← Book details Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 54

Sashe 38

Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Hibbah ni gani nazo tunda na aiko ki so kink'i fitowa ni d'in abin tsoro ne? Ni fa mutum ne kamar ki idan kuma kunya ce gaskiya tayi yawa" tayi shiru ta kasa magana "ok to ki saurareni ina so ne muyi wata mahimmiyar magana, kinsan so wani abu ne dake faruwa da mutum ba tare da zato ko kuma tsammani ba, munyi amanna da fad'ar Allah ta'ala shike jefa so a tsakanin d'ayanmu, na tsinci kaina a cikin wani hali mai wuyar fad'uwa may be ma kin fahimce ni kika basar, na nuna miki alamomi da dama ke mai hankali ce kinsan me nake nufi. Ina nufin kalma guda aure, idan banda shi bani da wata manufa a gareki, ni zan aureki amma da sharad'in abu biyu kina sona kuma kina ra'ayina don wad'annan abubuwan suke Gina aure."
Saura kad'an numfashinta ya d'auke wani abu taji ya harba a zuciyarta, duk lissafinta ya wargaje , wata sabuwa inji d'an caca ko da wasa bata tab'a tsammanin wannan furucin daga bakin Faheem ba, ikon Allah wai ita Hibbah 'yar aikin gudansa ba kazar kowa ba ita yake so? Ta yarda wani wajen Ana gudunka ana tsanarka wani wajen kuma sonka da k'aunarka ake yi, duk mutumin da ake yiwa hassada da k'yashi sai hassadar ta zama kamar taki ake barbad'a masa Allah abin godiya wai ita ke da matsayin da Faheem yace yanaso tabbas idan Allah bai wulakanta ka ba babu mai wulakantaka a duk fad'in duniyar nan, Inna lami taso lalata rayuwarta amma da yake Allah gafuru rahim ne sai yayi hanyar zuwanta birni don wasu su gyara mata *RAYUWA* mai makon a lalata, Allah ne ya bata wannan baiwar bamai iya ja da ikon sa.
"Ni zan aureki" kalmomin da suke mata yawo kenan, to me za tace abubuwa sun sark'e, "Hibbah" ya katse mata tunani, sai taji kamar ta fita da gudu don bayyana son nata gareshi zai dad'a nauyi da kunyarsa a tare da ita "Hibbah ya dai sai kin bani amsa ko muyi ta zama anan"
Ya rud'a mata k'wak'walwa ta rasa Kalmar da zata d'orata a harshenta. Ya zauna gefen gadon nan fa taji daddad'an k'amshin dake manne a jikinshi ya kuma tsumata, a yanayin da take jin Faheem ranta shi d'inne tsagwaronsa kamar yadda take ji a yawan lokuta idan sun had'u abin na yi mata yawo, ko me kenan? Zata iya fassara shi da kalmar "so" to amma anya wannan so ne, idan sone me yasa bata jinsa ga Jabeer ko Faruq, tunda suma suna sonta kuma dasu ne ta Saba mu'amalar soyayya musamman ma Jabeer. Yau dai gata ga Faheem mutumin da take d'ari d'ari dashi, hanyar da yabi ma bata so ta bi don kar suyi arangama saboda mutuncinsa da k'imarsa da take gani fiye da kowane mutum a rayuwarta.
"Haba Hibbah nifa bana son nayi ta magana a k'yale ni ni kad'ai bana jin dad''i, na jima a cikin k'alubalen sonki nayi k'ok'arin barin abin saboda wasu dalilai amma Hibbah na kasa jurewa, ba irin wannan son bane ake dak'ileshi yafin k'arfin hakan, na yarda da shi na kuma daina wani inkari cewa zan iya hakuri dashi domin ya wuce tunani na. Na sani kina ganin k'imata da girmana inason mu tafi a haka ki cigaba da ganin mutunci na, don ni hakan bazai hanani nuna miki k'auna ta zahiri ba tunda bawai wasa nake ba magana ce ta gaskiya ta aure, lokaci na k'urewa ko yaushe na k'ella ido na ganki sai abin ya tab'o min zuciya, bai kamata na b'oye miki ba don sai da amincewarki za muyi aure, kinga kuwa dole na nemi had'in kanki." Yayi murmushi gami da tsagaitawa ya maida numfashi "hmm Ana min rowar eyeball d'in nan har b'oyewa kikeyi don karna gani, Hibbah kinsan saboda ke nake dawowa gida da yamma, ko muryarki kawai naji sai hankali na ya kwanta, to ina zankai sonki bazai yuwu na iya daurewa ba ko kuma na cigaba da k'wauron baki ba, kinsan halayena nasan naki abinda na sani tuwo na maina za'ayi ki auri mai gidanki bana son tsaiko ki tare nan da sati biyu" ya dubeta "zuciyarki ta gamsu dani da shawarata?" Ta rufe idanunta da hannayenta magana dashi tana mata wahala.
Hmm shidai ya sani akwai sanshi a tare da ita, sai dai ta kasa fahimtarsa ko ta san itama tana sonshi d'in domin kunyar da take mishi ai alamune na akwai wani abu a can k'asan zuciyarta dake tirsasa jin kunyar. "Hmm amma dai Hibbah nan zansha wahala dake wannan kunyar taki tayi yawa amma akwai lokacin da zan rad'a miki wani abu sai kin manta da komai banda ni d'in nan" ya mik'e "inason tuwon masara da k'ashin rago miyar kukan nan, ga wannan ki bawa Isah ya siyo miki abinda kike da buk'ata." Kud'i ne ya ajiye a gefen gado.
"Zan fita ne tunda ruwan ya tsagaita" ya d'anyi murmushi ya kad'a Kai wannan yanayin bazai manta shi ba don a yanzu Hibbah ta zama mallakinsa, ya fice. Ta k'urawa kud'in idanu har yanzu k'amshin Faheem ke mamaye a d'akin, wani murmushi da bata san dalilin yinsa ba ya sub'uce a leb'enta, wannan shine k'auna da so Wanda yake daga Allah ne, ta dad'e tana son bincike da bin k'wak'wk'wafin abin amma sai zuciyarta ta dak'ile zargin, domin abune da take ganin har abadan bazai faru ba taya ma Faheem zaice yana sonta har ya aureta. Wannan ikon Allah da yawa yake, surar Faheem ta fara hango wa sai taga kamar abinda wuya cikakken mutum mai mutunci wayayye, shi komai nashi a tsare yake ta duba tsarin gidansa da yadda yake tafiyar da rayuwarsa. Ko Kausar matarsa ta isa ta firgita 'ya mace, idan banda ita da ta zauna da su ta karanci tsarin Kausar akwai abubuwa da dama data kuskure su bata kuma damu data gyara ba, wai kuma cikin ikon Allah ita d'in dai yake ra'ayi to me take dashi daya ja hankalinsa.
Kausar da Faruq sune k'adangaren bakin tulu, ita dai baza ta iya auren mijin Kausar ba kuma Yayan Faruq, don haka batun Faheem fa sai hakuri. Hibbah lallai Allah ya bata baiwa, wasu lokutan tana ganin Kausar takai k'arshe a sawun had'ad'd'un mata, wai me mace 'yar gayu irin Kausar yaya za'ayi ita ta burgeshi. A shirmen tunaninta kenan Allah sarki Hibbah rashin sani yafi dare duhu soyayya had'uwar jini ne, Faheem shi yaga abinda ya burgeshi harya yamutsashi da rud'ashi akan 'yar budurwar daya kira Hibbah. Sark'a Mai rikitaniya ya ta iya da Faruq idan yaji labari ga kuma bawan Allah Jabeer da ya mik'a wuya magana tayi k'arfi don kowa yasan dashi, furucinsa ya shiga ranta.
" _Hibbah ba zan tab'a wulakantaki ba har abada ni nasan darajarki, a yadda na ganki kinyi min kuma in sonki kamar raina shiyasa nake so muyi aure donki samu 'yancin kanki, Hibbah kina da daraja da baiwa amma sai mai hankali da nazari ne zai gane nasan ke baki san haka ba_"
Tana jin fitarsa saita samu...........

*Ga wannan ba yawa, banjin dad'ine ina barar add'ar Ku*

*by*
*Mamyn Najmah*
[10/26, 9:26 PM] Maman Najma Author P1: 📝🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓

*RAYUWA* page4⃣1⃣

*NA*
*MAMYN NAJMAH*

🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓

*DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION*

D.B.W.A

*DEDICATED TO AYSHA ALIYU GARKUWA*

*Fans naga dukkan sak'onninku na gode da addu'o'in ku Allah ya saka da alkhari, ya k'ara donk'on k'auna🤝*

Taro ne na mutane hud'u kacal don tattauna muhimmiyar magana domin kowanne a cikinsu zai bada gudunmawa da kuma taka rawar gani. Ya gyara xama yana kallonsu d'aya bayan d'aya don sun bada dukkan hankulansu don sauraronsa "kin bani mamaki Aysha zumunci fa babban abune Wanda zai iya Kai mutum aljanna ina so ku zama tsintsiya d'aya mad'aurinku guda dole ne ka sowa d'an uwanka abinda zaka soma kanka shine cikar imani, abubuwa suna ta faruwa ba akan idanuna ba saboda ni ba maxauni bane. Amma banji dad'in abinda kikayi ba Aysha kinsani komai lalacewar Faruq naki ne koda d'an ta'adda ne mai kisan mutane don haka ni d'innan zan tirsasaki dole kiso abinda yake so koda ke baki sonshi, indai har kinason ki gama da ni lafiya, ni banga dalilin zak'ewarki ba don Hana ruwa gudu kice bazai auri yarinyar da yake so ba, ke ba Wanda kike so muka amince kika aure shi ba? Waya hanaki? Haka ake rayuwar duniya idan jifa ya wuce kanka ya fad'a kan ko waye ko? Wato ke kinsamu shiya rasa. To bara na fad'a miki matuk'ar kina son shiri dani to karki sake saka baki a cikin maganar indai ba alkhari xaki fad'a ba wannan shine dalilina na Tara Ku anan gobe insha Allah zanje mu gana da marik'in yarinyar Alhaji Sani, Kai Faheem kai zaka wakilceni ka jagoranci komai babu shakka nasan baka da wata matsala. Next week zanyu tafiya kuma sati biyu zanyi insha Allah, kayi k'ok"arin gama duk wani shirye shirye za'a d'aura aure ne kafin Faruq ya tafi Germany Inda zaiyi contract d'insa bazai wuce wata biyu ba zai dawo idan ya dawo sai ayi binkin, shikenan idan babu Mai magana zaku iya tafiya"
Aunty Aysha ta girgiza kanta don ranta ya b'aci d'aci take ji a ranta tamkar ta rushe da kuka don bak'in ciki shikenan ta faru ta k'are, gashi Daddy ya d'ora mata laifi don shi daman a duniya babu abinda yak'i jini kamar ka tab'a Faruq to fa bashi da mak'iyi kamar kai, Faruq baya laifi a gurinsa duk abinda akace yayi zai k'aryata ya dinga bad'an da bashi da dalili wai ansa mishi yaro a gaba, wannan shine sanadiyyar lalacewar Faruq.
Chapter 38 · 0% Book details