← Book details Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 54

Sashe 30

Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Ya kalli inda Faheem yake a tsaye bashi ba dalilinsa, ya matso kusa da ita abinda bata so kenan, shi a wajensa ba wani abu bane don ji yake kamar ya rumgume ta, wutar k'aunarta yana faman huruwa a zuciyarsa duk sanda ya d'ora idanunsa a kan idanunta baya iya sarrafa kansa, ya matso sosai kusa da ita, bata da niyyar kulasa, "Hibbah kinsan kuwa irin sonda nake miki? Kada ki maida hannun agogo baya bana so ki dinga tuna baya ban tab'a tsintar kaina a irin wannan love d'in ba Hibbah." Ya dafa kafad'arta, a taorace ta kalleshi suka k'urawa juna kallo na d'an wani lokaci abinda ta gani a idanunsa tad'an tsorata don tabbas binda ke zuciyarsa ya fad'a, ta ture hannunsa.
Yayi murmushi "wannan gangar jikin mallakina ce sai nayi yadda nake so da ita in munyi aure, don haka ki dena guduna , ni d'in nan zan baki mamakin yadda zaki yi dadi indan na zama mijinki," murmushi tayi don ita a ganinta wauta kawai yake tace "abinda kamar wuya, naji zancen kamar almara ta Yaya zaka aure ni? Ka tuna fa kaso k'unsa min b'ak'in cikin da har na mutu bazan manta shi ba, kuma badon komai ba kawai don zalinci da son Kai, karma ka Fara yaudarar kanka don yarda ba yadda za'ayi dakai wai kai masoyina ne, don Allah na rok'eka saboda girmanasa ka k'yale ni ka k'yale min rayuwa haka." Ya kad'a kanshi "duk abinda kika fad'a gaskiya ne ni kaina ina cikin mamaki da tuhumar kaina Yaya akayi na samu kaina cikin sark'ak'iya har na fad'a tarkon sonki, banji haushi ba ai na fad'a miki kyauta kika sadaukar min da kanki wallahi zuciyata bazata iya daure wani abu dake ba matuk'ar ba aure mukayi ba," "ni kana bani mamaki to wai taya zamuyi aure? Wannan shirmen tunani ne abinda bazai yiwu ba." Yaji zafin maganarta ya take k'afafunta da takalmin k'afarsa, ta runtse ido saboda zafi, Faruq mugune yasan takan mugunta. Ya tallafo tallafo hab'arta yana wannan murmushin nasa na k'eta "dube ni sai na aure idan yaso in na aure ki ki hak'a rami ki binne ni da raina ko kuma kii gunduwa gunduwa da nama na saboda tsabar k'iyayyar da kike min," ya k'ura mata idanu tak'i bud'e idanunta, ji yayu tamkar ya lashi kumatunta, ya hurawa idanun iskar bakinsa duk da a rufe suke.
Ta bud'e idon tana dubansa shed'anin mutum kenan gani take kamar baya hankalinshi, Anya ma Faruq baya shan k'waya don abubuwan da yake yi kamar bashi da tunani a k'wak'walsa, duk inda ake neman namiji mai kyau Faruq ya kai sai bashi da hali.
Ya lakuce mata hanci, ya matso da kansa kusa da ita sosai ya sassauta murya "ke d'innan yadda kika shiga raina, ni sonki nake Hibbah kamar nayi hauka don Allah me kika yi min ne?" Ta juyar da kanta gefe, ya sa dariya "kin mai dani dodo ko Hibbah?" Yayi k'wafa "wata rana sai kin rumgume ne kinmin kiss, ni kuma shagwaba zan tayi miki," ya d'an ja da baya "ki samu cikin addu'a Allah yasa muyi aure."
Ta gyad'a kai cike da mamaki don ita wasa ta d'auki abin "aure? Wani banbarakwai nake jin abin na fad'a maka abin da kamar wuya taya ma hakan zai faru?" "Insha Allah za'ayi, ki fad'a min *I love you* zanji dad'i," kamar ta kurma ihu take ji ta rasa wanda zata cewa tana so sai Faruq.
"Kinsan halina sai na rumgume ki a nan ni babu ruwana gara ki fanshi kanki kawai kiyi abinda nace," tasan halinsa sarai zai aikata "amma ko na fad'a ka sani tursasani kayi kar kayi tunk'awo dashi *I LOVE YOU*" ya tuntsire da dariya, haushi yasa idanunta sukayi narai narai ya rik'o hannunta ta fizge don zuciyarta zafi take, da sauri tabar wajen yana ta shek'a mata dariya babu abinda yake so kamar yaga yasa Hibbah a gaba har tayi kuka, sai yaji wani sonta da k'unarta na shigarsa.

Ranar ya nace mata yak'i tafiya ko zama zaiyi saiya dawo kusa da ita sai ya waske yana yiwa Nawaz wasa, shareshi take yi don bata son Faheem ya fahimci suna wani d'asawa ne da Faruq.
Ya shigo fuskarsa a had'e kamar bai gansu ba, gani tayi Faruq ya daina rawar kai, "Faruq Ku had'a kayan nan mu tafi gida sun bamu sallama," Faruq ya kalleta "mene kike wani d'ari d'ari nifa bana jin kunya a gaban Ya Faheem sai na miki kiss kinga daya ga haka sai yasan yadda zai nema min aurenki, su bani abuna ko kuma na ja musu maga na b'allo ruwa." Ta marairaice "ka tabbatar min ka tsaneni shiyasa kake bin duk wanda nake da k'ima a wajensa kake zubar min da mutunci, Allah sai ya saka min," maganar ta shige shi ya janyo Nawaz ita kuma ta had'a kayan suka fito.
A nota suka iske shi yana danna ways Sam ya rasa mai yake masa dad'i ransa a b'ace yake, Faruq ya bud'e motar yana sa kayan, Nawaz ya shige gaban motar.
Chapter 30 · 0% Book details