Sashe 36
Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Faruq yana fita daga gidan Faheem cike da b'acin rai ya nufi gidan Aunty Aysha, bayan yayi parking ya nufi cikin gidan yayi knocking mai aikinta ta bud'e ya shigo ya zauna a kan kujerun d'akin.
Ta shigo "barka da zuwa yau kaine a gida na?" Yayi murmushi "to ya zanyi dake nayi fushina na gala ba zan iya gaba da ke ba, d'an uwa baya fushi da d'an uwansa" tayi dariya "Umar Faruq kenan yaya halinka? Ka canza ko har yanzu kana nan dashi?" "Ki bari dai kawai Aunty yanzu ma tawa ce ta kawo ni domin kece jagoraba don nasan zaki sharemin hawaye na," ya sassauta murya "Aunty aure nake son yi a cikin wannan lokacin kafin na tafi Germany, ki bani shawara kisa albarka kuma kiyi addu'a" tayi shiru tana nazarin maganar Faruq lallai Faruq yayi hankali ya nutsu tunda har ya yanke shawarar yayi aure, "to naji bayaninka kuma shi aure alkhari ne Allah yasa albarka yasa hanyar shiriyarka kenan ka dena wad'annan d'abi'un, nasan hali dai zanen dutse amma in da nauyin iyali a kan rusuna koma a daina gaba d'aya, yaushe ne za'a Fara shirye shirye, ka sanar da momy da Daddy da kuma Ya Faheem ya sani shima ko?" Ya sosa sumarshi "hmmm basu Sani ba tukuna, manta da Ya Faheem kinsan shi tsarine dashi zai iya kawo suka cikin lamarin don bana tunanin zai goyi baya" "to ai kuwa Ya Faheem shike da ruwa da tsaki a maganar aurenka shine yake wakiltar Daddy tunda ba zama yake yi a gari ba kuma kaga Abba ma bai fiya zama ba, kasan ance babban wa uba ne ko?"
Ya yamutsa fuska "ai kin gane ni na fahimci baya son alak'ata da yarinyar, labarin zuciya a tambayi fuska, kawai dai bashi da yadda zaiyi ya rabani da abinda nake so" Aunty ta girgiza kai "a'a shi dai yana duba halayyarka ne saboda me zaik'i son abinda kake so shi zaifi kowa farin ciki da aurenka, a kullum burinsa Faruq ka shiryu ka bar kaza da kaza wannan abin da kake yana zubar maka da k'imane fa,"
"Nifa ina mamakin wannan wane irin hali ne nawa kuke ta aibatani, ni ba kisan kai nake ba, ba fashi da makami ba ba shan giya ba, ba kuma na ta'ammali da miyagun aiyukan ta'addanci, men's a cikin rayuwar dana keyi bai hanani bautawa mahaliccina ba, na lura gani kuke ki kamar na kafirce ko bansan Allah ba ko nauyi zunubi na yakai Allah bazai yafe min ba ku daina shiga tsakanin bawa da ubangijinsa domin shi gafuru rahim ne." "Gaskiya ne to amma babu Wanda ke son yaga nasa ya lalace in baka gyarashi ba duniya zata gyara maka shi, in baka fashi da shan giya amma kamannin mutum ake dubawa a gane yaya halayyarsa take care banzane kona kirki, kuma banji kayi lissafi da neman mata ba ko ita bata cikin manyan ayyuka zina fa, dole ne Faruq na fad'a maka gaskiya nasan da d'aci da ciwo amma ina tausayin wadda zata aureka, ina tunanin rayuwarta a hannunka domin idan neman mata ya damk'i mutum masifa ne, don barinsa ba k'aramin jihadi bane......" Ya d'aga mata hannu ransa a b'ace "kin gani ya isa kawai bana son wani k'wak'ule k'wak'ulen maganganu ina ruwanki da harkokina don sa ido irin naki ai kowa da tashensa lokaci ne idan ya wuce ai shikenan kuma aure ne sai nayi" tayi murmushi "Umar Faruq kenan to a ina yarinyar take nasanka da lek'e lek'e da gane gane, zanso ganin wannan yarimyar dole na kirata mai sa'a don ta ciri tuta tunda har zata auri k'anina" yayi dariyar jin dad'i "yauwa mutuniyata ai 'yar gidan ki ce ba wata bak'uwa ba, yarinyar nan ce Hibbah" ji tayi kamar gini ya ruso Mata rigigim! Ta zaro idanu "wace Hibbah? Badai tawa ba?" Ya gyad'a kansa "Hibbah dai da kika Sani.................."
*by*
*Mamyn Najmah*
[10/26, 9:26 PM] Maman Najma Author P1: 📝🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓
*RAYUWA* page3⃣9⃣
*NA*
*MAMYN NAJMAH*
🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓
*DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION*
D.B.W.A
*DEDICATED TO AYSHA ALIYU GARKUWA*
Aunty hankalinta yayi mummunan tashi "yaushe har ka yaudareta ka hure mata kunne kuka k'ulla soyayya tayi k'arfi haka?" "Ni ina sonta kuma itama tana sona duk da miyagun halayena, bata ganin aibuna kuma tace bazasu hanata aurena ba" cikin b'acin rai ta nunashi da yatsa "wannan shirin ka ne ni nasan k'aryane, yaudararta kayi don magana ce wannan da k'wak'walwata ta kasa d'aukata ba sonta kakeyi tsakani da Allah ba, ka tuna ka kusa illata yarinyar nan tun da ka d'ana mata tarko Allah ya tserar da ita, shine ka b'ullo ta wannan sigar to babu kai babu auren Hibbah 'yar mutunci bata cancanta da kai ba, kawai kaje ka cuceta da zalincinka na 'yan bariki, nasan bazata soka ba koda bata fito k'arara ta nuna maka k'iyayyarta ba don tana jin nauyi a matsayinka na k'anina, bazan goyi da bayanka ba don nasan daka gama cin moriyar gagga zaka yarda k'wauronta, tayi miji mai sonta don Allah Jabeer iyayenta sunsan da maganar auren bazan tab'a yadda ka dagula zancen ba wallahi, babu kai babu ita zan ganta itama sai naci ubanta shashashar banza kawai bata San inda yake mata ciwo ba, wato ita bata tausayawa kanta bata nemawa kanta 'yanci." Ya mik'e yana wani irin huci iyakar fusata ya fusata fuskar nan tayi jawur "Ashe ke mak'iyiyata ce a yau na tabbatar ni ba jininki bane ai hannunka baya rub'ewa ka yanke ka zubar duk lalacewata ni naki ne, kince ni d'an iskane uban bariki ne ni ba d'anta ba, wallahi saina auri Hibbah idan yaso ki dinga yankar naman jikina kina k'onawa ko kuma ki fad'i ki mutu don bak'in ciki. Wallahi zamusa k'afar wando d'aya dake koda zamu k'ulla gaba ta har duniya ta nad'e, aurena da Hibbah ba fashi don ra'ayi nane kuma babu abinda kika isa kiyi." Yayi awon gaba da center table d'in dake parlor'n glass cups d'in dake kai suka fad'o suka farfashe, ko juyiwa baiyi ba yayi tafiyarsa don ya d'au zafi.
K'ofar fita sukayi karo da Sagir mijin Aunty Aysha saida ya gogi kafad'arsa, yaja baya yana kallon Faruq da mamaki, gaba yayi ko waigowa baiyi ba bare ya kula sa, ya kad'a kansa ya shiga ciki yana mamakin Faruq, ya zauna tayi masa sannu da dawowa.
Ya gano tana da damuwa cikin sigar rarrashi ya matsota "haba amarsu na kiyi hakuri nasan fad'a kukayi da d'an uwan naki, kinsan su sai ana hakuri dasu a hankali zai canza" ta numfasa "kayi hakuri naga har bangajeka yayi, Faruq fitinannen yaro ne ya damu family'n mu, kullum bama shiri jituwa dashi sai fad'a don na fad'a masa gaskiya ni kuma bazan fasa fad'a masa ba sai dai muyi ta fad'a dashi"
Ta fad'a mishi abinda ke faruwa. Yayi murmushi "ku mata wani lokacin tunaninku kamar na k'aramin yaro yake, Aysha ai ba'a fad'in abinda ba alkhari ba a lamarin aure idan ita kuma yarinyar tace shi take so sun had'a kansu fa, yaya zakiyi sai kiji kunya kuma har abada zai ta kallonki da wannan abin tunda bake kika haifeta ba na dai gane abinda kike hango mata, kina sonta kuma ke kin fita sanin halin d'an uwanki amma kamata yayi ki nuna goyan bayanki ki tayashi murna, ba yadda zakiyi dashi naka nakane saidai kiyi masa ta masa add'a da fatan auren ya zama sanadiyyar shiryuwarsa." Aunty ta numfasa "my dear abinda ka fad'a hakane amma karka manta fa akwai maganar aure a tsakanin yarinyar nan da Jabeer kuma har manya sun shiga sa rana kawai za'ayi sai yanzu zasu zo min da maganar banza daga ita har shi, ai itama zan sameta ne saina ci mata mutunci" "kibi abin a sannu, kum idan ita Hibbah tace bata son Jabeer ai dole ya hakura ko zakiyi mata dole ne?" Ta girgiza "to kingani kawai saidai muyi fatan Allah ya zab'a abinda yafi alkhari" "to ameen muje ka watsa ruwa ko?" Suka mik'e a tare suka shiga ciki.