← Book details Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 54

Sashe 15

Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*A*unty tana bud'e k'ofar ta danno kai cikin d'akin abin da ta gani ya d'aga mata hankali, Faruq ne akan ruwan cikin Hibbah daga shi sai trouser ita kuwa ya cire mata Riga bra ce kawai a jikinta sai skirt d'inta dake manne a k'ugunta, kukan kura aunty tayi cikin b'acin rai ta hankad'e shi ya fad'i k'asa. Ta d'ago Hibbah a gigice take kiran sunanta amma Hibbah ko motsi batayi, hankalin aunty ya kuma tashi ta kalli Hadiza dake tsaye gefe tana kallonsu duk jikinta yayi sanyi bata tab'a kawo Faruq da wata manufa yasa Hibbah ta gyara masa d'aki ba, Aunty tace "baba Hadiza dan allah bani ruwa yarinyar nan suma tayi," gaban fridge d'in Faruq ta daje ta bud'e tare da d'auko gorar ruwan faro ta bud'e ta mik'awa Aunty. Da azama Aunty ta amsa ta tsiyayo a hannunta ta shafawa Hibbah a fuska, wata sanyayyar ajiyar zuciya Hibbah tayi tare da bud'e idanunta a hankali karaf ta zubesu ana Faruq, wata zabura tayi cikin rud'u ta mik'e zaune tana k'ok'arin sauka daga gadon, rik'ota aunty tayi tana Mata sannu.
Bata saurari Auntyn ba sai cigaba da k'ok'arin kwace kanta da takeyi tana nuna mata Faruq cikin muryar data sha kuka har ta fara dashewa tace "Aunty Dan Allah ki taimakeni, Faruq kasheni zaiyi wallahi Faruq Bashi da tausayi," ta tusa kanta a tsakanin cinyoyinta ta cigaba da kuka, murmushi Faruq yayi Wanda kana gani kasan na mugunta ne donshi ko damuwa baiyi ba towel ma ya d'auko tare da d'aurashi a k'ugunsa yana shirin shiga wanka, Aunty ta sauko daga gadon cikin tsananin b'acin rai take yi masa wani mugun kallo ta k'arasa kusa dashi tare da fizgoshi yayi baya ta shiga marinsa da Kai masa duka ta ko ina, cikin zafin nama ya rik'e hannunta b'acin rai kwance a fuskarsa yake bin Aunty da kallo, itama Auntyn kallon fuskarsa take abinda ta hango a cikin idanunsa ne yad'an sa zuciyarta tad'anyi rawa, da wata murya yake magana"Aunty Aysha kin tsaneni kin takurani bakya k'aunar kiga farin cikina ko kad'an, me nayi miki kika tsaneni? Gashi yanzu lokaci d'aya kin har gitsamin shirina kin fifita bare 'yar aikitau a kaina" cikin bacin rai yake maganar. Fizge hannunta Aunty tayi itama cikin zafin rai tace "ban tsaneka ba Faruq halinka na tsana, amma tunda kace na tsane ka to na tsane ka d'in, kuma ina kaunar Hibbah a zuciyata fiye dakai bakayi k'arya ba na fifita Hibbah fiye da Kai saboda ta fika halaye kyawawa, kuma wallahi kaji na rantse sai na fad'awa momy duk abinda ka aikata," murmushi yayi ya d'aga kafad'a yace "I don't care kuma ki rubuta ki ajiye wallahi saina kusanci wannan yarijyar kota halin k'ak'a," yana gama fad'in haka yayi hanyar shiga toilet, aunty tace "to mugu mai bak'ar zuciya yanzuma kazo ka aikata k'udirinka akanta ta Allah ba taka ba, ya d'aga kafada alamar ku ta shafa ya shige toilet.
Shiru aunty tayi kafin ta kalli Hadiza tace "baba Hadiza pls kamamin ita mu fita da ita bata da karfin takawa," Hadiza tace to" tare da k'arasowa suka kama Hibbah suka fita da ita, tana rik'e da kanta inda Faruq ya buga Mata har ya fashe jini na d'isa d'is d'is. A parlor aunty ta d'auki mayafinta ta kalli Hadiza tace "bara na kaita asibiti ayi mata treatment kinga jini na zuba," Hadiza tace "eh gaskiya nima Bari na d'auko mayafina mu tafi tare," girgiza Kai Aunty tayi tace "a'a baba ki barshi, kije ki k'arasa aikin ki kinga yamma nayi bara muje mu biyo sai mun dawo," aunty ta fad'a suna fita daga parlor'n,Hadiza ta rakasu tare da binsu da addu'a.
Suna fita Aunty ta yiwa Adamu driver magana yazo ya kaisu asibiti, jiki na rawa Adamu ya fito da motar suka nufi asibiti, direct asibitin da suke zuwa suka nufa suna zuwa doctor yayi mata treatment d'in wajen ya basu magunguna sukayi godiya suka tawo.
A hanyarsu ta dawowa momy ta kira wayar Aunty take tambayar ta har yanzu bata zoba, aunty tace "wallahi momy da akwai matsala ne a gidan shiyasa banzo ba yanzu ma muna kan hanya mun dawo daga asibiti," cikin d'an hargitsi momy tace "matsala? Wace irin matsala Aysha? Waye ba lafiya?" Aunty ta kalli Hibbah dake gefenta tace "wallahi momy Hibbah ce ta samu rauni a goshinta amma da sauki ma" "a garin yaya Aysha?" Momy tayi tambayar cikin nuna damuwa. Aunty tace "ki kwantar da hankalinki momy ba wani ciwo bane, magana a waya bazai ba," momy tace "to shikenan allah ya bata lafiya, muma da anyi sallah zamu tawo" aunty tace "allah ya dawo daku lafiya," momy tace "ameen" tare da kashe wayar. Ta kalli Hibbah tace "sannu kinji Hibbah, babu abinda ya isa yayi miki Wanda Allah bai miki shiba, zan fad'awa momy da daddy duk abinda yakeyi nasan sai daddy yad'au k'wak'wk'waran mataki akansa," juyowa Hibbah tayi suna fuskantar juna tace "Aunty dan allah karki fad'awa kowa wannan abun, mu musilmi ne kuma ko wane bawa akwai k'addarar da Allah yake jarrabtarsa da ita, nasan ni wannan itace k'addarar da Allah ya d'oramin ta *RAYUWA*, ni na yarda da ita. Aunty a sharad'an imani yarda da k'addara yana ciki kuma imanin musilmi bazai tab'a cika ba har sai ya yarda da k'addara mai kyau ko mara kyau, don haka na yarda da wannan a matsayin k'addarar *RAYUWA* ta." Aunty ta kalleta k'aunarta na dad'a shiga ranta yarinya ta bata tausayi tace "Hibbah nasani wannan k'addara ce amma ki sani bafa a kanki Faruq ya fara wannan abin ba, Faruq har night club yake zuwa saida yaga daddy ya bud'e masa wuta sanan ya daina ashe ba dainawa yayi ba don kafin Ya Faheem ya tafi saida ya fad'a min bai daina ba amma nak'i yarda ashe kuwa bai daina ba d'in," Hibbah tace "Aunty waye kuma Ya Faheem?" Aunty tayi murmushi tace "baki sanshi ba Hibbah shine babban yayanmu, kafin kizo da sati d'aya ya koma abroad zaiyi wani cause yana da aure matarsa d'aya Kausar da yaronsa Nawaz anayin arba'in d'in Nawaz ne ma suka tafi." Girgiza kai Hibbah tayi tace "Dan allah karki fad'awa kowa Aunty" aunty tace "to naji bazan fad'awa kowa ba amma in one condition," Hibbah yanxu tana d'an fahimtar turanci ba laifi shiyasa ta fuskanci me Auntyn ta fad'a, Hibbah tayi murmushin jindad'i tace "to mene sharad'in?" Aunty ta kalleta tace "kiyi min alk'awarin zaki kwantar da hankalinki baza kisawa kanki damuwa ba," Hibbah tace "don wannan to nayi miki Aunty," "yauwa Hibbah na ammafa zan fad'awa momy saboda kinga na Fara fad'a mata ta waya," Aunty ta fad'a tana kallon Hibbah.
Hibbah tad'an had'e rai tace "a'a aunty itama banaso taji pls," girgiza Mata Kai aunty tayi tace "Hibbah kina so nayiwa momy k'arya?" Girgiza kai Hibbah tayi tare da cewa "a'a Aunty" Aunty tayi murmushi tace "to indai ba so kike muyiwa momy k'arya ba to mu fad'a mata." Hibbah ta d'an turo baki tace "to a fad'awa momy amma dan allah kice mata itama karta fad'awa kowa har daddy." Aunty tayi murmushi tace "to shikenan babu wanda zaiji." Hibbah cikin jin dad'i tace "yauwa Auntyna na gode," aunty ta d'an harareta tace "na fad'a miki bansan yawan godiya ko," rik'e bakinta Hibbah tayi tace "to na daina, amma Aunty inason na tambaye ki," aunty tace "you are free ina sauraronki," Hibbah tad'an muskuta tace "uhmmmm Aunty kiyi hakuri da tambayar da zanyi," aunty ta kalleta sosai tace "kiyi tambayar ki Hibbah matambayi baya b'ata" shiru Hibbah tayi tana jin nauyi tambayar tana kuma ganin kamar ta zak'e da yawa idan tayi tambayar tace "Aunty shikenan ma kawai ba sainayi tambayar ba," harararta Aunty tayi tace "ai kuwa baki isaba saikin fad'amin, fad'i ina sauraronki," kallon aunty tayi taga ta b'ata rai sai taji bataji dad'i ba tayi k'asa da kanta tace
"Aunty wai momy tana da abokiyar zama ne?" Aunty taji tambayar a wani iri ta kalli Hibbah sosai tace "me kika gani Hibbah?" Kuma sunkuyar da Kai Hibbah tayi tace "kiyi hakuri aunty idan maganata ta b'ata miki rai, naga gidan ku babba ne kuma b'angare uku ne a gidan." Dariya aunty ta d'anyi tace "baki b'ata min ba Hibbah, kuma bara na fahimtar dake, wannan b'angarorin da kika gani kowanne dame shi, kinga da bangaren mu dana Abba da kuma na hajiya kaka. Haka daddy yayi tsarin ginin, daya gama kuma hajiya kaka tace ita baza ta zauna ba shine ya bawa Ya Faheem part d'inta, shi kuma b'angaren Abba sai yazo kano yake zama a ciki da iyalansa a Abuja yake aiki," Hibbah ta girgiza Kai alamar gamsuwa, a ranta tace ko waye Abba d'in?
Aunty ta kalleta tana dariya tace "bara ma fad'a miki waye Abba don nasan zaki iya tambaya, Abba abokin daddy ne sosai tare suka taso tun suna yara, iyayensu ma aminan junane hakan yasa wasu suke tunanin ko 'yan uwane, amincin dake tsakanin su ne yasa suka zama tamkar tagwaye, d'aya baya tab'ayin abu saida d'an uwansa, sannan matar Abba ma k'anwar daddyn mu, Kausar ma matar Ya Faheem ma 'yar Abba ce, Abba yana da yara biyar Ya Haisam shine babba sa'an ya Faheem ne, sai Kausar wadda sa'a tace, sai Usman, Mubarak sai autar su Janan, yanxu kin fahimta?" Hibba ta d'aga Kai.
Da haka suka k'ara gida suna ta hirarsu kamar babu abinda ya Faru.
Chapter 15 · 0% Book details