Sashe 32
Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Washe gari da safe ta shirya zata tafi school taga Nawaz bai tafi ba yama cire uniform tace "Nawaz ina shirin makarantar?" "Aunty Hibbah daddy ne yace yau bazan je ba uncle d'in mu ya bani hutu sai gobe," tayi murmushi "to haka ake so Nawaz Allah ya k'aro sauk'i, ni kuma zan tafi school saina dawo" "aunty Hibbah ki tawo min da chocolate" ta shafa kansa "a'a Nawaz doctor ya hana shan zak'i saboda ciwon ciki" tana rik'e da hannunsa suka fito har bakin gate suka gaisa da Isah, yana tsaye a wajen Isah ya d'aga mata hannu "Aunty Hibbah bye bye sai kin dawo," ita ma ta d'aga masa hannu gami da fita daga gidan, ta soma tafiya har ta k'arasa bakin titi.
Ta jima a tsaye bata samu mota ba, duba agogo tayi taga ta kusa latti ta soma tafiya ko zata samu a gaba. Hon don haka ta kauce ta basu hanya, "Aunty Hibbah" juyowa tayu don jin muryar Nawaz, shine da Daddy a motar, sanye yake da T shirt ta d'an d'ame shi, sai ya koma mata kamar Faruq don shi bai saba d irin wannan shigar ba yafi sabawa da shigar manyan kaya. Nawaz ya fito ya bud'e mata baya, dak'yar ta shiga tace "daddy barka da safiya" "lafiya lau Hibbah, wane school kike ne? Ko kema kina inda su Saudat suka gama?" Tace "eh"
Shiru ya ratsa sai Nawaz dake ta suruntunsa, Hibbah kuwa zancen zuci take tana mamakin Faheem wane irin mutum ne shi Wanda ta kasa saboda dashi har yau. Sun iso makarantar ya ajiyeta a bakin gate, tana k'ok'arin fita taji yace "k'arfe nawa zaki tashi?" "K'arfe biyu ne" "ok ki jirani" a sanyaye ta fita daga motar, ta kasa shiga school d'in tabi motar da kallo. Ji tayi an dafata ta d'an tsorata ta waiwayo Fauzy ce tana mata dariya "Hibbah me kike jira ko har kin fara duty ne yau?" Hibbah tayi dariya "a'a Fauzy ai kema kinsan bana fara duty da wuri, yanxu fa nazo" fauzy taja hannunta "zo muje class da labari fa su momy sun amince da Ya Nazeef" Hibbah tana murmushi tace "da gaske?" "Wallahi kedai muje na baki labari," suka k'arasa class.
Ranar wani yanayi ne mai dad'i a ranta kawai tunanin Faheem ya tsaya mata a rai haka komai nashi take gani harta yarda yake yin tuk'i a nutse da kalamansa masu saka nutsuwa, Allah mai iko wai har takai matsayin da zai kaita school bayan ba komai bace ita sai 'yar aikinsa, Anya kuwa zak'ewar batayi yawa ba, ko da yake Faheem da Aunty halinsu iri d'aya ne sun d'auke ta ne a matsayin 'yar uwa ne ba 'yar aiki ba, kuma yana girmamata gashi akwai kunya da nauyinsa da take ji don bata iya hawa motarsa don dai bata iya yi masa musu. Wani tunani tayi, yanzu idan Kausar ta gano tana shigar mata motar miji ai ta shiga uku, Anya kuwa bazata gudu ba idan yazo yaga bata nan ai zaiyi tafiyyarsa, kuma tunda ba wata magana suke yi ba bazai tambaye ta ba.
Ana tashi kuwa tayi sauri ta had'a komai nata suka yi sallama da Fauzy, tana fitowa gabanta ya fad'i ras, mamaki take yi kamar a mafarki anya Faheem ne kuwa? Ikon Allah, tasan ya ganta babu maganar tserewa.
Yana kallon ta ta cikin glass ya Gaza d'auke idanunsa, magana yake a waya amma duk hankalinsa yana kanta sai yaji maganar ma tana neman gagararsa, ya had'iyi wani abu sai kace sihiri ya manne mishi kamar mayan k'arfe. Kamar ta nutse Sam ta kasa dubanshi tunda ta shiga motar ai gara d'azu da Nawaz shi yana gaba ita tana baya, wai wannan wane irin nauyi ne da kunyar Faheem Allah ya d'ora mata. Haka sukayi shiru a motar tamkar kurame, Faheem akwai shi da nutsuwa da lafazi a tausashe "Hibbah" ikon Allah saura kad'an numfashinta ta d'auke, shima sautin muryarsa ya sauya.
"Ina son muyi wata magana kin shirya saurare na?" Muryarshi tayi sanyi duk sai yasa ta wani yanayi da bazata manta shi ba a ranar, "nafi son ki bud'ame baki kiyi min magana tunda nima mutum ne kamar ke ki daina wani d'ari d'ari Dani, ni na d'auke kine tamkar 'yar uwata" yayi murmushi dayaga ta d'an Saki ranta "mene a tsakaninku da Faruq? Ki fad'amin gaskiya kinsan dai Faruq k'anina ne ke kuma amana ce a hannuna Hibbah" shiru tayi,
"Hibbah bakice komai ba" "daddy shine yake zuwa........." "Nasan shine yake zuwa ma'ana maganar daya shafi soyayya" ta d'anyi shiru "gaskiya batun wannan bansan a muhallin da zan iya ajiye Faruq ba, shidai a cewarsa wai zai aure ni...." " kin tabbatar kina sonshi?" Zuciyarta ta shiga harbawa a ganinta cin fuska ne tace bata son d'an uwansa ciki guda. Ya sauke ajiyar zuciya "baki ce komai ba hakan na nufin kinason shi kenan?" Ji tayi gabanta yayi mugun fad'uwa tace "Daddy magana ce mai nauyi zan fad'a amma ba'a wannan lokacin ba" yay d'an murmushi yaji dad'in wannan furucin nata. Yayi parking a wani babban shop ya shiga ya d'an jima a ciki kafin ya fito, tunda ya fito ta k'ura masa ido ta glass d'in tana kallon sa da yake glass d'in a rufe yake kuma mai duhu ne, tabbas wani abu take ji yana ratsa zuciyarta ko mene wannan d'in?
Yabshigo motar k'amshinsa kawai yana mata dad'i mutum ne gentle, ya ajiye ledojin a kujerar baya suka tafi.
Nawaz yana ya biyo su, yana gama parking ta shige gida ta barsu anan. Tana shiga tayi wanka ta sauya kayanta tayi sallah ta nufi kitchen, tana cikin aiki Nawaz yace Daddy na kiranta.
Ta iske shi zaune yana kallon MBC 2, taje ta durk'usa a gabansa yace ta kawo mishi ruwa, yaso su had'a ido amma kunyarta tayi yawan gaske, ta kawo masa ruwan a cup ya karb'a yasha. "Hibbah" ya furta, yau dai furucin nan yana tsumata, "d'auki wannan kayan naki ne" mamaki yasa ta kasa godiya d'auka tayi ta nufi d'aki. A kan gado ta zazzage, atamfofi ne guda uku da dogayen riguna biyu da hijjabai biyu sai riga da skirt kala biyu, masu daraja don duk 'yan waje ne, da mayuka da turarukan Mata, ta lumshe idanunta tunanin Faheem take da alkharinsa tun sanda suna mota take tuno irin k'amshinsa da kalamansa, Hibbah yadda yake furta sunan a tak'aice a harshensa, wani abu zuciyarta ke zargi don me Faheem yake yi mata wad'annan tambayoyin? Bata yi mamakin wad'annan kayayyakin ba, duk da bai tab'a yi mata kyautar kaya masu tsada kamar wad'annan ba amma dama ya saba yana yi mata kyauta.
Ta d'auko takarda da biro, ta soma tunanin me zata rubuta,kawai sai ta fara rubutun.
_Daddy_
_Bani da kalmomin godiya a gareka, na gode Allah ya k'ara girma da bud'i na alkhari ya barmu da Nawaz._
_Hibbah._
Ta kira Nawaz ta bashi ya kai masa, yana kwance a parlor ya haye kansa "Daddy gashi inji Aunty Hibbah" ya karb'a ya bud'e ya karanta, yayi nazarin kalamanta wani d'an murmushi yayu yarinyar ta shiga rayuwarsa, yayi ajiyar zuciya yau saboda da ita ne kawai yaji bai son fita ko ina yana hutawarsa. Allah yasa ta fahimci manufarsa, ko tama sanu take sharewa don yayi mata hannunka mai sanda oho, ai ita mai hankali ce zata gano shi a hankali matsalarta dai rashin son sakewa a gidan indai yana gidan, sai tayi ta nuk'u nuk'u bata son ko ganinta yayi har abin ya zame mata tsoro.