← Book details Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 54

Sashe 6

Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Cikin dare Hibbah ta farka saboda zazzabin dake nuk'urk'usarta ga kuma ciwon kai, tashi tayi daga kwanciyar datayi ta zauna tare da ruk'unk'ume jiki tana ta rawar dari hakk'oranta suna ta bugar juna. Kuka take yi a hankali Mara sauti. Cikin barci gwaggo taji gunjin kuka yana tashi a hankali, lalubar touch light dinta tayi ta kunna ta haska. Hango Hibbah tayi a zaune ta dukunkune tana kuka k'asa k'asa. Daga gadonta ta sauko ta k'araso kusa da Hibbah tace ''y'ar nan lafiya cikin tsakiyar dare ki tashi kina kuka?" Cikin muryar da bata fita sosai tace "gwaggo sanyi nake ji kaina kamar zai fashe, gwaggo sanyi sanyi nakeji," ta karasa maganar tana kuma k'amk'ame jikinta. Janyota jikinta gwaggo tayi taji yarda jikinta yayi zafi sosai tace "yi hakuri Hibbah bara na kawo miki ruwan raidore Dana tafasa dazu kisha insha allah zaki ji sauki kinji?" Kai kawai ta d'aga Mata.
Zame jikinta gwaggo tayi daga na Hibbah a hankali ta tashi ta dauki touch light dinta ta fita tana haskawa, a bakin murhu ta bude wata tukunya ta tsiyayo ruwan a kwano ta rufe tukunyar ta dawo d'aki. Tana shiga d'akin ta k'arasa kusa da Hibbah D'agota tayi ta kafa mata a baki, bismillah ta fara sha, ba laifi tadan sha da yawa ta kauda kai. Gwaggo ganin ta kauda kai bata takurata ba ta ajiye kwanon, tare da maida ta ta kwanta ta rufa mata zanin data rufa dashi tace "kiyi hakuri insha allah yanzu zazzab'in zai sauka," kallon ta Hibbah tayi tace "gwaggo kaina fa?" Sannu gwaggo tayi mata tare da mikewa tace "ina zuwa," bayan kofa ta nufa tadauko ruwan zafi a buta da take ajiyewa ta zuba a roba ta sirka dana sanyi ta kawo gaban Hibbah ta ajiye taje gaban buhun bakkonta ta dauko dankwalin kayanta sabo. Kasancewar ita bata daura dankwalin atampa. Ta rabashi biyu ta karaso kusa da Hibbah ta zauna ta janyo robar ruwan ta tsoma dankwalin a ruwan ta matse ta d'ora a goshin Hibbah ta shiga gogewa a hankali. Haka tayi tayi mata har wajen daya kunbura yad'an koma Hibbah sai raki take mata.
Bayan ta gama ta dauko d'ayan d'ankwalin ta daure mata wajen dashi sannan ta kuma kwantar da ita. Gwaggo ta d'auki ruwan robar takai bakin kwata tace da safe zata zubar itama tazo ta kwanta a hankali barci yayi awon gaba dasu.

Baba kuwa koda ya koma d'akinsa shiru yayi yana ta tunani yarasa meke masa dad'i kuma ya rasa tunanin me yake yi da haka shima barci ya d'aukesa.

B'angaren Inna kuwa koda ta ja Rahmatu tana zuwa cikin dakin ta shiga zakinta ta inda take shiga bata nan take fita ba. Ita kuwa Rahmatu ko a jikinta tace "to amma Inna me yasa wai baki k'aunar Hibbah ne, nifa gaskiya abinda kike yi mata Sam bana jin dad'i kawai dai ina boyewa ne kawai kita wani sata wahala haka kawai?" Inna kallon ta take cike da mamaki wata dabara ce ta fado mata tace "ke wai bakya kishin yarda kowa yake yabonta ke ba'a yabonki kuma baki ga tafiki kyau da farin jini ba ko a wajen k'awayenku?" Shiru Rahmatu tayi can tace "eh wallahi nima fa shiyasa wani lokacin nake ji bana sonta, amma kuma me yasa kikayi mata sharrin nan kika sa baba ya koreta?" Inna tayi murmushi tace "ai duk saboda ke nayi, ke kin damu da *RAYUWA*rta ne bayan ita bata k'aunarki ta tsaneki ke kuma kina nan kina tausayinta," ta karashe da tsaki. Rahmatu tad'an zaro ido waje tace "dama bata sona?" Inna tace "ina zata soki bayan uwarta ta tusa mata tsanarmu shiyasa nayi waje da uwar itama kinga gashi ta tafi, kinga yanxu dana yi haka ai sunanta ya b'aci a gari kinga yanxu kowa zai tsaneta, saboda abin kunyar da tayi sannan ke kuma su dawo sonki" Dariya Rahmatu tasa tare da ihun dad'i tace "Kai amma naji dad'in haka inna Ashe itama bata sona shiyasa d'azu da ina tambayarta meya sameta tayi banza dani, to nima na tsaneta inna." Inna cikin happy tace "yauwa y'ar gari" daga haka suma sukayi bacci.

*Dan allah kuyi hakuri da wannan, muna biki ne bansamu time nayi typing dayawa ba.*

*by*
*Mamyn Najmah*
[10/26, 9:22 PM] Maman Najma Author P1: 📝🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓

*RAYUWA* page1⃣0⃣to1⃣1⃣

*NA*
*MAMYN NAJMAH*

🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓

*DEDICATED TO AYSHA ALIYU GARKUWA*
Chapter 6 · 0% Book details