Sashe 29
Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Sai ya samu kansa da kasa samun nutsuwa sai yaje gidansu Hibbah don gaskiya yana so yaga Hibbah, dayake har lokacin momy na nan sai yace mata yana zuwa ya zari key ya fita, direct gidan Alhaji Sani ya nufa, Alhaji Sani ya tare shi suka shiga cikin parlor babu kowa cikin mutumci suka gaisa sosai Alhaji yana tambayarsa ya iyali, suka d'anyi shiru na wasu 'yan dak'ik'u Alhaji yana mamakin zuwan Faheem gidan sa ko Alhaji ne ya turosa ya kasa jurewa yace "Faheem Alhajin ne ya turo ka?" "A'a dama ina sone mu gaisa da Umma tana nan ne?" Alhaji yayi murmushi "to to naji dad'i bara nayi mata magana tana d'aki," Alhaji ya mik'e ya shiga d'aya daga cikin d'akunan cikin parlor'n, jim kad'an sai ga su sun fito shi da umman, Alhaji sukayi sallama da Faheem don shi fita zaiyi.
Faheem ya zamo daga kujerar da yake zaune ya durk'usa har k'asa ya gaishe da Umma ta tambaye shi Kausar da Nawaz (ta tab'a ganinsa ne a hoto da Aysha ta nuna mata shi). Yace "wallahi kinga ma shiya taso ni nazo don baijin dad'i ne, kuma ya damu da Hibbah don ciwon da sauk'i akan damuwar," Umma tayi murmushi "Allah sarki bamu sani ba ai da anje an dubo shi Allah ya Bashi lafiya, bawan Allah haka so yake gamuwar jini, badai abinda zamuce muku sai fatan alkhari, Allah ya biya da aljannah," yayi Jim wani abu ya tab'o zuciyarsa yaji dad'in kalaman Umma, yana son ta tashiga ransa sai yaji don me bazai fad'a mata damuwarsa ba damin a maganarta ya fahimci bata da masaniya akan abinda ya faru har Hibbah tayo musu yaji.
A nutse ya fad'awa Umma komai abinda ya kasance har yajin da Hibbah tayi musu na tawowa ba tare da saninsa ba, Umma ta kad'a kai "ikon Allah wallahi bansani ba ni nan b'oye min tayi bata fad'a min ba cemin tayi kunyi tafiya ne ni kuma nasan bata iya k'arya ba kuma Allah bai nufa munyi maganar da Alhaji ba, kai amma banji dad'i ba kuma bata kyauta ba. Ita d'in me tafi k'arfin ayi mata fad'a ne idan tayi badai dai ba ka tsawatar mata wannan shine tarbiya, wato tasan idan ta fad'a zanyi mata fad'a shiyasa b'oye tak'i fad'a min, don Allah kayi hakuri," Faheem sai yaji wani iri kamar Umma da girmanta da k'amarta ta dinga Bashi hakuri "a'a Umma babu komai wallahi," wadda take yiwa Umma share share ce tazo d'aukar abu Umma tace ta turo mata Hibbah, sai gata kuwa tana ganinshi tayi turus, zuciyarta tana bugawa kamar zata tarwatse ko a mafarki bata tab'a tsammanin shi ba, ta zube "ina yini Daddy," ya dubeta ya had'e fuska "bazan amsa ba Hibbah tunda nayi fad'a kikayi fushi har kika tawowarki gida bako sallama, kin bani girma kenan? Gashinan kinsa yaronki rashin lafiya yana asiiti kin kyauta kenan?"
Ta dubeshi a razane hantarta har ta kad'a ta had'iyi miyau dak'ar idanunta sun cicciko hawaye, Nawaz Allah sarki dama tasan za'a rina bata yi masa adalci ba, ita ma tana nan har d'an zazzab'i tayi shak'uwarsu tayi yawa ita da Nawaz, Allah sarki sak taji tausayin yaron da k'aunarsa na kuma shiga ranta. To yaya zatayi idan ba ta barwa Faheem gidansa ba don yayi mata hannunka mail sanda.
Umma kuwa ta rufe ta da fad'a "ni ban san sanda kika koyi k'arya ba halin hofi Hibbah don me baza'a fad'a miki kinyi ba dai dai ba kinfi k'arfi a tank'wara kine, to ki shiga hankalinki idan ka rasa mafad'i a duniya ka shiga uku, wad'annan mutanen sunan k'aunarki mutunan da suka d'aukekan tamkar d'an uwa na jini suke d'awainiya dakai, tun wuri ki sauya tunani ni ban goyi da bayan ki raina na gana da ke ba d'an halak baya manta alkhari, wallahi kar na kumaji kinyi irin wannan shirmen kuma ki d'auki kayanki ki koma, ki bashi hakuri yanzu,"
Zuciyarta tayi rauni jinkinta yayi sanyi ganin ran Umma ya b'aci sosai gashi tana ta yi mata fad'a abinda bata tab'a yi mata ba, da k'yar muryarta tana rawa tace "daddy kayi hakuri bazan k'ara ba, Allah ya huci zuciyarki Umma," ta fad'a tana share hawaye. Tausayinta yaji sosai ko da yake yaji dad'i umman ta burgeshi don shi mutum ne Mai son a bashi girma da girmama na gaba dashi don haka bai son reni ko kad'an shi yasa Hibbah ta shiga ransa don tana da biyayya da ladabi Sam bata kiransa da Yaya kamar yarda k'annansa suke kiransa saidai tace masa Daddy kamar yadda taji Nawaz yana fad'a.
Ta tashi ta d'auko Jakarta, ya ajiyewa Umma kud'i ba yadda batayi ba ya d'auke abinsa amma yak'i yaji dad'in karramawar da akayi masa da sanin ya kamata irin na iyayen k'warai, suka yiwa Umma sallama suka fito.
Ya bud'e mata gaban motar don yasan halinta sai ta zauna a baya, ta kalleshi gani tayi ya had'a rai babu alamar wasa a tattare dashi shiyasa ba musu ta shiga. Ya dad'e bai ji annashuwa ba kamar a yanayin nan ya kunna wakar Celine Dion yana sauraron baitukan wak'ar, yana tuk'i cikin nutsuwa, Hibbah ko numfashi bata yi k'wak'wk'wara ji take yi tamkar ta nutse, kunya ce nauyi ne rashin sabo ne, duk sunyi Mata dabaibayi don basu tab'a had'uwa haka gata gashi ba.
Ya dubeta a nutse domin duk damiwarsa babu ita ashe Hibbah ce ta hana zuciyarshi nutsuwa, "Hibbah ta Nawaz ya kikayi shiru ne na takuraki ko? Banji dad'i bane akan abinda ya faru ashe fushi ne dake haka, ki sani nayi miki fad'ane don kawai na damu dake ina kishinki tamkar k'annena su Safiyya ya d'auke ki badon haka ba babu ruwana da ra'ayin wani, ina data dai kin huce ko?" Bata ce komai ba, ya dubeta idanunta sunsha kuka kuwa, zata kuma iya ci gaba da yinsa idan har ya takurata sai yaji maganarta don a takure take ya Sani, shi kuwa so yake ta saki jiki dashi ta daina jin tsoranshi haka don haka ya rabu da ita, da haka har suka k'arasa asibitin.
Yana gaba tana binsa a baya, sama suka hau basuyi wata tafiya ba suka isa d'akin, suka shiga ta gaishe dasu momy lokacin Nawaz yana barci momy ta mik'e zata tafi wai dama shi take jira ya dawo yamma tayi sukayi sallama tayi masa fatan samun sauk'i suka tafi.
Jimawa kad'an Nawaz ya tashi yana ganinta ya mak'aleta yana k'yalk'yala dariya kamar zata sake gudu ta barshi, ta shafa kansa tana dubansa yayi 'yar rama ta share k'wallar data taru a idanunta. Nawaz ya rik'e hannayenta "aunty Hibbah shine kika gudu wajen Ummanki kika barni kinga inda doctor yayi min allura," ta tab'a wajen "sannu Nawaz Allah ya baka lafiya," "Aunty Hibbah nima zan biki wajen Umma."
Ta gyad'a Kai "to naji amma sai ka ji sauk'i zamuje," ta ja hannunsa suka fice barandar suna kallon titi dayaga abinda ya bashi sha'awa sai ya dinga nuna mata suna dariya, yana ta bata labarin abinda ya faru bayan tafiyarta.
Yana tsaye ya hard'e hannayensa a k'irjinsa yana kallonsu sun burgeshi da Bashi tausayi "Hibbah" ya ambata a zuciyarsa sunan mai dad'i, ga mamakinsa ashe maganar ta fito fili har tabi iska ta isa kunnenta kawai gani yayi tad'an juyo ta kalleshi, suka had'a idanu cikin wani yanayi a hankali ta d'auke kanta, wani sanyi take gani cikin idanunsa sai taji abin yana mata yawo a k'wak'walwarta.
"Hey! My boy," duk suka dubeshu, yayi zanzaro da hula Hana sallah a kansa, da siririyar sark'a tana k'yalli a wuyansa har taso ta shak'e sa, "Yaya ya jikin boy d'in?" "Alhamdulillah yaji sauk'i sosai," hankalinsa yana kan Hibbah bai ko damu da ganin Faheem ba, ya d'auki Nawaz ya rumgume shi tare da yi masa kiss a kumatunsa, shi kuwa ya mak'ale hannayensa a wuyansa tare da zagaye k'afafunsa a jikinsa, Faruq kenan yana k'aunar Nawaz shiyasa shima Nawaz yake k'aunar uncle d'in nasa.
Hibbah kuwa kallo d'aya tayi masa ta d'auke kanata don har yanzu tsoransa take ji...............
*by*
*Mamyn Najmah*
[10/26, 9:25 PM] Maman Najma Author P1: 📝🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓
*RAYUWA* page3⃣5⃣
*NA*
*MAMYN NAJMAH*
🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓
*DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION*
D.B.A.W
*DEDICATED TO AYSHA ALIYU GARKUWA*