamu huce sai munyi waya," "to shikenan Hibbah na gode ki gaida min da Yaya," Jabeer yayi zaraf "Aysha mai zai hana na kaita tunda da mota a hannuna," da sauri Hibbah ta d'ago Kai ta kalleshi, aunty ta kalli yanayin Hibbah duk ta rud'e tace "ai kuwa da ka kyauta, kasan yanzu kafin ta samu mota ma aikine tunda yamma tayi," Hibbah ta kalle Aunty tayi narai narai da ido.
Jabeer yaji dad'in furucin aunty jiki na rawa yafita, Aunty tayi murmushi tace "Hibbah Jabeer yana sonki so na hak'ik'a me yasa bazaki karb'i tayinsa? Kullum idan yazo gidannan Bashi da zance sai naki," Hibbah ta kalli Auntyn ta "aunty bana k'i karb'ar tayinsa bane kawai ni inajin tsoran maza ne," "a'a Hibbah ba duka aka taru aka zama d'aya ba, kinga yanzu yana jiranki a mota, kaso mai sonka kinga shi aurenki zaiyi da kin k'arasa school amma dai kiyi tunani."
Hibbah tace "to shikenan aunty na gode," aunty ta bata wata leda bak'a cike da kayan kwalliya ta amsa tayi godiya. Aunty ta rakota har bakin motar ta bud'e mata kusa da Jabeer ta shiga suka tafi, a mota Jabeer sai janta yake da hira ita dai ba magana daga uhmm sai a'a, dayaga haka sai yayi ta jan Nawaz da hira har suka shigo unguwar nan ne ma dai tayi ta nuna masa hanya.
A bakin gate d'in gidan yayi parking Hibbah kanta na k'asa tace "na gode," Nawaz ya bud'e motar ya fita da gudu ya shiga gida. Jabeer ya kalleta yace "Hibbah maganar mu fa?" "Sai na fad'awa aunty," ya kalleta "nasan Aysha zata bani da yardar Allah," "Allah yasa," ji sukayi an bud'e k'ofar ya janyoh hannun Hibbah tare da sinka mata mari "uban me kikeyi a motarsa?" Hibbah ta d'ago kai ta kalleshi, cikin tsoro ta furta " *Faruq* kaine yaushe ka dawo?" "Bansani ba, me kikeyi a motarsa nake tambayarki," Jabeer cikin zafin yace "kai dallah ya isheka kawai daga ganin yarinya muna tare sai ka shiga dukanta," "na daketa d'in, ta maka waye ni a wajenta ta fad'a maka matsayinta," ya kalli Hibbah dake rik'e dakuncinta yace "ke ki fad'a masa matsayinki a gidan mu," Hibbah tayi shiru wasu zafafan hawaye nabin fuskarta "tunda ke baxaki fad'a ba ni bara na fad'a, Hibbah ba kowa bace a gidan mu face 'yar aiki kuma baiwa!!!" Kalmar tayiwa Hibbah zafi da gudu tayi cikin gida tana kuka.
Jabeer ya cilla masa wani mugun kallo "ba baiwa ma ko wace Hibbah ina sonta ina kuma k'aunarta a hakan Zan aureta," yana gama fad'in haka ya shige motarshi ranshi a b'ace ya figi motar. Faruq kuwa ya kasa nutsuwa yana tunanin koya bita cikin gidan sai kuma ga koma motarsa ya had'a kansa da sitiyarin motar. Yana mamkin meya kawo ta gidan ya Faheem.
Hibbah kuwa tana shiga gida d'akinta ta nufa ta zube a kan gado ta shiga rera kuka, tana mai jin zafin abinda Faruq yayi mata ace a gaban saurayinka yayi maka wannan rashin mutuncin wannan wace irin *RAYUWA*ce? Ta kuma rushewa da kuka tana kuma tunano *RAYUWARTA* ta baya. Nawaz ne ya shigo rik'e da chocolate a hannunsa yana sha ya mik'o mata "Aunty kinga uncle ya bani chocolate," da sauri ta goge hawayen ta tana murmushi tace "to jeka sha Nawaz nima bara na shiga kitchen," ta mik'e ta nufi kitchen ta had'a musu dinner ta gyara kitchen d'in, tana gamawa taji ana kiraye kirayen sallah tayo alwala tazo ta gabatar da sallar, ta d'ebo abinci ta zauna suna ci ita da Nawaz sai shirme yake mata ita kuwa duk abin da Faruq yayi mata ne yake damunta har ta kwanta tana tunanin abin.