Sashe 17
Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Washe gari k'arfe tara na safe suka d'auki hanyar Bunkure cike da tsaraba, Hibbah tana nunnunawa driver hanya har suka isa gidan, driver yayi parking a k'ofar gidan suka fito.
Da sallama suka shiga inna (babar Abu) tana iza wuta a bakin murhu ta k'araso kusa dasu tana yi musu sannun, ta shinfid'a musu tabarma suka zauna ta d'ebo musu ruwa Aunty tana gaisheta ita sam bata gane Hibbah ba saida ta gaida ta da taji muryarta sannan ta ganeta ido ta zuba mata tare da rik'e hab'a cikin mamaki tace "Hibbah kece haka? Ai ni Sam bangane ki ba lallai birni ta karb'eki kinga yarda kika koma tubarakallah kinyi kyau," Hibbah ta rufe fuskarta da mayafinta, ita kuwa Aunty murmushi tayi, inna ta d'ora da cewa "ai a wajen malam (mahaifin Abu) nake jin wai lami ta turaki birni aikatau kuma ta horeki karki kuskura kizo ganin gida, bayan sharrin da tayiwa Aysha kema tayi miko saida ta rabaki da 'yan uwanki, Kai wannan Mata allah ya rabamu da sharrinta." Aunty tace "Amen, inna dama munzo wajen ummanta ne na kawota zatayi hutu anan, tunda can an hanata zuwa." Inna tayi murmushi tace "allah sarki Hibbah kinyi dacen iyayen gida, amma fa saidai kunyi rashin sa'a don ummanta tana gama allah ya kawo mata wani Alhaji a birni, ubangidan malam yace yana sonta aka d'aura musu aure bayan bincike da malam yayi ya tafi da ita birni," Hibbah ta d'ago da sauri ta kalli inna ta kalli aunty.
Aunty ta d'an gyara zama tana kallon inna tace "inna a birni wane gari suke?" "Ai a nan garin kano suke da zama," inna ta bawa Aunty amsa, aunty tace "wace unguwa a birnin," inna ta d'anyi shiru kamar mai tunani can tace "wallahi 'yar nan na manta sunan unguwar amma da sa'idu zaizo daya fad'a muku sunan unguwar don jiya ma yaje ya kai mata sak'o," Hibbah tace "inna zai jima ne bai dawo ba?" Girgiza kai inna tayi tace "a'a don naga bai d'auki kayan aikinsa ba, yanxu zaki Ganshi ya shigo, bara na k'arasa iza wutar can," ta fad'a tana tashi, shiru sukayi can saiga sallamar sa'idu kallon su Hibbah yayi alamar rashin sani ta gaida Aunty, Hibbah ta gaishe shi itama saida tayi magana ya ganeta nan, inna ta k'araso tana cewa "yauwa sa'idu dama Hibbah ce tazo take son ka rakata gidan ummanta idan baka komai," sa'idu yace "ba matsala dama baba ya aikeni kasuwar su muje kawai," aunty tace "a wace unguwa take a kano d'in?" Sa'idu yace "a wai goran dutse," "ok" aunty ta fad'a tare da mik'ewa Hibbah ma ta mik'e, nan dai suka yiwa inna sallama aunty ta zube mata kud'i tayi ta godiya suka tafi.
Garin kano suka koma, unguwar goran dutse suka nufa sa'idu yana yiwa driver kwance har suka isa gidan, kallon gidan Aunty tayi da mamaki ta kalli driver tace "Adamu wannan ba gidan Alhaji Sani bane?" Adamu driver yace "eh shine hajiya..............
*by*
*Mamyn Najmah*
[10/26, 9:22 PM] Maman Najma Author P1: 📝🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓
*RAYUWA* page2⃣5⃣
*NA*
*MAMYN NAJMAH*
🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓
*DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION*
D.B.W.A
*DEDICATED TO AYSHA ALIYU GARKUWA*
*Wannan page d'in naku ne DA BAZARMU WRITERS allah ya k'ara had'a kanmu cikin k'aunar juna*
Mamaki fal a fuskar Aunty ta b'alle murfin motar suka fito Hibbah ta kalleta tace "Aunty kinsan gidan ne?" Aunty tana kallon gidan tace "gidan Alhaji Sani ne, shine babban yaron daddy," Hibbah ta kalleta Auntyn ta kawai bata ce komai ba, aunty ta cigaba "idan har Alhaji Sani shine mijin ummanki, to ta more don Alhaji sani mutum ne mai kirki shekarun baya matarsa ta rasu da d'ansa guda daya mallaka sanadiyyar accident da sukayi a hanyarsu ta dawowa kano daga Abuja, shi kuma a lokacin sunyi tafiya da Abba," Hibbah ta karyar da kai yanayin jin tausayi tace "allah yayi masu rahma."
Suka nufi gidan, gida ne madaidaici, mai gadin ya gane sa'idu don haka ya barsu suka shiga dayake ma irin almajiran nan ne yara, direct parlor'n gidan sa'idu yayi dasu suka shiga da sallama Umma tana zaune tana kallon sunnah TV suka shigo. Umma ta kalli k'ofa da sauri ta mik'e tsaye tare da zaro ido waje tana nuna Hibbah tace "Hibbah? Kece ko mafarki nake," Hibbah tana murmushin farincikin hawaye nabin fuskarta ta k'araso kusa da Umma ta rumgume ta, sai kuma ta saki kuka Umma ma hawaye nabin fuskarta, bata tab'a tunanin zata had'u da Hibbah a nan kusa ba. Ta d'agota daga jikinta tana share mata hawaye tace "kiyi shiru Hibbah ki daina kuka kinji," ta d'ago ta kalli Umma sannan ta maida kallonta ga Aunty tace "Umma ga Auntyna ita ce ta gyara min *RAYUWA*, inna lami da inna delu sunso b'ata ni sai allah ya taimake ni kuma aunty da momy suka taimakeni," Umma tana murmushi ta k'arasa kusa da Hibbah tana cewa "Auntyn Hibbah kiyi hakuri ban tare ki ba koh? Wallahi murnar ganin Hibbah ne yasa," ta k'araso ta rik'o hannun Aunty suka shigo cikin parlor'n aunty tace "lahh babu komi Umma ai tsakanin d'a da haifi sai Allah," ta zauna a kusa da Hibbah tace "Hibbah na yau sai kwana tare da Umma ko," Hibbah ta rufe fuska tana gyad'a kai. Shi kuwa sa'idu dama suna shiga ya nemi wajen zama.
Umma kuwa kitchen ta shiga ta d'ebo musu dangin su snacks da drinks ta cika musu gaba dashi, suka d'an ci suna ta hirar yaushe gamu, Hibbah ta Saki jiki sunata hira da umma ita kuwa aunty mamakin Hibbah take yadda ta Saki jiki tana ta zuba surutu tana bawa Umma labarin abinda ya faru tun bayan tafiyarta har taimakon dasu aunty sukayi mata. Aunty ta kasa jurewa tace "Hibbah wai dama haka kike da surutu?" Hibbah ta tad'an rufe fuska tace "Kai Aunty," aunty tace"eh mana gashinan sai hirarki kike da ummanki," Hibbah tayi murmush.
Umma ta kalli aunty tace "mun gode Auntyn Hibbah allah ya saka da alkhari, gaskiya naji dad'in abinda kuka yiwa Hibbah bamu da bakin yi muku godiya Allah ya bar zumunci." Aunty tace "ameen Umma dama na kawota ne zatayi hutunta anan idan sun koma zan turo driver ya d'auketa," Umma tace "to shikenan nan auntyn Hibbah Allah ya kaimu," aunty ta mik'e tana d'aukar jakarta tace "Umma ni Zan tafi sai yazo d'aukar Nata" ta kalli Hibbah tace "Hibbah ni Zan huce sai Adamu yazo d'aukarki idan kuma na samu time zan zo" Hibbah ta mik'e tace "to aunty na gode allah ya saka," aunty ta d'an harareta. Umma tace "mun gode fa Aysha kiyiwa momyn naku godiya kafin muzo, ki gaida gida allah ya tsare" umma ta rakota har bakin k'ofar parlor tana ta yi mata godiya Aunty har ta Fara jin nauyi ma.
Har wajen mota Hibbah ta rako Aunty, sannan sukayi sallama cike da kewar juna. Hibbah ta koma suka cigaba da hira shima sa'idu yace zai tafi, umma ta Bashi kud'in mota ya tafi. Da umma zatayi girki ma tare sukayi da Hibbah, umma tayi mamaki Gannin yarda Hibbah ta iya girki haka.
Lokacin da mijin umma ya dawo Alhaji Sani ya taya umma murnar ganin Hibbah kuma yace zai d'auketa ya rik'eta tamkar 'yar da ya Haifa.
Haka Hibbah ta cigaba da zama wajen ummanta, kullum cikin bawa ummanta labarin gidansu aunty take, har umma taji bazata iya karb'ar Hibbah a hannunsu ba, dan sunyi shawara da Alhaji akan zasu karb'eta yace zai rik'eta, a haka har hutun Hibbah ya k'are aunty tazo ta d'auki Hibbah tare sukaje da umma tayiwa momy godiya.
*****
*RAYUWA*r Hibbah ta canza daga k'unci ta koma farinciki, Hibbah ta kuma gogewa ta waye, ta kuma zama budurwa idan kaga Hibbah sai ka rantse tafi shekaru sha bakwai, ta kuma cika ta ko ina ta zama cikakkiyar budurwa. Yanxu suna shirin shiga SS 2, Hibbah ta kuma maida hankali akan karatunta don tana cikin d'aliban da malamai keji dasu a makarantar. lokacinne kuma aunty ta kammala makarantar ta *BAYERO UNIVERSITY KANO*, zata tafi service d'inta, da farko Enugu state aka turata, sai da Abba ya shiga ya fita suka dawo da ita arewa inda aka tura Aunty Abuja, taji dad'in turata Abuja da akayi don a gidan Abba zata zauna.
Matsalarta d'aya Hibbah bata so tabar Hibbah a gidan saboda tasan any time Faruq zai iya dawowa kuma tasan k'udirinsa akan Hibbah, idan kuma tace zata tafi da ita Abuja momy bazata ji dad'i ba ga kuma karatunta zata fara lalata mata shi.
Haka Aunty Aysha tayi ta tunanin mafita daga baya ta yanke shawarar kaita gidan ummanta, ta fad'awa momy shawarar data yanke kuma momy tayi na'am da hakan, Ana gobe zatakai Hibbah, Hibbah ta tattara kayanta suka tafi gidan umman nata, aunty ta yiwa umma bayanin komai sannan ta tafi suka rabu cike da kewar juna. Kafin aunty ta tafi saida ta bawa Hibbah waya wai su dinga gaisawa.
Haka Hibbah ta cigaba da zama a wajen ummanta cikim kula irin ta uwa tare da taimakon mijin nata Alhaji Sani, umma ta samo mata mai adaidaita da yake kaita makaranta yana dawo da ita, da haka har aunty ta dawo daga service d'inta lokacin da ta dawo ana hutun makarantu shiyasa bata je d'auko Hibbah ba kuma bata fad'a mata ta dawo ba.