← Book details Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 54

Sashe 18

Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai Ana saura one week su koma school da yamma aunty taje ta d'aukota, tun a bakin gate Hibbah ta fara ganin taron Jama'a amma mafi yawansu mata ne, ta kalli Auntyn ta tace "Aunty me akeyi a gidan naga taron mutane," aunty tayi murmushi tare da cewa babu komai Hibbah," ita dai Hibbah bata yarda ba duba da k'unshin dake hannun Auntyn, driver ya shiga cikin gidan tare da yin parking, suka fito duk harabar gidan 'yan mata ne 'yan gayu masu ji da Kansu gefe guda kuma ga manyan mata a zazzaune akan fararan kujeru.
Suna doso cikin gidan 'yammatan suka shiga ihun Amarya Amarya, kan Hibbah ya kuma d'aurewa ta kalli Auntyn ta sai taga ta kawar da kai tana murmushi taja hannunta suka shiga cikin gidan, a parlor ta kuma ganin tawagar wasu matan ta kuma gani nan ma suna shiga suka shiga yi mata ihun Amarya, daga can gefe ta hango Saudat, Safiyya da wata da bata Santa ba sai wani yaro da bazai huce shekaru uku ba d'an kyakykyawa yana ta wasansa.
Ta gabansu suka zo hucewa zasu hau stairs taji wannan Wanda bata sani d'in ba tana tambayar aunty "Aysha wannan kuma wace naga bansanta ba," aunty ta d'an kalleta tace "k'anwata ce," tana gama fad'in haka suka hau stairs, Safiyya ta tab'e baki tace "uhhmm aunty Kausar 'yar aiki ce fa aunty ta maida ta kamar wata 'yar uwarta, wallahi abinda aunty take yiwa Hibbah komu bata yi mana," Saudat ta harareta tace "nifa banga wani abu ba don ta taimaka mata, to ke ina ma ruwanki dan ta d'auketa a matsayin k'anwa?" Rama hararar Safiyya tayi tace "aike dama sam baki da kishi wallahi, ni haushinki nake ji ki rasa dawa zakiyi k'awance saida 'yar aiki" Kausar ta rik'e baki "y'ar aiki? Itace ta koma haka kamar wata 'yar wani da wata, ni wallahi ji nake ma k'anwar Sagir d'ince," safiyya ta tab'e baki tace "hmm ni fa aunty abin da yake kuma bani haushi school d'in mu fa aunty ta kaita allah ya taimakeni ma ba class d'in mu aka kaita ba amma islamiyya ajinmu d'aya wallahi ga yarinyar da shegen farin jinin tsiya" Kausar ta zaro ido waje "har ta samu wannan matsayin, lallai da matsala" "to wai ku ina ruwanku," Saudat ta fad'a tana mik'ewa tabar wajen, Safiyya ta tab'e, Kausar tace "gaskiya Aysha bata kyauta ba 'yar aiki ta maida haka, to me momy tace," Safiyya ta d'auki wayarta ta fara dannawa tace "ai duk bakinsu d'aya," Kausar ta jinjina kai.

Aunty kuwa suna hawa d'akinta suka nufa a bakin gado suka zauna ita dai Hibbah so take ta tambayi aunty me akeyi a gidan, ta d'an sunkuida kai kar k'asa tace "aunty dan allah ki fad'a min me akeyi a gidan nan naji anata ce miki Amarya, ko bikin ki akeyi aunty kike b'oye min," aunty ta k'araso kusa da ita da wata Leda babba a hannunta ta zube a gado tare da zama a kusa da Hibbah ta rik'e hannun Hibbah tace "kiyi hakuri my Hibbah abubuwa ne sukayi yawa shiyasa banma zo da wuri na d'auke ba kuma baki Sani ba, amma kiyi haku..........." Hibbah tayi saurin rufe mata baki da hannunta tace " haba aunty hakuri fa kike bani ni wace? Wallahi ni aunty ba laifi kika yi min ba ai abin farin cikine, yau aka fara bikin?" Girgiza Kai aunty tayi tace "a'a Hibbah d'azu aka ma d'aura aure nima da k'yar momy ta barni nazo d'aukarki shima saida nayiwa sagir waya na tambaye shi," Hibbah ta d'anyi kalan tausayi "amma aunty shine baki zo kin d'auke ni ba," aunty tace "kiyi hakuri Hibbah abubuwa ne sukayi min yawa wallahi ko zama bana samun damar yi shi kanshi Adamu baya zama shiyasa ban turo shiba, amma ai yau za'ayi dinner amma sai an Fara kai Amarya tukunna," Hibbah tace "to shikenan nan aunty Allah ya sanya alkhari," "ameen" aunty ta fad'a tare da janyo ledar ta shiga fito da kayan, material da lashe sai kuma atampa had'ad'd'u anyi musu d'inkin zamani a goge suke sai wani abin d'auri kalar kayan yayi Kyau, sai takalma da pulse duk kalar abin d'aurin.
Hibbah ta shiga d'agawa cikin happy tana ta yiwa aunty godiya, aunty ta kalleta cikin nuna tausayi tace "Hibbah kiyi hakuri na yanke wani hukunci ba tare da saninki ba," Hibbah ta ajiye kayan ta juyo tana kallon aunty "aunty ai duk abinda kikayi daidai ne ni a wajena, kuma komai kikace nayi zanyi miki shi aunty ke uwace a wajena," aunty ta shafa gefen fuskarta tace "kalamanki Hibbah suna sani nishad'i," Hibbah tayi murmushi aunty ta d'ora "Hibbah kinga yanzu aure zanyi kuma ni bazan iya barinki a gidan nan ba saboda kinga Faruq ya kusa dawowa kuma nasan halin Faruq tunda yace saiya kusance ki nasan zai aikata. Ya Faheem ya dawo daga abroad wata biyar dasuka huce kuma ya koma gidansa dake Nasarawa GRA, yana samun matsala da Kausar matar sa, aikin banki take idan ta fita tunda safe bata dawowa sai dare Bashi da wanda yake kula da gidan kullum cikin yawon restaurant yake yana ciyo abinci, ga yaronsa Nawaz babu mai kula dashi saidai kullum idan ya dawo daga school a wuce dashi gidan k'anwar Abba," aunty ta dan numfasa "shine ya nemi shawarata akan yadda zaiyi donshi ya gaji, ni kuma kawai nace masa ya d'aukeki nasan zaki kula masa da gida, Hibbah amma idan na takura ki barshi." Hawayen farinciki ne ya zubowa Hibbah ta rumgume aunty tana cewa "nayi dacen uwa mai kaunata, aunty zaki bar gidan nan ki tafi gidan mijinki amma ke tunaninki yarda zaki tserar min da mutuncina, wallahi aunty bani da kamar ki a duniyar nan banda bakin gode miki na gode allah ya Baku zaman lafiya, kuma aunty nayi miki alk'aqarin kula masa da gida." Itama aunty rumgume ta tayi tana mata godiya sund'au lokaci a haka, momy ta shigo take cewa aunty ta shirya za'a tafi da ita, nan ta mik'e tayi wanka tana fitowa tace Hibbah ta shiga ita kuma aunty ta shiga shiryawa wata atampa ta fito musu da ita iri d'aya tayi musu da Hibbah, bayan Hibbah ta fito itama ta shirya sunyi kyau sosai. Mammy (mahaifiyar Kausar) itace tazo ta fita da aunty, hannun aunty rik'e Dana Hibbah har fito harabar gidan a mota aka sa Aunty su mamy suka shiga. Mamy tacewa aunty "Aysha wace aminiyar taki tazo mu tafi," aunty da kanta ke rufe tace "mamy Hibbah ce Hibbah zaku Kira min," aunty ta fito daga motar ta kalli Hibbah tace "kece Hibbah ko?" D'aga mata Kai Hibbah tayi, mamy ta bud'e mata kusa da driver ta shiga, driver yaja sai gidan Amary...........

*by*
*Mamyn Najmah*
[10/26, 9:22 PM] Maman Najma Author P1: 📝🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓

*RAYUWA* page2⃣6⃣

*NA*
*MAMYN NAJMAH*

🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓

*DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION*

D.B.W.A

*DEDICATED TO AYSHA ALIYU GARKUWA*

*Sis shema allah ya bada zaman lafiya ya barku tare har mutuwa cikin so da k'aunar juna, nan da wata tara muzo suna, allah kawo k'azantar d'aki ammafa bata rashin shara ba🤣🤣.*

Gida ne me kyau kana gani kasan gidan Amarya ne su daddy sun zuba dukiya a cikinsa, ita Hibbah sai kalle kalle takeyi tsarin gidan ya burgeta. Bedroom d'in aunty kai tsaye akayi da ita mamy da wasu 'yan uwanta sukayi mata fada akan zaman aure dake su daddy tun sanda aka d'aura aure sukayi mata nasu, saida 'yan Mata wanda zasu wajen dinner sukazo sannan su mammy suka tafi.
Wata budurwace tazo kusa da aunty ta yaye mata mayafi tare da cewa "Aysha ki tashi kiyi sallah kukan ya isa haka, kinga takwas ta kusa kuma wannan make up d'in yana da cin lokaci," aunty da idanunta sukayi jajazir ta kalli gefenta tace "ina Hibbah?" Wadda tai maganar tace "sun fita da Saudat da k'anwata fauzy," aunty tace "Dan Allah surry d'an sa a kirata ki fara yi mata kafin nayi sallah," surry tace "ok bara na Kira fauzy," aunty ta girgiza kai tare da mik'ewa ta nufi toilet d'in d'akin. Surry ta shiga dialing number fauzy, bugu d'aya ta d'auka "hello sis kun gama ne?" Fauzy ta fad'a a yayin da ta d'au wayar, surry tace "a'a Hibbah zakice mata tazo inji Aysha," "to kuna ina?" Fauzy ta tambaya, muna sitting room d'inta" fauzy tace "ok to bara na fad'a mata" fauzy ta kalli Hibbah tace "y'ar gidan aunty kije aunty na kiranki wai suna sitting room," Hibbah tai murmushi tace "au kema haka zaki ce?" Saudat da suke ta aikin make up ita da fauzy dayake su duk sun iya har kit ne dasu tayi karaf tace "to ba 'yartan bace," ta kalli fauzy "ai fauzy jelar aunty ma zakice mata ai, ga wanan na Aunty ne kayanta ne ta bari a d'akinta shine momy tace na tawo mata dashi," suka sa dariya Hibbah ta mik'e tare da d'aukar kayan ta nufi sitting room d'in, a lokacin su Hibbah har sunsa ankonsu na sisters baby pink yayi mata kyau sosai.
'Yan matane a zaune a parlor kowacce na kintsa kanta sunsha wani material sky blue sunyi kyau, ta k'arasa ciki inda yayar fauzy surry take tace "Yaya surayya gani" surry tace "zauna Hibbah Aysha tace a Fara yi miki," tace "to" ta zauna aka fara yi mata a zuciyarta tana jin k'aunar Auntyn ta na ratsata.
Aunty ma alwala ta d'auro tazo ta tada sallah saida ta fara gabatar da maghrib sannan tayi isha'i, ta kalli inda Hibbah take tayi murmushi ganin yarda Hibbah tayi kyau bata ce komai ba, saida aka gama yiwa Hibbah aka d'aura Mata d'ankwali tayi kyau kamar itace Amaryar sannan aka Fara yiwa Aunty, Hibbah ta sunkuyo da kanta daidai kunnan aunty tace "aunty ga kayanki nan inji momy, kuma aunty na gode Allah ya saka da alkhari ya barki da uncle sagir." Aunty taji dad'in add'arta a zuciyarta tace ameen a fili kuwa hararar Hibbah tayi, Hibbah cikin sauri tabar d'akin ta koma wajen su fauzy ba jimawa ma akace su fito ga motoci nan.
Chapter 18 · 0% Book details