Sashe 21
Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
Sai bayan sallar maghrib suka shigo da daddyn shi, suka nufi dinning suna cin abincin Kausar ta shigo da sallama ta ajiye Jakarta akan kujera itama ta zube a kan kujerar tace "wash Allah, daddyn Nawaz yau har ka yo take away d'in kenan," Faheem bai kulata ba saida suka k'araso inda take da yake sun gama cin abincin ya zauna a d'aya daga cikin kujerun parlor'n yace "a'a aini yanxu na wuce wannan wajen, Aysha ce ta bani shawarar kawo mai kula min da gida ta kular min da yaro tunda ke kin zab'i aikinki akan mijinki da iyalanki," maganar ta yiwa Kausar zafi "haba daddy'n Nawaz kaima fa kasan yanayin aikina, kayi min uzuri mana," "wane uzuri zanyi miki Kausar? Bayan hakurin zaman da nake yi dake yanxu," maganganunsa sun fara yi mata zafi ta kalli Nawaz a tsawace tace "Nawaz kira yarinyar da tazo Kace ta kawo min abinci," Nawaz ya kalleta a d'an ta yace "to momy bara na k'arasa kallon wannan film d'in," "dallah ka tashi kaje ka kira min ita," Kausar ta fad'a tsawace da gudu Nawaz ya fita duk ya tsorata.
Faheem ko kallon ta baiyi ba sai wani cika take tana batsewa, Nawaz ya dawo Hibbah na biye dashi suka shigo parlor'n da sallama Faheem ne kawai ya amsa ita kuwa ko kallonta bata yi ba tace "ke zubo min abinci," Hibbah tace to" ta nufi dinning ta zubo mata abincin ta kawo gabanta ta ajiye, tana shirin tafiya Kausar tace "keehh" Hibbah ta juyo ta kalli Kausar tace "na'am aunty," cikin mamaki Kausar ta mik'e "ke meya kawoki gidana?" Ta kalli Faheem "badai wannan ka kawo min a matsayin 'yar aiki ba," yayi mata kallon gefen ido "a ina kika ganta? Ina ce a cikin gidan nan kika ganta kuma na miki bayanin ai ko?" Tace "haba Faheem ya ina tambayar ka kana yi min magana a duk'unk'une," bai kulata ba ya kalli Hibbah yace "tashi kiyi tafiyar ki," "ke dawo karki sake ki koma min cikin gida mayya kawai," cikin masifa Kausar take mata magana, cikin tsawa Faheem ya d'aga mata hannu "ya isheki Kausar baki isa ki hana Hibbah zama a gidana ba, ni na kawota cikin gidannan kuma ko kinaso ko bakyaso dole ne ta zauna," ya kalli Hibbah yace "ki tafiyarki ciki babu Wanda ya isa ya hana ki zaman gidan nan," Hibbah ta nufi cikin d'akinta.
Kausar kuwa takaici ne ya isheta tasan halin Faheem sarai yanxu zai dizgata a gaban yarinyar nan, ta suri jakarta tana ta mita ta shiga ciki.
Faheem ko kallonta baiyi ba ya cigaba da kallon news, Nawaz ya kalli daddyn shi yace "daddy ni yau a wajen aunty zan kwana," Faheem ya kalleshi "a'a Nawaz zakaje ka takurawa Hibbah ne da surutu ne kawai," "daddy bazan yi mata surutu ba," "to shikenan kaje ka canza kayan naka sai kaje Ku kwanta," Nawaz ya tashi yana murna yaje ya canza kayanshi ya tafi d'akin Hibbah, ya shiga da sallama waya yaga tanayi tace "aunty kiyi hakuri zanzo amma ba yanzu ba, saina daina xuwa islamiyya tukunna," daga can aunty tace "yaushe ne zakuyi walimar ne Hibbah?" "Next week Sunday," Hibbah ta hawa aunty amsa, "to Allah ya kaimu," "ameen Aunty," Nawaz ya matso kusa da ita "aunty bani mu gaisa da momy Aysha,," Hibbah ta mik'a masa wayar suka gaisa da aunty sannan sukayi sallama ta kashe wayar.
Ta kalli Nawaz tace "Nawaz daddy ne yake Kira na?" Ya girgiza kai "a'a aunty nazo mu kwana tare ne," "ok to zo muyi alwala sai mu kwanta," suka mik'e suka d'auro alwala suka yi addu'a tare da kwanciya.
Da safe Hibbah ta tashi tayi duk wani aikin gidan sannan tayi wanka tayiwa Nawaz ta shiryashi sukayi breakfast ta wanke cups d'in, da rana ma haka tayi musu girki hakama da dare.
Haka Hibbah ta cigaba da yi musu bauta a gidan amma Kausar bata tab'a yi mata koda kallon aizik'i ba balle ta samu godiya daga wajenta. Da haka har ranar walimar su Hibbah tazo, aunty da umma sunyi bajinta kwarai don duk wani abu da akewa 'yar gata da walimarta haka sukayi wa Hibbah ta fito kamar ba ita ba, haka taro ya tashi aka sallami 'yan sauka aka basu allon su tare da kyaututtuka.
***
Watan Hibbah d'aya agidan har ta Saba sosai kullum sai tayi komai na gidan take tafiya school, daddy kuwa Nawaz yake aikowa ya kai mata kud'in motarta.
Ranar lahadi Faheem yana gida da wuri Hibbah ta gama komai ta kira Nawaz tace "Nawaz jeka fad'awa daddy zamuje gidan Aunty," Nawaz yace "nima zani gidan momy Aysha," tace "to jeka fad'awa daddy kazo mu tafi," ya juya cikin happy ya tafi wajen daddyn nashi dake harabar gidan yaje yace "daddy wai inji Aunty Hibbah zamuje gidan momy Aysha," Faheem yaji dad'in yarda Hibbah ta bashi girmansa ya zaro kud'i a aljihunsa ya mik'awa Nawaz "ka kaimata Ku hau mota kuce ina gaishe da Aysha," Nawaz ya amsa ya kawo wa Hibbah kud'in.
Hibbah ta shirya cikin wata atampa yellow da ratsin royal blue tayi kyau sosai ta shirya Nawaz suka fito titi Neman adaidaita. Da k'yar suka samu suka nufi gidan Aunty.
*by*
*Mamyn Najmah*
[10/26, 9:23 PM] Maman Najma Author P1: 📝🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓
*RAYUWA* page2⃣9⃣
*NA*
*MAMYN NAJMAH*
🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓
*DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION*
D.B.W.A
*DEDICATED TO AYSHS ALIYU GARKUWA*