← Book details Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 54

Sashe 52

Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Daddy ya baiwa baba duk wata dukiyarsa da take wajensa da da farko baba yak'i karb'a yace ya barsu ya cigaba da juyawa amma daddy yace ina kawai ya amsa, haka badon baba yaso ba ya amsa. Part d'in da Faheem ya zauna nan daddy ya mayar na baba.

Kwanansu uku da dawowa daga k'auye, suna zaune kamar kullum don tunda suka dawo kullum da yamma zasu zauna a parlor ko a garden suyi ta hira, mai gadi ne ya shigo da hanzari yayi musu sallama suka amsa yace "Alhaji dama wani ne ya bada sako a kawo maka" ya mikawa daddy takardar dake hannunsa yace "kuma yace don Allah idan yanzu kana gida idan ka karanta sakon dake ciki ka hanzarta zuwa asibitin" daddy ya kad'a kai "to shikenan zaka iya tafiya" mai gadin ya juya ya koma bakin aikinsa.
Daddy yana rike da takarda yana zulumin abinda zai gani a cikinta yana tunanin to daga k'ark'ashinwa wannan takardar tazo sannan waye a asibiti? Su Abba da sauran mutanen dake zaune kuwa kowa da abinda ke cikin ransa tunda sukaji an ambaci asibiti.
Da k'yar daddy ya iya bud'e takardar ya karanta sak'on da ya gani ya d'aga masa hankali ya d'ago ya dubi su baba da duk shi suke kallo yana furta Kalmar Inna lillahi wa inna ilaihirraji'un yace "Ku tashi mu tafi asibitin murtala" a gigice suke kallonsa waye ba lafiya baba yace "waye bashi da lafiya" Daddy da har ya kai kofar fita yace "kuyi hakuri ba lokacin bayani Ku tawo kawai mu tafi" haka su momy suka d'augo hijjabansu suka fito, motoci suka shiga kai tsaye asibitin murtala Muhammad suka nufa, bayan sun gama parking suka nufi cikin asibitin d'akin da aka yiwa Daddy kwatance suka nufa Daddy ne yake jagorantarsu har suka isa d'akin.
Da sallama suka shiga yarinyar da take jinyar tashi ta amsa masa, Wanda baba ya gani yana jinyar ne ya sashi karasawa kusa dashi cikin hanzari "Ibrahim Ibrahim me ya sameka garin ya wannan Abu ya faru?" Baba duk ya rude sai tambayoyi yake masa. Su momy kuwa sai sannu suke masa, Alhaji Ibrahim dake kwance a gadon na asibiti ya rame yayi bak'i kasusuwansa duk sun bayyana kamar mai cutar Ebola ga hannunsa d'aya babu k'afa ma babu guda d'aya bakinsa kuma ya karkace ya rik'o hannun baba "Mukhtar ka yafe min kaji k'aina nayi nadamar yadda na rusa amincin mu ta hanyar cin amanarka, wallahi nayi dana sanin san duniya irin nawa" ya ja numfashi da k'yar baba ya kuma k'amk'ame hannun nasa "Mukhtar kaga k'arshena ko? Kaga k'arshen zab'ar duniya akan lahira da nayi ko? Kaga illar cin amana ko? Sannan ga uwa uba shirka da nayi da ubangijinmu, Mukhtar duk wani hali da ka shiga a baya wallahi nine sila ni nayi maka sammun da aka zautar maka da tunani ni nasa a lalata maka k'wak'walwa, kaga k'arshena ko Mukhtar kowa ya gujeni hatta 'ya'ya sun gujeni matata ma haka wannan yarinyar nurse ce ita kad'ai ce take jinyata don Allah ka yafe min wallahi nayi nadama....." Ya karasa maganar hawaye na bin fuskarsa sannan ya soma wani irin tari kamar zai amayar da hanjinsa.
Allah sarki baba shi duk tausayinsa yake ji sashen zuciyarsa kuwa na mamaki irin wannan san zuciya na mutane ashe har Ibrahim zai iya yi masa wannan rashin imanin? Da sauri ya girgiza kai nima ina da lefi da ina bawa kaina kariya da Neman tsari wajen ubagiji da bazaiyi tasiri a kaina ba, baba ya kuma rik'e hannun Ibrahim yace "na yafe maka Ibrahim Allah ya yafe mana" murmushin k'arfin halin Ibrahim d'in yayi bayan ya tsagaita tarin ya dubi su Abba dasu momy da su Hibbah masu arhar hawaye har amfara ambaliyarsa yace "don Allah Ku yafe min" daddy ya dube shi "ba komai ni na yafe maka Ibrahim Allah yana son masu yafiya" suma su momy su Aunty duk sukace sun yafe masa.
Sai kuma ya dinga wani tari sosai ba k'ak'k'autawa har numfashinsa na d'aukewa, yarinyar dake jinyarsa ta fita da sauri don kira doctor shi kuwa baba dake kusa dashi sai maimaita masa Kalmar shahada yake amma ina ya kasa kamawa a haka har numfashinsa ya d'auke gaba d'aya (to dama Wanda yayi shirka ina zai cika da Kalmar shahada).
Dr ya shigo tare da budurwar ya shiga duba shi lokaci daya ya gano cewar ya rasu ya lullub'a masa zanin dake jikinsa ya dubi su Daddy "Alhaji sai dai hakuri Allah yayi masa cikawa" su baba dama tuni suka gano hakan sai suka bishi da addu'ar samun rahma wajen ubangiji don ba'a shiga tsakanin Bawa da ubangijinsa. Haka suka d'auko gawar suka mata sutura aka kaishi gidansa na har abada, sannan aka nemi iyalinsa aka fad'a musu.

An kashe kudi a bikin Hibbah da Faheem don ko wajen events d'in kawai da aka gabatar kawai kud'insa ya isa ballantana azo ga irin dukiyar da su Abba suka kashe mata a kayan d'akinta dana kitchen, gaskiya su Daddy sun sunyi rawar gani don kuwa Hibbah ta zama 'yar gata ta ko wane b'angare.
Wani tank'ameman gida aka shigo da Hibbah ko a iya get d'in gidan kawai kasan gidan ya tsaro mamy data rik'o hannun Hibbah na dama yayin da aunty ta rik'o d'ayan hannun nata gaba d'aya Hibbah a rumgume take a jikinsu fuskarta a lullub'e tana ta kuka k'asa k'asa, mamy ta rad'a mata "my Hibbah nemi tsarin Allah ki yi add'u kafin ki shigo ki shigo da k'afar dama kiyiwa aurenku addu'a da sa masa albarkar ubangiji" duk da kuka take hakan bai hanata yin addu'a ba ta kuma shiga da k'afar dama. Haka su mamy suka shigo da ita cikin k'aton gidan nata dake ta zuba uban k'amshi mai dad'i direct bedroom d'inta suka huce da ita inda suka sauketa a kan gadonta, nan mamy ta kuma yi mata nasiha sosai a k'arshe ta rufe da kuma koya mata wasu dabarun zama da miji kafin kuma su tafi.
Haka 'yankai Amarya suka tafi suna ta zuba santin gidan, aka bar Hibbah ita kad'ai sai Saudat Safiyya da fauzy da aka bar mata suma suna gama gyara inda 'yan kawo Amarya suka b'ata suka ce zasu tafi Saudat tace "Aunty Hibbah mu dai mun tafi kar ango yazo ya bubbugemu, ni dai da safe zanzo gashi" fauzy tace "lallai kam ni dai kazar za'a ajiye min" Safiyya tace "auntyna mudai mun tafi" suka fita suna dariya adamu driver ya kaisu gida. Haka suka bar Hibbah ita kad'ai duk tsoro ya cikata ga kuma kunya tana tunanin da wane ido zata kalli Faheem a matsayin mijinta?
Chapter 52 · 0% Book details