← Book details Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 54

Sashe 51

Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*by*
*Mamyn Najmah*
[10/26, 9:27 PM] Maman Najma Author P1: 📝🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓

*RAYUWA* page5⃣3⃣

*NA*
*MAMYN NAJMAH*

🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓

*DEDICATED TO AYSHA ALIYU GARKUWA*

```watpad@mamyn_najmah2222```

Kafin su fito ya had'a musu wasu k'ullika ya bata "ga wannan ki barbad'a a wajen da kika tabbatar zata tsallaka daga yanzu da kika amsa karya awa d'aya baki yi amfani dashi ba sannan da kinje gida ki barbad'a tana tsallakewa da mintuna biyar ki share, karki karya k'a'ida ko guda d'aya idan aka samu matsala d'aya a cikin mu zai mutu ko ni na mutu ko ke ki mutu" babu ko d'ar a zuciyar Inna lami ta amsa suna k'ok'arin zube masa k'ud'i y katse su "wannan aikin naku yana da had'ari ku bari sai aiki yayi kyau sai ku kawo" nan suka tashi sukayi godiya suka tafi.
Suna tafiya suna ta hira a kan maganin da bokan ya basu, sunzo tsallaka wani d'an k'aramin titin da zai sadasu da k'auyen katsalle da yake titi guda d'aya ne sai ji kake k'uuuuuuuuuu wata k'atuwar dab tayi shoki da su delu ma'ana tayi sama dasu a take suka zube a wajen.

Can gidan kuwa ana kiraye kirayen sallah dukkanninsu suka tashi mazan suka nufi masallaci yayin da matan sukayi a gida bayan sun idar kuma suka shiga tattare gidan don Daddy yace yau zasu koma gida, suna shirin d'ora girki sai gashi gwaggo ta aiko musu da breakfast mai rai da lafiya. Nan suka amsa tare da godiya aka zauna aka nad'i girkin gwaggo bayan sun gama kuma sukayi wanka Ana ta shirin komawa birni.
Ita dai Hibbah bata so komawarsu ba taso zuwa gidan Abu kodan suka juna ta kuma fad'a mata abinda yake faruwa tasan abu zata tayata murna. Haka ba don tana so ba suka gama shiryawa suka nufi gidan gwaggo don d'aukota su tafi sannan su yiwa malam sallama, da suka je ma itama ta shirya suka kuma yiwa malam godiya suna shirin fita saiga Abu ta shigo ta gaishe dasu momy sannan ta rumgume Hibbah tana murnar ganinta ita ma Hibbah cikin d'auki da murna ta rumgume Abun, Abu tace "na tayaki murna Hibbah naji dad'in wannan al'amari ashe dama rabon kiga dangi ne ya kaiki birni" Hibbah ta kuma k'amk'ameta sai dai taji bata rumgume Abu sosai ba don wani abu ya tokare tsakaninsu Hibbah ta d'an saketa ta d'an matsar da ita daga jikinta tana son ganin mene abun da ya hanasu had'a jiki sosai. Ido Hibbah ta zaro da mamaki tana kallon Abu tayi k'asa da murya tace "Abu me nake gani ciki?" Abu ta d'an buge kafad'art "ni har kin bani tsoro wallahi ji nake wani abun ne, to cikin bashi bane ribar aure"
Hibbah ta rik'e baki tana mamaki wai Abu ceda ciki kenan itama dole ne ta k'unshi nata?" Ta girgiza Kai Anya kuwa zan iya? Abu ta dafata "tunanin me kike yi?" "Ba komai waya fad'a miki nazo garin nan?" Hibbah ta tambaye ta "Abban Amina ne ya fad'a min" kallon ta Hibbah tayi da mamaki "waye kuma Abban Amina?" Abu tace "au a shefa baki santa ba, 'yar da na Haifa ce ta rasu" "au wai kina nufin wannan cikin bashi ne na farko ba? Tab kina k'ok'ari" "k'ok'arin me?" "K'ok'arin d'aukar wannan cikin" dariya ma Hibbah ta Bawa Abu tace "kema zaki d'aukane" Saudat dake gefensu tana jin duk abinda suke cewa tace "tab har na hango Hibbah da k'aton ciki nan kina tafiya da k'yar" ta kuwa kwashe da dariya.
Hibbah ta harareta bata ce komai ba, Saudat ta cigaba "kinga dama Daddy yace nan da sati biyu zaki tare kinga kenan nan da wata tara zamu so suna" Abu ta kalli Hibbah da mamaki "au Hibbah kinyi aure kema?" Da Sauri ta katseta "k'arya fa take yi" Saudat tayi zaraf "wallahi da gaske nake sanadin auren ne ma yasa muka zo garin nan kuma ki tambayi su gwaggo" "na yarda ma wallahi, to ke Hibbah ai ba'a b'oye abin alkhari" ita dai Hibbah bata ce komai ba sai hararar Saudat da take yi.
Suna nan zaune sukaji sallama babban mutum ne wai baba yake nema, baba ya tashi ya fita abinda ya gani ne ya sashi juyowa gida da sauri ya shigo duk a hargitse kallon mamaki su Abba duk suke masa suna tambayar lafiya? Yama kasa magana waje kawai yake nuna musu ganin ya kasa magana yasa suka mik'e suka fita don ganin abinda ya rikita baba.

Inna lillahi kawai suke kira duk sun firgita da abinda suka gani, Inna lami ce da delu a kwance a k'ofar gidan inna k'afafunta sun cire fit babu hannaye ga idanunta ba duk bata gani sai surutai take yi "wallahi Hibbah saina ga k'arshenki dama saida boka halakakke yace karna sake na bari ki dawo k'auyen nan idan kika dawo akwai mummunan al'amari da zai faru kuma na gargad'eki karki dawo amma sai da kika dawo gashi nan munje wajen bokan mun tadda shi yana ci da wuta don haka kema sai na k'onaki" sai kuma tasa wata muguwar dariyar da ta tsorata su duka wajen ga 'yan k'auyen duk sun zagayeta.
Sai da tayi mai isarta sannan ta tsagaita dariyar "na tsaneki Hibbah bazan iya barinki kiji dad'in rayuwa ba shiyasa muka tafi wajen wani bokan yayi amfani dani ya bani wasu k'ullika yace ina komawa gida na barbad'a miki kar na huce awa d'aya ban barbad'a ba, kuma idan na barbad'a miki kina tsallakewa na share kar yayi mintuna biyar ban share ba idan ba haka ba ni ko shi d'aya a cikinmu zai mutu, mun tawo akan hanyar mu ta dawowa mota ta bigemu........" Sai kuma tasa wata muguwar dariya can kuma tasa kuka kamar yarinya wai ciwo jikinta yake mata "wayyo malam jikina ciwo" sai ta kuma sa dariya "malam kaima nice nayi maka asiri don karka koma garinku saboda inasonka bayan nayi maka asiri ne na fad'awa baba shine ya aura maka ni. Kuma nice na rabaka da Aysha da Hibbah nasa ka tsanesu nayiwa Aysha sharrin zina nasa ka rabu da ita Hibbah ma nice na tura mata kwarto d'akintaaaaa!" Sai ta kuma fashewa da da dariya.
Gaba d'aya jikinsu yayi sanyi sai kallonta suke yi hauka take sosai tana ta fad'in abinda ta aikata, delu kuwa dake can gefe ko numfashi bata yi da alama ma ta mutu. Rahmatu da Hibbah sun had'a Kai sai kuka suke yi Rahmatu wani zugi take ji a zuciyarta ace mahaifiyarka na aikata shirka yanzu kuma ta haukace a wajen bin bokayen nata gashi ba hannaye ba k'afafu ba idanu wannan kad'ai ya ishi masu yi isara.
Mijin delu dake gefe ya dubi baba "malam Mukhtar kaga *RAYUWA* ko kaga aikin bin bukaye ko wallahi nayi danasanin kasancewarta mata a wajena Allah ya isa tsakani na dake delu bazan yafe miki ba" daddy yayi saurin kace shi "a'a malam ba'ayi haka ba ba'a bin mamaci da mummunar addu'a kayi mata fatan rahmar ubanjgiji kawai" mijin delu ya gyad'a kai zuciyarsa na k'una yace "Allah yayi miki rahma"
Baba kuwa ya kasa magana su momy kuwa al'ajabin abin ya hanasu magana sai fatan allah ya bata lafiya suke.

Haka dai suka d'auko hanyar garin kano bayan an kai delu gidanta na gaskiya, inna lami kuwa acen suka barta a gidan cikin hauka don baba cewa yayi baza su tafi da ita ba da Abba ya buk'aci su tawo da ita saisu kaita gidan mahaukata amma fafur baba yace aa a barta abinda ta shuka take girba.
Sun dai tawo da Rahmatu da take ta kuka tana yiwa mahaifiyarta fatan samun lafiya don hannunka baya rub'ewa ka yanke ka yar.

Haka suka iso garin kano direct gidan Daddy dake rijiyar zaki suka huce anan suka yada zango, bayan sunyi wanka suka ci abinci aka zauna zaman hutu. Ba jimawa Umma tace ita zata huce gidan mijinta, baba yayi mamaki don shi a tunaninsa Umma bata yi aure ba yana shirin mai data d'akinta sai kuma yaji ashe tana da aure, sai kawai ya kawar da tunanin yana addu'ar Allah ya zab'a masa wadda tafi alkhari.

Daddare duk suka watse Aunty ta koma gidan mijinta da tace da Hibbah zata tafi momy tace a'a ta barta anan tayi zamanta. Kausar ma Faheem d'aukarta yayi suka huce yaso ya d'auki Amaryarsa Hibbah amma Daddy ya hana haka badon yaso ba suka tafi shi da Kausar suka bar mata Nawaz a wajenta don cewa yayi shi a wajen Aunty Hibbah zai zauna.
Rahmatu kuwa da gwaggo sunsha gata da tarairaya gata iri iri. A daren Rahmatu ta haifi 'yarta mace amma 'yar bata zo da rai ba.

Tun dawowar su daga k'auye aka shiga shirye shiryen bikin *Hibbah* da *Faheem* sosau su momy suka shiga kintsa Hibbah da sabulai maya mayai na gyaran jiki Dana sa laushin fata ga turaruka kamar Ana b'arin turare a jikinta ko hucewa tayi ta kusa da kai sai k'amshin ya jima bai baje ba, ga wasu had'i da ake bata kamar me har su Saudat ma sha suke yi don suma an tsaida maganar aurensu, Saudat kuwa sun daidaita da Usman d'an Abba ita kuwa Safiyya wani saurayinta ne Yusif.
Faheem kuwa duk ya k'osa a kawo masa matarsa baya iya jure rashin ganinta a kusa dashi shiyasa kullum yana hanyar zuwa gidansu don ganin abar k'aunarsa. Momy da mamy har gwaggo sun gane take takensa shiyasa suka kuma d'aura d'amarar gyara Hibbah.
Su Aunty ma sun fito da anko kala biyar wai bikin 'yar gata za'a yiwa Hibbah, mamy ce ta had'o mata lefe na gani na fad'a........

*#Juma'at mufeedah to you all my fans😍❤🤝*

*by*
*Mamyn Najmah*
[10/26, 9:27 PM] Maman Najma Author P1: 📝🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓

*RAYUWA* page 5⃣4⃣

*NA*
*MAMYN NAJMAH*

🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓

*DEDICATED TO AYSHA ALIYU GARKUWA*

```wattpad@mamyn_najmah2222```

*wannan page d'in d'ungurin gum na sadaukar dashi gareku masoyan littafin RAYUWA ina son Ku ina jinku a zuciya ta, Kuyi hakuri bakwa jina kwana biyu wallahi bana samun time ne.*
Chapter 51 · 0% Book details