Sashe 7
Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da hanzari baba ya fito daga dakin cikin bacin rai da tsana yake bin Hibbah da mugun kallo, Hibbah ta tsorata da kallon da yake mata. Abu ta matso kusa da ita ta kunce Dan kwalin kanta ta mika mata tana cewa "rufe k'irjin ki da wannan," karb'a Hibbah tayi ta daura shi a k'irjinta.
Cigaba baba yayi da binta da mugun kallo yana karasowa kusa da ita hannunsa ya daga ya yarfa mata wani gigitaccen mari, kafin ta dago ya kuma dagota da dayan b'angaren, cikin kakkausar murya yake magana "ni zaki wulak'anta ki batawa suna a gari Eye? Wato kinyo gado koh?" Ya cigaba da dukanta. Inna lami cikin kissa tazo ta shiga gaban baba tana cewa "haba malam kaima kasan barewa bazatayi gudu d'antq yayi rarrafe ba, taga uwarta nayi itama dole tayi." Cikin muryar kuka har tana sarkewa Hibbah take cewa "wallahi baba fyade zai yi min bani na gayyato shi ba, kaga rigata ma ya yaga min saboda naki bashi hadin kai." Abu ce taje gaban baba ta tsugunna tana bashi hakuri "kayi hakuri baba, da gaske ne ba ita ta kawo shi ba shi ya kawo kansa kuma wallahi baba fyade yaso yayi mata." Kallon Abu yayi yace "me kika sani? A gaban ki akayi?" Girgita masa Kai tayi tace "a'a baba ba agabana akayi ba," dauke kansa baba yayi daga gabanta yace "kinga kenan kema baki da tabbacin ba ita ta kawoshi ba, tunda baki da wata sheda daza ta tabbatar min da hakan." Cikin daga murya da b'acin rai ya nuna Hibbah dake gefe a tsugunne tana ta rusa kuka yace " baza ki maida min gida bariki ba ki tattara kayanki ki barmin gida!!" Furucin baba ya tsorata kowa dake wajen, cikin rudu Hibbah ta taso da gudu ta rike kafafun baba tana kuka tace "don allah baba kayi hakuri wallahi bantaba aikata abinda kake zargina dashi ba, fyade zaiyi min baba idan nabar gidan nan ina zani baba babu inda nasani." "Kibi uwarki kema ki shiga duniya!" Muryar inna lami sukaji tana bada amsa. Kallon ta su Abu sukayi, cikin tsana Abu take hurga mata harara ta kalli baba tace "Baba ina da sheda," "mece shedar taki?" Baba ya tambaye ta.
Karasawa tayi kusa da Hibbah ta tallafo fuskarta tana nuna goshinta tace "Baba kalli koshinta inda ta yanke," Baba ya kalli goshin nata tare da kawar da kai. Abu ta cigaba"saboda taki bashi hadin kai ne ya buga mata Kai da kofar dakin ta yanke, sannan ga rigarta ma inda ya yaga Mata duk saboda bata bashi abinda yake so ba. Na tabbata Baba da ita ta gayyato shi baza ta bari ya yaga mata sutura koya ji mata ciwo ba. Da kuma shima bazata............" "Malama wannan duk zancen banzane!" Inna lami ta katseta cikin fada.
Shiru baba yayi yana nazarin kalaman Abu ya kalli inna lami yace "lami lamarin yarinyar nan fa akwai k'amshin gaskiya," cikin fada Wanda ya zame mata jiki inna lami tace "eh dama dole ka fadi haka kai ga mai 'ya koh? To wallahi ni bazan zauna da mazinaciya fasik'a a cikin gidan nan ba idan ita bazata bar gidan nan ba toni saina tafi," ta fada tana girgita jiki saboda tsabar masifa. Kallonta baba yayi yace "a'a lami wai da a duba lamarin kafin........." "A duba lamari koh? To bari kaga idan na tafi gidan mu Kai saika zauna da mazinaciyar," ta fada tana yin hanyar dakinta. Ita kuwa Hibbah kuma fashewa tayi da kuka tana karanto _inna lillahi wa inna ilaihira ji'un_, su Abu karime da dije ne suka karaso kusa da ita suna lallashinta. Shi kuwa Baba da sauri ya Sha gabanta yace "haba lami ai ko bata aikata komi ba kikace tabar gidannan saita Bari," ya juyo ya k'araso kusa da inda Hibbah take ya nuna ta "ki tashi ki barmin gida tun kafin na b'ab'b'allaki," Hibbah ta kalleshi hawaye na bin fuskarta tace "Baba idan na bar gidan nan ina zani yanxu ga dare, baba baka tsoron wani abu ya cutar dani?" Baba yace "ni dai kawai nace ki barmin gida!" Ya kuma d'aga murya. Rahmatu wadda ta shigo yanxu ta kalli Hibbah yarda take kuka kamar zata shid'e, sai taji ta bata tausayi duk da rashin kunyar Rahmatu tana son 'yar uwarta kawai bata nunawa ne saboda tasan halin Inna.
Karasowa tayi kusa da Hibbah tace "Hibbah meya faru? Me kika yiwa baba yace kibar masa gidansa? Mene a goshinki?" Kukane yaci k'arfinta ta kasa magana, daga cen suka jiyo muryar inna lami tana cewa "karuwa ce mazinaciya fasik'a har gida take kawo su, yarda taga uwarta nayi." Zaro ido waje Rahmatu tayi tace "karuwa fa kikace Inna?" "Eh karuwa ce da kwarto aka kamata," inna ta bata amsa.
Shiru Rahmatu tayi ta kalli Abu tace "Abu a gabanki akayi?" Da Abu batayi niyyar amsata ba, amma kanin yarda ta damu da Hibbah yasa ta Girgiza kai tace "a'a nazo dai na ganta ta fito da gudu daga dakin a gigice," Rahmatu tace "kinga kwarton?" Hibbah kallon ta takeyi da mamaki saboda Rahmatu bata tab'a nuna damuwarta akan Hibbah ba, ba Hibbah kad'ai ba harsu Abu da inna lami mamaki take basu.
Abu ta kalleta tace "eh na ganshi," da sauri Rahmatu tace "waye?" "Sale direba ne," "sale direba?" Rahmatu ta maimaita tana kallon inna wadda yanayinta yad'an sauya tace"Anya inna baki da masaniya akan wannan abun kuwa?" "A gidan uwarki nake da masaniya?" Inna ta fad'a tana yi mata dak'uwa tace "malam yarinyar nan idan fa bazata bar gidannan ba ni Zan tafi" baba yace "kafin na irga uku kibar min gida" Rahmatu da sauri tace "allah baba kayi bincike naga fa inna dazu da sale a kofar gida."
Gaba d'aya kowa ya waiga yana kallon Rahmatu, da sauri inna ta k'araso kusa da Rahmatu ta buge mata baki sannan ta fara janta, ciccijewa Rahmatu ta shigayi tana cewa "wallahi sai na fadi gaskiya, baba kayi bincike kafin ka yanke hukunci, da sa hannun inna a cikin wannan abun....." Kuma buge mata baki inna tayi tare da cewa "wallahi malam idan na kuma maimaita Hibbah ta bar gidannnan to ni zan barshi." Jin haka yasa baba da hanzari yazo gaban Hibbah yana masifa "ki tashi ki fita nace koh?" Cikin sark'ewar murya Hibbah tace "baba ka tsaya kayi bincike....." "Bazan yi ba d'in mai bak'in hali ki fita," ya buga mata kafa "baxa ki tashi ba so kike ki kashe min aure?" Ya kuma Kai mata duka. Ganin yana shirin ji mata ciwo yasa su dije da Abu suka d'agata don ta kasa tashi.
Dak'ar take takawa har suka je bakin k'ofar fita juyowa tayi ta kalli baba taga ashe shima ita yake kallo, cikin murya mai rauni tace "baba me yasa zaka yankemin hukuncin barin gidanka koda ace lefin da kake zargina dashi na aikata? Baba ka rabani da mahaifiyata mai k'aunata, yanzu kuma ka rabani da gidanka bayan kuma idan na barshi babu inda zani nan d'inne kawai muhallina, me yasa baba kake son kuntata min? Me yasa kake son na rayu cikin kunci da kad'aici? Kafison *RAYUWA*ta ta lalace? Me yasa baba? Me yasa.........." Kukane yaci k'arfinta. Shi kuwa baba jikinshi yayi sanyi bakinshi kuma yayi nauyi ya kasa ce mata ta dawo.
Su Abu ne suka jata suka bar gidan a k'ofar gidan Hibbah taja tunga ta tsaya tana kallonsu d'aya bayan d'aya hawaye na sintiri a fuskarta tace "yanxu Abu ina zanje da wannan daren me yasa baba bazaiji tausayina ba?" Abu ta dafa kafadarta tana goge mata hawaye tace "kiyi hakuri Hibbah ba lefin baba bane saboda baya hayyacinsa, yanxu kizo muje wajen gwaggo ( mahaifiyar Aysha, umman Hibbah ) kawai." _gwaggo kaka ce a wajen su Abu da Hibbah, Abu 'yace awajen malam Habu yayan Aysha. Tunda aka kawota yaye bata koma gidansu ba_ Dije tace "tabbas nan ne kawai zakije Hibbah," kallonta Hibbah tayi tace "kuna ganin babu matsala?" Karime tace "haba Hibbah kema kinsan KO kowa ya zargeki gwaggo bazata zargeki ba." Hibbah tace "shikenan nan muje."
Kai tsaye gidan gwaggo suka nufa, abakin kofar gidan sukayi sallama dasu karime. Su kuma suka shiga cikin gidan, dakin gwaggo suka nufa lokacin ma har tayi barci Abu ta tasheta.
Tashi tayi zaune tana kallon Abu da Hibbah tace "lafiya kika tasheni ina barci? Ke kuma Hibbah me yasa kika biyota baki ganin dare yayi?" Abu tace ina fa lafiya gwaggo? Baba ne ya koreta daga gidan," cikin mamaki gwaggo tace "ya koreta to saboda me?" Nan Abu ta fada mata duk yarda akayi. Tattafa hannu gwaggo ta shigayi tana sallallami tace "ai dama nasan za a rina matar da bata bar mahaifiyarki ba balle ke" Baban su umman su Hibbah ne ya lek'o yana cewa "lafiya ne naji kina sallallami?" Gwaggo tace "ina fa lafiya........." Nan ta shiga labarta masa komi kamar yarda Abu ta fad'a mata.
Shi kanshi baba yaji ba dad'i amma sai yace "to ai shikenan sai tayi zamanta anan din tunda bata da inda zata." Yana gama fadin haka ya koma dakinsa. Gwaggo ta kalli Hibbah tace "ki kwantar da hankalinki kiyi zamanki a nan kinji? Kuma karki kuskura ki zargi mahaifinki don bashi da lefi baya hayyacinsa ne, *RAYUWA* ce wata rana sai labari kinji?" daga Mata kai Hibbah tayi tace "insha Allah gwaggo" gwaggo tace "yauwa 'yar albarka allah ya muku albarka" sukace amin. Tashi sukayi suka dauro alwala suka kwanta................
*by*
*Mamyn Najmah*
[10/26, 9:22 PM] Maman Najma Author P1: 📝🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓
*RAYUWA* page1⃣4⃣
*NA*
*MAMYN NAJMAH*
🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓
*DEDICATED TO AYSHA ALIYU GARKUWA*