← Book details Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 54

Sashe 37

Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Faruq kuwa yana fita daga gidan Aunty cikin b'acin duk inda ya wuce sai an dube shi kamar mai shirin barin garin, gudu yake sosai a mota bai tsaya a ko ina ba sai a night club, idanuwannan a hargitse banda masifa babu abinda yake ji ransa a mugun b'ace yake ji yake kamar ana tsigar gashin kansa, tabbas da yana da bindiga da sai yayi gangancin harbin Aunty Aysha mene amfanin mak'iya a duniya ya tabbatar yanzu bashi da makiyi kamarta.
Kid'a ne yake tashi kamar zai tsaga ginin wajen, ya zauna yana muzurai kamar wani kumurcin maciji, ya d'auko sigari ya kunna mata wuta wai ko zai rage zafin abinda yake ji, ya dubi mashaya barasa kala daban daban yakanji a wajen abokansa wai giya na gusar da mummunan tunani da kauda bak'in ciki ga d'an karan dad'i amma shi bai tab'a sha'awar Shanta ba, ya kansha ganye da wasu kwayoyin shima tun lokacin yana secondary school tare da tak'adiran abokansa da suke kiran kasu bad boys, amma tuni ya manta dasu shidai burinsa yaga macen da yake ra'ayi kawai yayi mu'amalarsa da ita.
Hankalinsa ya kasu biyu ya kalli barasar yana kwad'ayin lasawa ya wurga idanunsa yana kallon kangararrun matan dake shawagi wurin duk baiga Wanda ransa ya biya ba don haka ya yafito hadimin wajen da hannunsa. Da harshen turanci ya gaisheshi cikin ladabi "barka da dare me kake buk'ata" ya mik'a mishi wata takarda da jerin nau'ikan barasa, ya karb'a yana d'an nazari sai ya yatsuna fuska "kowanne ka kawo" don bai san wanda xai zab'a ba. Ya dire tray da manyan kwalaban giya masu sanyi, ya d'auki guda d'aya idanunsa sun shige ciki ya k'ura mata idanu, yana tunani zuciyarshi yasha ko karya sha, ya sha kawai koya huce zuciayarsa ta raya masa. Yana kaiwa bakinsa ta karb'e kwalbar, ya cira ido da k'yar ya dubeta, siririya ce doguwa Fara Sol, tana sanye da wani bulun skirt iya cinyarta da wata 'yar figigiyar riga data manne a jikinta. Ta zauna gami da rik'o hannayensa da wani asirtaccen murmushi akan fusakarta tuni tayi awon gaba da tunaninsa, Rita kenan yana son yarinyar don tasan ta kanshi sosai da ranshi ya b'aci zata sauko da fushinsa. Ya kewaya hannunsa a k'ugunta suka mik'e suka hau sama don cin karensu babu babbaka.

****

Bak'in hadarin daya taso da wata iska mai k'arfi, sannan ruwan ya sauko yana tarwatsewa bisa glass d'in motar yana sauraron wak'ar Dr Mamman shata, yau dai yana cikin annashuwa yana tunanin maganganun Umman Hibbah sun sashi farin ciki har yana hangen wata *RAYUWA* a gaba da zasuyi dole ne yayi azumin godiya ga Allah daya cika masa burinsa ya mallaka masa abinda yake matuk'ar so,shikenan ta zama mallakinsa.
"Karka damu komai nufi ne na Allah, nayi farin ciku da jindad'i tsakaninku da yarinyar nan amanace, wannan ita ce k'auna domin Allah sai addu'ar alkhari, Allah ya tabbatar da alkhari zan fad'awa Alhaji yanzu daya shigo ayi komai a yau d'in nan a gama."
Yayi ajiyar zuciya ya tuna maganganun masu dad'in sauraro, wannan wani sirri ne daga shi sai Allah sai kuma Umma data share masa hawayensa, tura ce takai bango har yaji bazai iya zama da kashi a ciki ba don baya maganin yunwa, don haka ita kad'ai tasan maganar ya dad'e da gamsuwa da halin dattako irin nata, don yasan zata taka rawar gani ta magance masa matsalar data addabeshi shi, shiyasa ya kai mata ziyarar gaisuwa da rok'on iri kamar uwa ya d'auketa ba suruka ba.
Yana parking ya k'ura mata idanu ta cikin glass d'in motar, tana rik'e da lema tana tarar ruwan saman a wani bokitin roba shi kuma Nawaz yana Tara nashi cup d'in yak'i taruwa, ta dinga yi masa dariya ya shammaceta ya ture nata bokitin ruwan ya zube, sai ya hau shima yi mata dariya harda tsalle yana k'yak'yata mata dariya k'ya k'ya k'ya. Ta lura da motar Faheem don basu ji shigowarsa ba saboda ruwan da akeyi a tunaninta bazai fito ba saboda ruwa karya jik'asa, ga mamakinta fitowa yayi abinsa, Nawaz ya dinga d'aga masa hannu "Daddy Daddy ruwa zai dokeka ka gani ya jik'a ka" ya karb'e lemar daga hannunta yana kallonta, ta sunkui da kanta "Hibbah" wannan lafazin na Faheem sai taji.muryar tashi ta canza "baki kawo min lema ba kin Bari ruwa ya jik'a Daddy'n Nawaz."
Ya ilahi, ita dai wani abu take ji tamkar zata fad'i k'afafunta suka d'auki rawa, ya zuba Mata idanu kawai yayi nisa ya tafi da yawa ikon Allah haka so yake Allah ya had'aka da Wanda baka tab'a tunani ba. Kamar bata motsi kunya da nauyinsa sun rutsa da ita.
Shi da kansa ya samu damar da yake jira yasa Hibbah ta fad'a tarkonsa yau k'wauron baki ya k'are zai fasa k'wai. "Hibbah" da sauri ta juya da gudu cikin gida, yayi d'an murmushi yana Mai jinjina wannan irin kunyar ta Hibbah.
D'akinta ta shiga ta d'ora kanta a bisa pillow zuciyarta kamar tana harbawa idanunta Faheem kad'ai take gani kamar cikin cikin film wannan abu yak'i goguwa nauyi ne tsoro ne ko kuma kunya me yasa haka? Faheem dodo ne? Tsabar cika ido da kwarjini ne ta bawa kanta amsa. "Hibbah" yadda yake futawa take tunawa a tausashe sai taji kamar yafi kowa iya furtawa. "Aunty Hibbah kizo inji Daddy" zumbur ta tashi zaune ta kad'a kanta "to ina zuwa"
Ta jima tana sak'a da kwancewa me ya hanata fita kiran Faheem don fa ya rud'ata nauyinsa ya k'aro.
Ya bud'e k'ofar ya shigo, ta dubeshi ya jingiba bayansa da k'ofar ta saci kallonshi wata k'atuwar rigar sanyi sanyi ya Santa mai taushi kamar gashin jikin mage, ya cire hular jikin rigar daga kansa gami da Santa hannayensa cikin aljihun rigar. "Hibbah" sai da ta kad'u sassanyan kiran ya ratsa zuciyarta "Hibbah ni gani nazo tunda na aiko ki zo kin k'i fitowa ni d'in............

*by*
*Mamyn Najmah*
[10/26, 9:26 PM] Maman Najma Author P1: 📝🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓

*RAYUWA* page4⃣0⃣

*NA*
*MAMYN NAJMAH*

🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓

*DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION*

D.B.W.A

*DEDICATED TO AYSHA ALIYU GARKUWA*
Chapter 37 · 0% Book details