← Book details Mahaifin Mu Ne Sila Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 31

Sashe 7

Mahaifin Mu Ne Sila Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Safwaan ne ya mike da kyar sai kuma yace"abba ni zan tafi office sai na dawo, kallon sa yayi sai kuma yace"karka fita daga gidan nan,saurin kallonsa umma tayi, take nima abinda ya bani mamaki idanunsa ne suka fara sauya kala daga fari zuwa baki,umma ce taja hannunsa zuwa wani kofar dakin wanda dakin ya kasance da kyauren karfe sabanin na gidan daya kasance na katako mai kyau.

Abba ne ya fito daga gidan cikin jerin motocin da suke waje ya za6i wata ash ya shiga sannan ya fita daga gidan.

✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

*MAHAIFIN MU NE SILA*

*By*
_*WALEEDA MUHAMMAD*_

         QUEEN WALEEDAH

   _HAZIƘAI BIYAR DAGA_👇

*✨TAURARIN MARUBUTA WRITER'S ASSOCIATION✨*

        *T.M.W.A.✍️*

✨✨✨✨✨
       💪😊

*TUNANI MAI ZURFI KAFIN RUBUTU SHINE TAKEN MU, RUBUTU MAI FAD'AKARWA DOMIN AL'UMMA,AL'K'ALAMIN MU ABIN AL'FAHARINMU, RUBUTU BAIWA CE GA WANDA ALLAH YA BAWA,TAKENMU SHINE HASKAWA A CIKIN AL'UMMA DA FIKIRAR DA ALLAH YA MANA, TAURARU A DUNIYAR MARUBUTA.*

✨✨✨✨✨
        💪😊

https://whatsapp.com/channel/0029VbB4z8xCnA7sRc849y0F

Whatsapp Channel

Page 11

Najwa ce ta fito da kwano a hannunta, cikin rashin sani ta take kafar nabila, nabilar ce ta kalleta tace"ke yaya najwa kina ji kika bigemin kafa, cikin jin haushi tace"to sai me idan kuma kin cika kizo ki rama, kowa na wajen buda baki yayi yana kallon najwa, wadda take a tsaye tana jiran ko akwai mai mata magana, nabilar ce ta mike taje gabanta tace"yaya najwa nace kin taka ni,kallonta tayi sai kuma ta tsugunna ta fara kyakyata dariya kamar wata sabuwar kamu.

Umma kallonta tayi kawai ta kauda kai domin tasan tabbas wanann abin yana daya daga cikin dabi'ar najwa a iya wannan shekarar da take kokarin shiga, fahad ne yace"haba yaya najwa ki bata hakuri mana, dariya taci gaba da yi sai kuma ta tashi ta fita da gudu, nabila fahad suka bi bayanta da gudu,abin mamaki shine dik inda ta wuce sai dai kuga wajen ya zube, idan kuwa bishiya ce sai dai kuga ta kama da wuta hakanne ya kara tsorata ni, amma dik da haka banja baya ba sai binta da nayi.

Gudu take a iya lokaci daya ta bacewa su nabila, dai dai wajen shagon mai nika naga ta tsaya, wannan dajin shi ta kalla sai kuma naga ta tattare zsnen jikinta ta shiga wajen da gudu.

Fahad,nabila da zainabu nemanta sukeyi, yayin da al'ummar garin ke neman dauki domin kuwa mafi akasari tayi musu 6arna,dan dik yawancin kauyen rumbun nan sun kama da wuta,su suna neman najwa su kuma suna kukan kamawa da wutan da garin yayi.

☄️☄️☄️☄️☄️☄️☄️☄️☄️☄️☄️☄️

Safwaaan ke fara jijjiga kofar wadda ta kasance ta karfe ce, umma ganin haka yasa ita ma tabi bayan abba bayan fitarsa,cikin abinda bai fi abinda mintuna 10 ba ya karya kofar, wani gurnani naji da sauri naja baya,safwaaan cikin wani irin yanayi gaba daya jikinnsa ya chanja daga fari zuwa baki, yayin da wasu irin gashina suka firfito masa, da gudu ya fita daga dakin ya bar gidan ma gaba daya.

Umma ce ta ga fitarsa daga gidan ta saman bene da sauri tabi bayansa, kallon mai gadin tayi tace"kai wane irin shashasha ne haka,yaushe zakayi hankali, dan allah taya zaka barsa ya fita a wanann yanayin, shiru yayi sai kuma can ya nuna mata gate din gidan, ganinsa tayi a kasa da sauri ta leka waje amma abinda yayi matukar bata mamaki babu shi babu alamunsa, a wajen ta durkushe tana saka kuka.

Ji tayi an dafa ta bata juyo ba dan tasan ko a mafarki tasan da cewa sakina ce kadai wadda zata dafa ta, a wanann lokacin har an fara kiraye kirayen sallar isha'i, daidai lokacin da motar abba ta nufo gida, cike da tashin hankali tin daga nesa ya fito yana mai furta"inalillahi wa inna ilaihi raji'un, kallon umma yayi ko ma yafi babu bare hijabi.

Da kyar ya lallabata ta shiga ciki sannan ya yace"lafiya cikin kuka mai tsuma zuciya tace"to ai gashi nan koma menene wacece sila habiba ce da 'yarta, gashi yanzu ya bar gidan, ya fice ma daga gidan sam an nemesa an rasa, na saka yara su duba mini amma babu shi babu alamunsa,inalillahi wa inna ilaihi raji'un, ni ameenatu allah ka bani ikon cinye e wanan jarabar.

Ciki yayi sai kuma ya juya ya dauki motarsa yana kallon yanayin amina da ta gama fita daga hayyacinta da kuka a idanunta, sai kuma naga ta tashi da kyar ta sgige ciki.

☄️☄️☄️☄️☄️☄️☄️☄️☄️☄️☄️

Alhj gambo ne ya fito daga mota yana parking daidai wani kaaton hotel,cikin abinda bifi mintuna 2 ba wasu escorts suka zagaye sa kowanen su sanye da bakaken kaya da wata katuwar bindiga wadda ina da tabbacin da an harbawa mutum ba lalle ya sake tashi ba sai dai idan ajalinsa ne bai yi ba.

Taka step din wajen yake yana kallon kowa yana muzurai kamar wani tsohon zaki,daidai wani dan karamin room ya tsaya sai kuma naga ya daga musu hannu alamun su dakata anan, kowanen su kamewa yayi yana mai jiran umarnin shugaba, yadda kasan basu ta6a dariya ba.

Shiga yayi a zaune wani mutum ne fuskarsa da kasumba cike tuli,gani nayi ya kalli mutumin take suka kwashe da dariya, dayan ne yace"sam alhj gambo baka duba time kasan tin yaushe na adana maka kayan can kawai dan saboda biyan buqatarka,murmushi Alhaji gambo yayi yace"shege ghali nifa nasan kai din zaka iya, turus yayi yace"aa gambo taya bazaka hada da alhaji ba, kasan dai ni tawa alhajin bada kudi na sayeta ba ko, tin kafin na shiga inda nake yanzu naje hajj ko.

Dariya gambo yayi yace'amma ga hajj din bata hana ka fadawa cikin wanann kungiyar ba ko, kuma banda abinka banason tone tone, yanzu dsi muje sai na za6a domin ni kaina so nake yau na cika umarnin shugabanmu.

*MAHAIFIN MU NE SILA*

*By*
_*WALEEDA MUHAMMAD*_

         QUEEN WALEEDAH

   _HAZIƘAI BIYAR DAGA_👇

*✨TAURARIN MARUBUTA WRITER'S ASSOCIATION✨*

        *T.M.W.A.✍️*

✨✨✨✨✨
       💪😊

*TUNANI MAI ZURFI KAFIN RUBUTU SHINE TAKEN MU, RUBUTU MAI FAD'AKARWA DOMIN AL'UMMA,AL'K'ALAMIN MU ABIN AL'FAHARINMU, RUBUTU BAIWA CE GA WANDA ALLAH YA BAWA,TAKENMU SHINE HASKAWA A CIKIN AL'UMMA DA FIKIRAR DA ALLAH YA MANA, TAURARU A DUNIYAR MARUBUTA.*

✨✨✨✨✨
        💪😊

https://whatsapp.com/channel/0029VbB4z8xCnA7sRc849y0F

Whatsapp Channel

Page 12

11:00pm

Abba ne ya karyo kan motarsa, abin da ya bashi mamaki ganin har yanzu umma na wajen a zaune, sai dai yanzu da hijabi a jikinta, gefe kuma sakeena ce tana share hawaye,parking yayi bai dade da parking wata motar naga ta tsaya anan ne naga ashe masu gyara gate din ne.

Karasowa yayi wajenta ya kama hannunta, sanann suka juya suka koma zuwa cikin gidan, ba kowa a falon hakan ya ba su damar zama a falon, sai kuma sakennah data mike zatar wajen,abba ne yace"sakina ina zaki, da kyar tace"kwanciya zanyi abba gibe munada exams a school,zauna inason magana daku, ki huce kije ki kiramin safna da mahaifiyarki.

Sakeena ce tace"tohm abbah sannan ta huce, umma ce ta kalli abbah bayan ta fita daga dakin tace"haba abbah taya zaka ajiye wannan takardar a wannan dakin gashi yanzu tazo ta gani kuma tayi sanadiyyar barin safwaan gidan nan, abba ne yace "kiyi hakuri aminatu na bada cigiyarsa kuma insha allahu zai dawo kamar yadda ya tafi sannan ni kaina ba haka zan zauna ba, zanci gaba da yi masa addu'ah.

Daidai lokacin sakina ta dawo tace"abba na fada musu tace" gata nan, zama tayi tana jiran fitowarsu, sunfi mintuna 20 sanan sai gasu sun fito tare, safna ce daga ita sai wamdo da riga iya gwiwa, ita kuma habiba atamfar dazu ce.

Bayan sun zauna abbah ne ya kalli habiba yace"yanzu ke habiba kin kyauta, waya baki izinin shiga daki na, habiba cike da gadara tace"auuh dama a matsayinka na miji na dole sai na nemi izini kafin na shiga dakinka, to na shiga kuma dik abinda kakeji zakayi sai dai kayi, domin ni ba wanda ya isa ya hanani shiga dakin ka.

Abba bai kara mata magana ba sai ya juya ya kalli safna da sakeenah yace"yanzu a kanku zanyi magana, safna sakina a matsayina na mahaifinku, nauyin kula daku yana kaina dan haka a wannan lokacin kuma na yanke hukuncin yi muku aure.

Sannan kuma na fitar muku da mazajen da suka kwanta min, insha allahu zuwa nan da jibi za a daura muku aure kamar yadda addinin musulunci ya tanada, kuma bai rufe bakinsa habiba tace"wallahi abba ba wanda ya isa yayiwa yarana auren dole, auren dole fa kake kokarin yi musu, to wallahi bazai yiyu ba, kallonta umma tayi dik da tana cikin damuwa hakan bai hanata furta "haba mana habiba wanann fa mijin mu ne ko banza ya kamata kina darajasa, tinda shi saurin katseta tayi tana fadin" ke dalla shashasha rufe min baki, aikin banza aikin wofi, to ka sani ko auren nan sai dai kayiwa waccan shashashar badai safna ba.

Cikin 6acin rai tace"ya isheki habiba,, ya isa haka karki nemi ki maidani danki mana, to ki tabbatar da cewa ko ta fito da miji kafin nan kafin jibi ko kuma na bata dik wanda naga dama, wannan maganar bazata chanja ba wallahi kuma ki sani dik abinda ya faru bayan auren karta kuskura ta dawo min gida domin ni bazan iya zama da safna ba haba sai kace ba ciki daya suka fito da sakina ba.

Sam sakina ta fita hankali ta fita nutsuwa da sanin yakamata, gata karama amma sam ba hanya daya suka dauka ba, duba kiga ita yanzu bata dadewa a makranta, bata 6atan rai amma ke (yana mai nuna safna) maganar yau daban ta jibi daban to ki sani ladan rashin mutumcin da uwarki tasa kikayi wa yayanku shi ne ki tabbatar kin kawo min miji ko kuma na aura miki dik wanda naga dama daga haka ya zazzage ya bar wajen yana mai huci.

Sakina da gudu ta mike tabar wajen tana mai rusa kuka, domin ai ko ba komai batayiwa yaya rashin mutunci ba,taya abba zai hukunta ta, ai kamata yayi ya hukunta safna ita kadai, kan gadon ta fada tana mai rusa kuka kamar wadd ranta zai fita, tafi mintuna 30 sanan taji shigowar umma.

☄️☄️☄️☄️☄️☄️☄️☄️☄️☄️☄️☄️☄️
Chapter 7 · 0% Book details